MURMUSHIN ALKAWARI-22
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Ina kuma zaki? MAKALEMATA. Dan gajeren daraktan yace da ita yana kallonta da murmushi. Kalima ta harareshi sannan tayi tsaki.
Wayace ma shi zan bi uban sa ido? Dan gajeren daraktan ya fashe da dariya yace.
Kya karata can da munafurcinki kina so kina kawai kasuwa....
Allah kiyaye... Ai kasan Wallahi salim ba saurayina bane ubangidana ne.
To indai gaskiya ne ba kya son sa me zai hana mu sasanta kinga sai in kara ta biyu da ke. Kalima ta harare shi tace cikin tsiwa.
Allah sawwaka ahaka din zan aureka?... Kamar akife da kwando.
Adaidai lokacin da dan gajeren daraktan ke cacar baki da kalima salim ya isa farfajiyar otal din wasu yan mata guda biyu sukazo wucewa ta kusa dashi sai sukayi turus domin sun gane shi don sun sha ganinsa a fina finai.
Sannu... ABBAS. Dayar datace dashi. Abbas shine sunan daya fito dashi acikin fim din Gaibu. Salim ya juyo fuskarsa ahade ya dubesu yace.
Yawwa sannunku dai sannan ya dauke kansa gefe guda. Ganin basu sami shimfidar fuska agurinsa ba sai yan matan biyu sukayi gaba kafa ba kwari amma duk da haka dai sunyi farin ciki da ganinsa azahiri.
Salim na nan tsaye adaf da wata bishiya mai kamar dabino saiyaji wayarsa ta dauki sauti cikin damuwa salim ya bude wayarsa domin yaga sakon da aka aiko.
Salim ya dubi fuskar wayar sannan yafara karanta sakon kamar haka...
.
.......TUN DAZU NAKE JIRA KO ZAKA BANI AMSAR SAKONA NA FARKO, BAKA AIKO BA SAIGASHI CIKIN IKON ALLAH KA SAKE MATSOWA KUSA DANI AYANZU HAKA MA INA IYA GANIN KYAKYKYAWAR FUSKARKA. SHIN KANA SON GANIN TAWA FUSKAR? MATSOWA GABA KAWAI ZAKAYI SAIKA SHA KWANA ANAN ZAKA SAMI FALMATA.
.
Salim ya rufe wayar ahankali cikin tsananin mamaki sannan ya dubi gabansa adaidai da inda tace yasha kwana zai ganta agurin.
Yau kuma da wa Allah ya hadani? Salim ya tambayi kansa cikin mamaki yana girgiza wayar dake hannunsa tsahon lokaci yana gurin tsaye zuciyarsa nata wasi wasi. Shin ya leka ya ganine ko kuwa kada yaje. Meyiwuwa ma wata shakiyiyarce take son yin wasa da hankalina.
Salim ya fadawa kansa. Ba'a dade ba sai yaji wayarsa ta dauki sauti mai kara cikin sauri ya daga wayar zai amsa saiyaji ta daina yin sautin.
Koda ya duba lambar wayar da aka buo saiyaga lambar falmatan dake damunsa ce dai. Hannunsa na rawa cikin mamaki ya bude wayarsa sannan saiya buga lambar ya kara a kunne ba'afi ko dakika biyar ba sai yaji acan daya bangaren ance.
Hellooo. Salim yaji gabansa yafadi tun dayake bai taba jin muryarsa mai dadin wannan ba. Wacece ke maga....na salim ya tambaya muryarsa na rawa.
Zagayo nan ka ga mai maganar mana. Aka ce dashi sannan lokaci guda ta katse wayar daga can bangaren. Salim ya dubi gawar kan wayar da ke hannunsa ya sake kallon saitin kan kwanar akaro na biyu sannan saiya nufi gurin ahankali yana tafe hannunsa na wasa da fulawowin da sukayi jerin sahu har zuwa karshen ginin inda za'a sha kwanar sa'ar da salim yaje daidai da karshen ginin saiya dan tsaya ya karkata kunne ahankali yana saurare ko zaiji motsi tsahon dakiku baiji sautin komai ba sai sautin katon injin bada wutar lantarkin dake can bayan ginannukun otal din. Sannan ne salim yaji wani irin turare mai taushin kamshi ya bugi hancinsa zuciyarsa ta harba. Duk dayake bai taba jin kamshin irin wannan turaren ba amma kamshinsa yayi kama da irin kamshin turaren mata. Salim ya jingina kafarsa jikin ginin gamida ajiyar zuciya kana yayiwa kansa murmushi yace.
Haba jarumin jarumai ya kake abu haka kamar wani farin shiga. Da wannan kalamin sai salim yasa hannayensa biyu cikin aljihu ya karya kwanar yana takama. Koda yasha kwanar sai kuma ya tsaya cak cikin mamaki domin babu kowa agurin. Salim ya dan sake matsawa gaba ahankali yana takawa daidai kamar namijin agwagwa har dai yakawo daf da wasu rukunin shuke shuken baiga wani mahaluki ba sai wasu mutane biyu magidanta daga can nesa suna busa sigari. Salim ya girgiza kai cikin mamaki gamida murmsuhi oh duniya dai baka rabata da masu son wasa da hankulan mutane. Yace da kansa sannan saiya mika hannunsa zai tsinko wani jan fure dake tsakiyar rukunin shuke shuken katsam sai yaji wani tattausan hannu ya dafa kafadarsa ta baya salim yayi mutuwar tsohuwa hannunsa makale a sararin samaniya bai iya kaiwa ga tsinkar furen ba domin ko shakka bayayi hannun mace ne ya dafa shi. Salim ya juyo ahankali tattausan kamshin turaren na bugun hancinsa yana juyowa sai yayi ido biyu da cikakkiyar halittar.
.
Kayi hakuri naga kamar na tsorata ka. Sannan saita haske shi da murmushin alkawarinta.
SUNANA FALMATA. Kai ko ba ka ma sunanka ba domin na dade da saninka falmata tayi shiru kana ta sunkuyar da kai kasa cikin murmushi hannunta na hagun akan kafadarta ta dama yayinda hannunta na dama ke dauke da wayar tafi da gidanka tana latse-latsen lambobi. Tsawon lokaci salim na tsaye yana kallon tsabagen kyau idanunsa suka dauko hoton santa santalan hannayenta suka zarce zuwa dogon wuyanta madaidaicin bakinta ma'abocin MURMUSHIN ALKAWARI.
Sannan da girar idanunta baki sidik tana sheki gashin kanta.
Tags
# adabin hausa
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
adabin hausa
Category:
adabin hausa