Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Yadda Zaka Bude Account din banki a a Facebook

Mai karatu barka da warhaka da fatan kana jin dadin kasancewa da mu.
Kasancewar al’amarin wannan duniya ta fuskar fasaha kullum kara gaba yake.
A yau mun zo muku da yadda zaka bude asusun ajiya na Banki wato Bank Account ta FaceBook, wannan fasahar da zata bawa mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook damar bude asusun ajiya na banki cikin kasa da mintuna 5 ba tare da kaje banki ba.
YADDA ZAKA BUDE ACCOUNT DIN;
Nasan da daman masu amfani da Facebook messenger kan ci karo da tallan Bankin UBA wato UBA Chatting Banking.?
In kuwa haka ne kayan kaya zinke a gindi kaba.
Yadda zakai shi ne :
Zaka bukaci yin hira da shi Bankin wato “chat” kana dannawa LEO zai ma ka marhaba sannan ya tambaye ka me kake da bukata, a nan ne zaka danna opening account.
Sa su tambayeka abubuwa kamar haka:
Lambar waya
Suna
Shekarar haihuwa
Adireshinka
E-mail
Hoton ka.
Za suyi maka wadannan tambayoyi ne daya-bayan-daya, kana gaba shigarwa zasu turoma activation code a wayar ka , wacce zaka saka itama a gurin bude account din daga karshe , nan take zaka samu Account da bankin UBA.
Abin Lura:
Bayanan da zaka shiga ka tabbatar sune a jikn BVN dinka, don in kaje karbar ATM da su za’ai la’akari.
Passort kuma nan take zaka dauka in baka da shi a wayar ka.
Wannan shine karshen bayani kan yadda zaka bude Account ta FaceBook.
Mun gode!!!