Labari da dumi dumin sa, wata kotun taraiya mai zama a kan titin Court Road dake Kano ta kwace takarar Gwamna daga hannun Abba Kabir Yusuf dan kungiyar Kwankwasiyya inda ta mikawa Alhaji Ibrahim Al-amin Little bisa rashin gaskiya da aka yi wajen zaben fidda gwani na jam'iyar PDP.
Toh tusa fa ta kwacewa bodari, kuma a daidai gabar nan babu wata dama sai dai mu taya mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR murnar lashe zaben sa na ranar asabar.
Alhamdulillah Kano Ta Ganduje Ce!
Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
March 4, 2019.
#KanoCentralDecides2019
SITUATION ROOM
Yanzu karfe sha daya da rabi daidai na safe mun hada sakamakon da muke samu daga wakilanmu, mun samu sakamakon zabe daga kananan hukumomi 15 wadanda suke a Kano Central. A Cikin kananan hukumomi 15 a gaba dayan Kano Central.
Mal. Ibrahim Shekarau APC: 499, 835
Aliyu Sani MadakinGini PDP : 274,125
TAZARAR APC da PDP 225, 711
Karin Bayani: Kananan hukumomin sune Dawakin Kudu da Warawa da Kura da Garun Mallam da Madobi da Gwale da Tarauni da Kumbotso da Ungoggo da Kano Municipal da Munjibir da Dala da Gezawa da Fagge da Nassarawa.
#ShekarauNewMesiaTeam
11 KARAMAR HUKUMAR DOGUWA.
* Gina gada da magudanar ruwa a hanyar garin beguwa.
* Samar da titi mai tsahon kilomita daya da kwalbati da magudanar ruwa a rukunin gidajen ma'aikata a garin riruwai.
* Gina ajujuwa, ma'ajiya da kuma ofishin malamai a makarantar JSS Burji.
*Zuba kujeraru Da bencina Jss Doguwa
*Gina Babban titi na Kudaru zuwa Dadin kowa
*Gina Ajujuwa a SSS Doguwa
*Gina Gidajen Malamai na SSS Doguwa
*Gina Masallachi a Garin Dabakkari
*Gyaran Masallachin juma’ah a Tagwaye
*Gina Islamiyya da Masallachin Doguwa
*Karasa Masallachin juma’ah a Zainabi
*Aikin Wutar lantarki a Fanyabo a Dandabo
*Samar da Transformer a Maigwado,S-Kaura Da Hayin Kano
*Samar da wutar lantarki a Dandoki,Dokar sati,Bahaja.
*Samar da Ruwa a Dadin kowa
*Gina kotun Majistri Da Gidan Alkali a Doguwa
* Samar da hanyar garin Rufai zuwa Maraku.
* Gina gida mai dauke da dakin kwana guda 3 da boys kwatas a cikin rukunin gidajen ma'aikata a garin Riruwai.
* Aikin karasa ginin asibitin garin Burji.
* Aikin Samar da wutar lantarki a gidajen ma'aikatan karamar hukuma.
* Aikin Samar da lantarki a garin tagwaye zuwa kaura, H/kano da magwado.
* Gina katafariyar cibiyar musulunci mai dauke da ofishin hisba da katafaren dakin taro.
A yanzu mai girma Sardauna yana takarar sanata a kano ta tsakiya Wanda aikinsu shine Samar da doka. Mai girma Sardauna zai yi iya yinsa don ganin cewar alummar da yake wakilta sun rabauta da ayyukan raya kasa.
#Shekarau4KanoCenrtal
AYYUKAN RAYA KASA DA GWAMNATIN SARDAUNA TA SAMAR A KANANAN HUKUMOMI A ZANGON FARKO NA MULKIN SA.
#ShekarauNewMediaTeam
10 KARAMAR HUKUMAR DAWAKIN TOFA.
Mai girma Sardaunan kano kuma tsohon gwamnan jihar kano hawa Biyu ya Samar da ayyukan raya kasa a garin dawakin tofa. Ayyukan sun hada da:
* Gina Asibiti a garin tattarawa.
* Gina islamiyya a garin sarauniya.
* Gina islamiyya a garin dawanau.
* Gina titi a garin Alkamawa.
* Samar da hanyar garin Jalli.
* Samar da rijiyoyin burtsatse a sassa da dama a cikin karamar hukumar dawakin tofa.
* Aikin gyaran kurkuku da ke cikin garin dawakin
Tofa.
* Samar da wutar lantarki a garin Kyaure.
* Aikin janyo wutar lantarki a garin Mata da Barguma.
*Gina masallaci a unguwar Gado Quaters Dawanau
*Gina makarantar Muntada a Dangora
*Gina Islamiyya a Kunnawa Dorawar Shehu
*Gina ajujuwa a Tumfafi
*Gina Islamiyya a Tumfafi
*Gyaran makabarta a Kalebawa
*Gina kwalbati a Dawanau
*Gyaran sugar lantarki a D/Tofa da Bgarmawa/kabi
*Gyaran wutar lantarki a Gangari saunter yan awaki
*Samar da Tranfomers a Kadawa/Saji da Ilesha , Gargari
*Gyaran Transformer a Tumfafi.
*Samar da wuta a Dawanau
*Samar da titi daga D/Tofa zuwa Kiyawa
*Gina Gadar Zaura
*Samar da titi daga K/zira zuwa Zaura
*Samar da titi daga Dungurawa zuwa Jalli zuwa Tattarawa
* Gina gada da ta hada Dungurawa zuna Tattarawa
* Samar da titi daga dawakin tofa zuwa tofa
* Gina katafariyar cibiyar musulunci mai dauke da ofishin hisba da katafaren dakin taro a garin dawaki.
Wannan sune kadan daga cikin ayyukan da alummar dawakin tofa suka rabauta dasu a zango farko Mulkin Mal Shekarau farko a jihar kano.
A yanzu Mai girma sardauna yana takarar sanata kano ta tsakiya, Kamar yadda kowa ya sani cewar aikin yan majalisa shine Samar da doka, mai girma sardauna zai yi iya yinsa domin ganin cewar alummar da yake wakilta sun rabauta da ayyukan raya kasa.
#Shekarau4KanoCentral
AYYUKAN RAYA KASA DA GWAMNATIN MAL. IBRAHIM SHEKARAU TA SAMAR A KANANAN HUKUMOMI A ZANGON FARKO NA MULKIN SA.
# ShekarauNewMediaTeam
9 KARAMAR HUKUMAR DAWAKIN KUDU.
* Gina Masallacin Juma'a a garin Tamburawa.
* Gina masallacin Juma'a a garin Dosan.
* Gina Shaguna a kasuwanni makole da kuma dawaki.
* Gina islamiyya a garin Kantsi.
* Gina asibiti a garin Gano.
* Gina titin mai dauke da kwalbati hannu Biyu a garin Tamburawa.
* Samar da tankin ajiyar ruwan sha a garin dawakin kudu.
* Samar da tankin ajiyar ruwa mai dauke da injin wuta a garin Gano.
* Aikin Samar da wutar lantarki a garin busaya dake dandini.
* Aikin karasa ginin babban dakin taro a sakatariyar karamar hukumar dawakin kudu.
* Gina katafariyar cibiyar musulunci a garin dawakin kudu.
*Gina Islamiyya a Tsakuwa
*Gina Islamiyya a Daba Bardai
*Samar da wuta a Danmaje
*Samar da Transformer a dokawa
*Samar da wuta a Korewame Charo
*Gyara Asibti a Gadar Tamburawa
*Gyara Islamiyya a Gadar Tamburawa
*Gyara da zuba kayayyaki a asibitin D/kudu
*Gyaran wutar lantarki a Hausawar D/kudu
*Samar da Borehole masu aiki da hasken rana a Daba kwari
Wannan sune kadan daga cikin ayyukan da mai girma sardauna ya Samar a dawakin kudu a zangon mulkinsa na farko.
A yanzu mai girma sardauna yana takarar sanata a kano ta tsakiya Wanda aikinsu shine yin doka. Mai girma sardauna zai yi iya yinsa don ganin alummar da yake wakilta sun rabauta da irin wannan ayyukan na alheri.
# Shekarau4KanoCentral