*AMFANIN LALLE GUDA 34*
Lalle icce ne daga itatuwan gidan aljannah.Wadda ta fara shuka lalle itace Nana Hajara matar annabi Ibrahim(A.S).
To alhmadulillah muma cikin ikon Allah sae muka samu ilimin lalle kamar haka ga kadan daga cikin magungunan da lalle keyi:
1)a dafa ganyen lalle ko garinsa a tafasa sae a juye a roba a barshi ya dan sha iska a zauna tsawon minti goma yana maganin toilet infection na mata. Yara ma ana iya yi musu saboda matsalar tsarki da suke harda wurin fitsari da kasha baki daya su wanke yana magani.
2)a dafa lalle a kurkure baki da ruwan yana maganin warin baki da ciwon hakori.
3)a hada garin lalle da garin kanumpari ko gawayi a hada gurI daya a rinka yin brush dashi yana kashe kwayoyin cuta kuma yana cire dattin hakora.
4)a kwaba lalle a kunsa gwiwa yana maganin ciwon kafa ,bayan an cire kunshun sae a samu albabunaj a dafa a rinka tsoma tawul a gasa gurin sannan a samu garin lallen da man zaitun da kal tufa a hada arinka shafawa a wurin gwuiwa.
7)a hada lalle da wardi ko xaafaran yana maganin cin ruwa.
8)a kwaba garin lalle da ruwa a matsa yana sa mace ta matse ,a matsa kamar awa biyu sae a wanke da ruwan dumi.
9)masu ciwon diabetes idan suka ji rauni a xuba lalle (garin)akan raunin yana sa ya warke da wuri.
10)a dafa lalle da ruwan khal a rika sha ana shafawa a baya yana maganin ciwon baya.
11)ganyen lalle guda biyu da cup daya na ruwa ko tea spoon daya na garin lalle da jug daya na ruwa asa xuma ko sugar yana maganin ciwon hunhu.
12)a dafa lalle a rinka wanka da ruwan yana maganin warin kashi.
13)a dafa lalle(ganyen ko garin)ana sha da zuma yana maganin juwa.
14)yawan kunsa lalle yana maganin ciwon akaipa (dan karkare).
15)a shaki garin lalle (inhale)yana sa kaipin kwalwa.
16)a jika ganyen lalle guda uku da sugar a barshi ya jiku sosae sae asha..bayan kwana 2 sae a kara sha yana maganin ciwon koda.
17)a dafa lalle asha da xuma yana maganin hawan jini da bugun xuciya.
18)ana shafa garin lalle a konewa ko rauni a xuba garin lallen yana tsaeda jinin yasa wurin ya warke.
19)ganyen lallle guda 20 da sugar 10g a jika a kwanon shan ruwa 1 yana maganin ciwon kuturta (danya amma) kuma a rinka shan kirfata na kwana 20.
20)lalle yana koya gyaran daedaeta alada ...a rika yawan kunsa lalle a kafa da hannu yana gyaran rikicewar alada.
21)ana kwaba lalle da man shanu ana shafawa a jiki yana kashe kurajen fata.
22)a hada ganyen lalle da furen lalle da xuma a jika a cup asha yana maganin mura.
23)a tafasa lalle asha ruwan da xafinshi yana maganin ciwon ciki.
24)a kwaba lalle da ruwan khal a shafa akae yana maganin ciwon kai.
25)a kwaba lalle a dora a hanci yana maganin habo.
26)a dafa ayiwa yara xururu yana maganin dankanoma manya kuma suyi seat bath.
27)a dafa ko asa ganyen lalle cikin ruwan wankan mae jego da jarirI yana kashe fuk kwayoyin cuta kuma yana sa karfin jiki.
28)a shafa man lalle a karaya yana saurin hadeta.
29)ana shafa man lalle a hada da maul wardi ana shafe jiki dashi yana maganin stroke(shanyewar jiki).
30)a hada garin lalle da man kafur yana maganin sanyin kashi;ba kafur na gida ba.
31)ganyen lalle guda 2 asa ruwan xapi kopi daya da sugar tea spoon daya asha yana maganin shawara.
32)a samu garin lalle1/4 na kopi,garin habbatussauda kopi 3 a kwaba da ruwan xapi a shafa a kae na 3hours sae a wanke da ruwan dumi yana hana karewar gashi musamman cikin sanyin nan yanda gashi ke kakkaryewa.
33)a hada lalle da xuma a rika. Shafawa akae yana guara gashi (steaming)a wanke da ruwan dumi.
34)a hada lalle da xuma kwae da manta da hulba a shafa a jiki sae a tafasa lalle ayi siraci sae ayi wanka da ruwan yana gyara fata.
Duka anan muka kawo karshen wannan shiri na amfanin lalle..
Wata Sabuwa Angano Amfani Lalle Guda 33
Tags
# magunguna
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
magunguna
Category:
magunguna