Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Showing posts with label magunguna. Show all posts
Showing posts with label magunguna. Show all posts

Shin kunsan amfanin magarya kuwa

 Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.
Ya kasance ana amfani da ita tun kafin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka fadada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani.
Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanun ganye da kuma "ya"yan magarya. Bincike ya baiwa masana ilimin har hada magani na yan kunan turai da wasu yan kunan kasahen duniya na Larabawa da India dama na shiyarmu ta Afrika, wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin dake da karfi da saurin warkar da cututtukka.
*Ga kadan daga cikinsu:*
1- *Ciwon daji* A dafa garin magarya misalin kofi daya karami sai asa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci.
Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature.
2- Miki ko kuraje a kan fatar jiki ko wani sashe na gangar jiki: sai a tafasa garin magarya da ruwan khal sai a wanke mikin ko kurjin da kyau da wadannan ruwan sai a marmasa garin magarya kadan a kan mikin bayan ya wuni a haka sai a saka ruwan dumi a wanke maganin sai a sake maimaitawa. In sha Allahu za a samu sauki.
3 - *Cututtukan* ciki kama daga kumburin cikin da baya da alaka da cin wani abinci ko abin sha, zafin ciki da yawan tsuwar hanjin ciki akai akai sanadiyyar wasu kwayoyin cuta na bacteria sai a nemi ganyen magarya mai kyau sai a saka ruwan dumi a tace da kyau a sha kashi daya daga cikin kashi uku na karamin kofi. Haka za a maimaita da yamma. -Saurin warke ciwo. Anan,
4- idan ana fama da jinya ko a lokacin da ake farfadowa daga wata rashin lafiya wacce ta kontar da kai a sanda kake jin jikinka ba karfi ko kaji baka son cin komai saboda baka jin dan danonsa. To sai ka nemi garin "yayan magarya kamar cokali uku kanana sai ka sanya zuma ka kwaba ka sha. Za ka rinka yin haka a kalla sau biyu a wuni a cikin kankanin lokaci za ka ji karfi da kuma dadin jikinka.
5- Ko kuma mafi sauki ka nemi " ya "yan magarya ka dunga sha, A hakika suna kunshe da dimbin sinadirran bitamin C wanda yake hura garkuwar jiki fiye da wanda ke cikin bitamin C din da muke siya a kemis din saida magani.
6- Ganyen magarya na da karfin yakar cututtukan fata, kama daga makero da kazzuwa da kurajen fata na ba gaira ko ake kallon kamar na iska ne, to za a kwaba garin sai a shafa da man kade ba baseline ba a inda matsalar ta shafa. Idan maganin ya dauki lokaci sai a wanke da ruwan dumi. Ko mafi sauki a nemi sabulun magarya mai kyau a dinga amfani da shi.
7- Yana tsaftace jini – yana dauke da sinadiran saponin, alkanoide da kuma triterpenoid da ke gyara jinin jikin dan’adam.
8- Yawan gajiya da ciwon jiki ko yaushe, sai a rinka shafa ganyen dan yensa a sanya a cikin ruwan dumi a tace da kyau a sha.
9- Ganyen magarya na tsaida gudawar da ta tsananta sanadiyar lalacewar ciki, ko dai matsalar daga abinci ne ko cin karo da wata kwayar cuta ta bacteria, a nan banda gudawa a sanadin ciwon tsida, za a sha cokali daya karami na 5ml a koko ko ruwan zafi.
10- *Karya sihirin maye:*
A gargajiyance wannan magani ne da aka sha jarrabawa kuma ake samun dacewa, Idan maye ya kama mutum to sai a nemo busashen ganyen magarya a hada da wani turaren wuta da ba zamu fadi sunansa a nan ba saboda wasu dalillai to sai a zo a tirarawa wanda maye ya kama a nan take mayen zai sake shi.
11- Ana karya sihiri ta amfani da ganyen magarya sai dai ilimin yanda ake amfani da ganyen magarya a karya sihiri ya sha banban.
.
12 - Mata masu karancin sha’awar saduwa sai su dunga shan ganyen da madara 5ml a kullum.
13- Ganyen magarya na maganin damuwa da hawan jini saboda kunshe yake da ninki ba ninki na sinadiran potassium.
13 - Ganyen magarya na maganin gyambon ciki.
14- Ganyen magarya na kare cututtukan hanta dana koda.
15- Yana daidaita nauyin jikin mutum.
16- Garin "ya "yan magarya na karawa garkuwar jiki kuzari. -
17- Ana gauraya garin "ya"yan magarya da garin dabino rabin cokali sai a sanya ruwa a tafasa a sanya zuma kadan a sha dan magance yawan mantuwa da ta yi tsanani musamman a sanda za a kwanta.
18- Matan da suka haihu za su iya hada ganyen magarya da garin " ya "yan bagaruwa su tafasa sai su rinka tsarki da ruwan, amma kada a cusa garinsa, wannan zai taimaka su samu dai-daituwa da kuma sake hadewa.
19- Ana tsotsar " ya "yan magarya dan maganin kurajen da ke tsiro a harshe ko a cikin baki.
Allah ya bamu da cewa

Wata Sabuwa Angano Amfani Lalle Guda 33

*AMFANIN LALLE GUDA 34*


Lalle icce ne daga itatuwan gidan aljannah.Wadda ta fara shuka lalle itace Nana Hajara matar annabi Ibrahim(A.S).

 To alhmadulillah muma cikin ikon Allah sae muka samu ilimin lalle kamar haka ga kadan daga cikin magungunan da lalle keyi:

1)a dafa ganyen lalle ko garinsa a tafasa sae a juye a roba a barshi ya dan sha iska a zauna tsawon minti goma yana maganin toilet infection na mata. Yara ma ana iya yi musu saboda matsalar tsarki da suke harda wurin fitsari da kasha baki daya su wanke yana magani.

2)a dafa lalle a kurkure baki da ruwan yana maganin warin baki da ciwon hakori.

3)a hada garin lalle da garin kanumpari ko gawayi a hada gurI daya a rinka yin brush dashi yana kashe kwayoyin cuta kuma yana cire dattin hakora.

4)a kwaba lalle a kunsa gwiwa yana maganin ciwon kafa ,bayan an cire kunshun sae a samu albabunaj a dafa a rinka tsoma tawul a gasa gurin sannan a samu garin lallen da man zaitun da kal tufa a hada arinka shafawa a wurin gwuiwa.

7)a hada lalle da wardi ko xaafaran yana maganin cin ruwa.

8)a kwaba garin lalle da ruwa a matsa yana sa mace ta matse ,a matsa kamar awa biyu sae a wanke da ruwan dumi.

9)masu ciwon diabetes idan suka ji rauni a xuba lalle (garin)akan raunin yana sa ya warke da wuri.

10)a dafa lalle da ruwan khal a rika sha ana shafawa a baya yana maganin ciwon baya.


11)ganyen lalle guda biyu da cup daya na ruwa ko tea spoon daya na garin lalle da jug daya na ruwa asa xuma ko sugar yana maganin ciwon hunhu.

12)a dafa lalle a rinka wanka da ruwan yana maganin warin kashi.

13)a dafa lalle(ganyen ko garin)ana sha da zuma yana maganin juwa.

14)yawan kunsa lalle yana maganin ciwon akaipa (dan karkare).

15)a shaki garin lalle (inhale)yana sa kaipin kwalwa.

16)a jika ganyen lalle guda uku da sugar a barshi ya jiku sosae sae asha..bayan kwana 2 sae a kara sha yana maganin ciwon koda.

17)a dafa lalle asha da xuma yana maganin hawan jini da bugun xuciya.

18)ana shafa garin lalle a konewa ko rauni a xuba garin lallen yana tsaeda jinin yasa wurin ya warke.

19)ganyen lallle guda 20 da sugar 10g a jika a kwanon shan ruwa 1 yana maganin ciwon kuturta (danya amma) kuma a rinka shan kirfata na kwana 20.

20)lalle yana koya gyaran daedaeta alada ...a rika yawan kunsa lalle a kafa da hannu yana gyaran rikicewar alada.

21)ana kwaba lalle da man shanu ana shafawa a jiki yana kashe kurajen fata.

22)a hada ganyen lalle da furen lalle da xuma a jika a cup asha yana maganin mura.

23)a tafasa lalle asha ruwan da xafinshi yana maganin ciwon ciki.

24)a kwaba lalle da ruwan khal a shafa akae yana maganin ciwon kai.

25)a kwaba lalle a dora a hanci yana maganin habo.

26)a dafa ayiwa yara xururu yana maganin dankanoma manya kuma suyi seat bath.

27)a dafa ko asa ganyen lalle cikin ruwan wankan mae jego da jarirI yana kashe fuk kwayoyin cuta kuma yana sa karfin jiki.

28)a shafa man lalle a karaya yana saurin hadeta.

29)ana shafa man lalle a hada da maul wardi ana shafe jiki dashi yana maganin stroke(shanyewar jiki).

30)a hada garin lalle da man kafur yana maganin sanyin kashi;ba kafur na gida ba.

31)ganyen lalle guda 2 asa ruwan xapi kopi daya da sugar tea spoon daya asha yana maganin shawara.


32)a samu garin lalle1/4 na kopi,garin habbatussauda kopi 3 a kwaba da ruwan xapi a shafa a kae na 3hours sae a wanke da ruwan dumi yana hana karewar gashi musamman cikin sanyin nan yanda gashi ke kakkaryewa.


33)a hada lalle da xuma a rika. Shafawa akae yana guara gashi (steaming)a wanke da ruwan dumi.


34)a hada lalle da xuma kwae da manta da hulba a shafa a jiki sae a tafasa lalle ayi siraci sae ayi wanka da ruwan yana gyara fata.

Duka anan muka kawo karshen wannan shiri na amfanin lalle..