IYA ZAMA DA MIJI DAGA BAKIN MARIGAYI SHEIKH JA'AFAR
Daga Shema'u Auwal Adam
1-Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.
2-Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.
3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa harma da dangantakarsa.
4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.
5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki.
6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.
7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.
8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.
9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.
10- Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.
11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki.
12- Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.
13- ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki, da sauransu.
14- Ki dinga girmama Iyayan mijinki da 'yan uwansa da abokansa.
15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.
16- Kada ki zama mai satar fita unguwa.
17- Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.
18- Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya baki.
19- ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.
20- ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da safe, rana, dakuma dare.
21- Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.
22- Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi.
23- Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.
24- Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki, kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a duk lokacin kwanciya.
25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.
26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.
27- Ki zama mai yawan canza zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.
28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.
29- Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke dukkan wani hukunci.
30- Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake yi miki fada ko Nasiha.
31- Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.
32- Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.
33- Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na zuwa unguwa.
34- Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.
35- Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin sirrin dake tsakaninki da mijinki.
36- Idan zaki yiwa mijinki magana kiyi masa da tattaunsan harshe, da murya mai karya zukata.
38- Ki zama kin iya kallo mai nuna alamun sha'awa ko soyayya.
39- Idan kika samu sabani da mijinki ki bashi hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.
40- Ki zama mai tattali a cikin dukkan abinda kika mallaka a gidan mijinki.
41- Kada ki zama mai kwauron baiwa dangin mijinki abinda ya umarceki da a basu.
42- Kada ki zama mai yin dare wajan girki.
43- Kada ki zama uwar adashi ba tare da sanin mijinki ba.
44- kada ki zama mai yawan fada da makwabtanki.
45- Kada ki kasance mai yawan zagi ko Ashariya.
46- Kada ki ringa baiwa Iyayanki Labarin laifin da mijinki yake miki.
47-Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar Iyayan mijinki da 'yan uwansa.
48-Idan mijinki ya yi miki laifi kada ki nuna masa bacin ranki a gaban iyayanki ko 'yan uwansa.
49-Kada ki ringa daga murya sama idan kuna sa-in-sa da mijinki.
50-Kad ringa baiwa 'yan uwan mijinki labarin laifukansa.
52- Ki dinga yiwa mahafiyar mijinki Ihsani da 'yanuwa
Taku
Maman Ikhram
Zokiji Yadda Zaki Iya zama Da Mijinki
Tags
# Zamantakewar Aure
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
Zamantakewar Aure
Category:
Zamantakewar Aure