Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Raliya 17

RALIYA-17
.
Dumfama ya saita bindigarshi ya auna wani dan kakkaura a cikin tsofaffin 'yan sandan biyu" ya dirka masa bindigar" dan sandan yayi kuwwa sannan ya wuntsila ya fada cikin ciyayi
abokinshi ya fashe da kururuwa ya tambayeshi
"Bilya meya sameka?
Dumfama dake boye a cikin ciyawa yayi
murmushin mugunta" sannan ya auna goshin
ragowar dayan daga nesa" A daidai lokacin da
yaja kunamar bindigar ne kan dan sandan ya
tarwatse kwanyarshi ta watse a cikin gonar
tumatirin dake wajen lokacin da gangar jikinshi ta fadi gefe guda" ko sau daya bai sake motsawa ba
Dumfama ya jefar da bindigar sannan ya saki
hannunshi dake dafe da raunin da Naziru yaji
mishi" ya yiwa sullubebiyar wukar kallon karshe wacce ke yashe a kasa tayi dama-dama da jini yana nan akwance a wurin yana haure-
haure azaba" kafin mutuwa tayi awon gaba dashi har zuwa lokacin bai mance da babban abokin shi ba daya ha'ince shi Rambo
.
=====>++++++()+++++<=======
.
Rufa'i baisha wahala ba" wajen kwance igiyar
dake daure a hannunshi ta hanyar kwana da yayi yana gwagwiyar ta da hakora" bayan ya kwance daurin da 'yan sandan sukayi mashi" sai yayi hanzarin kwance igiyar da suka zagayeshi da ita a jikinshi da kafafuwanshi kamar huhun goro Da kwancewarshi ya fasa tagar da wata kujerar katako daya dake cikin dakin" Rufa'i ya haura ta cikin tagar ya gudu yabar tsohon gidan da suka kawoshi suka kulleshi" har lokacin da ya nemi motar komawa kauyensu daga birnin kano yayi tsammanin 'yan yankan kaine suka kamashi Sai lokacin da ya koma gida ne ya rude da yasami labarin abinda ya faru a wurin masoyiyarshi Raliya" wacce take ta faman kukan farin ciki tun dawowarshi
A ranar ba'a yi barci ba a kauyen Danmarke"
domin kuwa an ga bala'in da ba'a taba gani ba"
An tsinci gawarwaki har hudu" daya gawar
Naziru ne babban dan ladanin garin" da kuma
gawar 'yan sanda har biyu" tare da gawar wani
bakin saurayi da ba'a san inda yake ba
'yan sanda sunyi iyakar kokarinsu wajen gwaje-
gwaje domin su gano mafarin al'amarin to
amma kuma da maganar taje kunnen
kwamishinan 'yan sanda "Danmasani" sai ya
gargadi jami'an dake da alhakin binciken ya
tattara maganar yayi watsi da ita" cikin
gaggawa" nan da nan aka kwashe 'yan sanda aka tafi dasu" tun daga nan ba'a san inda maganar ta nufa ba.
to amma kuma da ace za'a tuntubi Raliya da
masoyinta Rufa'i sun fi kowa sanin yadda
al'amarin ya faru" sunyi shiru ne domin kuwa
basa son wani abu ya sake kawo musu cikas a
wannan lokaci nasu mai muhimmanci da zasuyi aure
Bayan kwana biyu kuma hankali ya fara
kwanciya" sai kuma wani masunci dake kamun
kifi ya lalubo gawar wani saurayi a kasan kogin
dake garin harta fara rubewa" bayan jama'a sun
taru ne jingim a bakin kogin sai aka gane ko
wanene Hashimu ne dan gidan malam makeri wanda matasan kauyen Dan marke ke kiranshi Shegen Sama
A ranar kwana akayi ana kuka da Addu'o'i a
kauyen dan marke" domin kuwa ba'a taba yin
jana'iza har uku a jere a cikin kwana biyu ba sai
a wannan lokaci babu wanda yasan dalilin
faruwar wadannan munanan abubuwa" to amma kuma wasu mutanen dake kauyen acan cikin zuciyarsu farin ciki sukeyi" domin kuwa dama wadannan shakiyan samari biyu sun gallabesu. a satin ne aka tsayar da lokacin auren Raliya da masoyinta Rufa'i sha hudu ga watan sallah Babba
.
=====>*******************<========
.
Kwana shida kacal da faruwar al'amarin
kwamishinan 'yan sanda dan masani ya sami
bakar takardar kora daga babban insifrktan 'yan
sanda na kasa" jami'an tsaro da dama basuyi
mamakin korar kwamishina da kuma yi mashi
ritaya da akayi ba cikin gaggawa"
Domin kuwa ya dade yana cin amanar aikin
tsaro ta hanyar amsar cin hanci daga wurin
rikakkun 'yan fashi da makami da kuma masu
safarar miyagun kwayoyi
A rana ta biyu da sallamar kwamishina" yaje
wani gidan giya yasha yayi tatul da daddare"
domin kuwa yawanci idan yana cikin bacin rai to giyar kawai yake sha yaji ta kwatar mashi da
hankali bayan dare yayi nisa" saiya kamo hanyar dawowa gidanshi inda wata karuwarshi bose ke zaman jiranshi tsawon lokaci bata san inda ya shiga ba
Danmasani yana cikin tafiya bai ankara ba wata
katuwar motar daukar kaya ta shawo gangara
aguje" babu fitila ko daya a gabanta" motar ta
fada wani gargada tana sukuwa" cikin kosawa ta cimma tsohon najadun"
Bai ankara ba sai yaji motar ta haye kanshi tana
burari" yaji lokacin da katuwar tayar motar ta
gaba ta haye kan ruwan cikinshi" daga nan kuma bai sake jin komai ba" sai radadin da ya
mamayeshi a lokacin da kayan cikinshi sukayi
falle-falle akan titi
Alhaji Elbashir ya bude jaridar dake dauke da
labarin mutuwar tsohon kwamishinan 'yan
sandan" yayi dariya" sannan yace" yanzu na
tabbatar na huce haushin miliyoyin kudina" banyi asararsu a banza ba
Yana cikin doki ne da farin ciki" da sassafe washegari ya je ofishinsa dake birnin tarayya" sai yayi wasu muhimman baki a motoci sanye da bakaken kot" Sai bayan da mutanen suka cika ofishin ne kamar kwari" sannan ya fahimci
rundunar hana barna ne da babakere akan dukiyar kasa" shugaban tafiyar ya kalli Alhaji Elbashir yace dashi
"Munzo ne domin kayi mana bayanin yadda ka
salwantar da Dala miliyan hamsin daga sashinka" sannan kuma an tsinci gawarwakin
abokan aikinka an gina wani rami a cikin wani
rafi a kano an binne su" muna so kayi mana
bayani akan abinda ka sani
Alhaji Elbashir yaji kamar duniya ce ta ruguzo
masa domin dai yasan cewar tashi tazo karshe
.
======>******************<======
.
Kwana uku cur" Rambo yana tafiya a cikin
kusurgumin daji" idan dare yayi" sai ya haye
bishiya ya rungumo akwatin kudinshi yayi shiru
yana tunanin hanyar da zaibi ya gudu yabar
kasar dasu" yana jin tsoron fitowa cikin gari
domin kuwa yayi tsammanin tuni an baza jami'an tsaro domin su gano inda ya shiga"
Wani lokacin yakan yi ta wuce tsaunuka da lardin da fulani ke zaune jefi-jefi" ya gwammace yaci gaba da rayuwarshi a daji" komai dadewa idan kura ta lafa yasan cewar zai fito sarari zai ci gajiyar miliyoyin kudinshi"
wannan wani lamari ne dake bukatar juriya da
hankuri" Rambo ya kware a wannan fannin tun awani zama da yayi na wata takwas a gidan yari.
A dare na uku Rambo yana saman wata katuwar tsamiya" yayi lamo a cikin duhu sai kace aljani yana rungume da akwatin kudin" yana sauraron
kukan kwari da tsuntsaye" farin wata ya haske ko ina a cikin dajin ba gida gaba ba gida baya"
Rambo yana matukar jin yunwa mai tsanani"
domin kuwa rabon ya sami wani abu yasa a
cikinshi tun kwana biyu da suka wuce a lokacin
da yasami wata gwandar daji ya tsinka yasha"
tun lokacin har aka kwana biyu Rambo bai sake
samun wani abu naci a duk yawon da yake yi a
cikin dajin ba
To amma kuma da Rambo yaji yunwa ta
tsananta mishi sai ya fara tunanin saukowa ya
fita cikin dajin ya zagaya me yiwuwa ko tsada ya samu" to amma kuma da yayi tunanin barin
ringimemen akwatin kudin a saman bishiya" sai yaji baya bukatar saukowa daga kan bishiyar" yafi so duk inda zai shiga yana nan tare da akwatin miliyoyin kudin shi sune mabudin jin dadin rayuwarshi da yake so yayi nan da wani dan lokacin idan ya koma kasar turai"
Rambo yana nan kwance akan wani reshe sai yaji motsin wani abu a kusa da gindin bishiyar ya taho yana keta kayoyi da ganyen gauda dake
warwatse ako ina a cikin dajin" sannan kuma yaji wani gurnani" da nishi mai karfi ya cika ko ina awajen"
Rambo yayi saurin gyara zama a tsorace ya duka da kanshi ya kalli kasan bishiyar" domin ganin abinda ke motsi" yaji gabanshi ya fadi" hantar cikinshi ta motsa wata shirgegiyar kura ce" tana tafiya dakyar" tana zaro harshe tana lashe bakinta Rambo yayi lamo a cikin bishiyar ya daina numfashi " sai kace bashi da rai domin kuwa yasha jin ana bada labarin kuraye tun yana yaro"
Ya dade yana jin cewar in har kura ta jiyo warin
mutum ko daga ina take saita biyo warin tazo ta cimmashi"
Rambo yasan cewar warinshi ta jjiwo daga nesa shiyasa take ta zagaye zagaye a gindin tsamiyar tana gurnani tana tona ganyaye da kafafuwanta domin taci sa'ar ganin inda mutum yake ta sami abinda zata ci ta kaiwa jariran 'ya'yanta ragowa
Rambo yana kallonta ta saman bishiyar" tana ta
neme-neme" gabanshi sai faduwa yake yi" amma kuma akwatin kudinshi yana nan a kankame a kirjin shi.
Bayan wani lokaci sai kurar ta hakura ta koma"
Rambo ya hangota a cikin hasken farin watan
cikin ciyawa" da ganyaye tana tafiya" bayan tayi
nisa ta bace" ya daina hangenta" sai ya kama
reshikan tsamiyar ya sauko" domin ya gudu
yabar dajin" ya sami labarin idan har kura ta
kwallafa ranta akan abinda take so" to koda ace
tafiya tayi" ba hakura tayi ba zata sake dawowa.
Rambo ya diro daga saman bishiyar" ya yanki
wani bangare na dajin ya fara cin gudu" nauyin
akwatin kudin dake kankame a hannunshi ya
sashi yin zufa" amma kuma bai tsaya ba sai dai
lokaci-lokaci yakan sa hannunshi ya share zufar dake a fuskarshi"
Rambo yayi nisa yana cin gudu" wani lokaci
yakan fada cikin kananan ramukan da ganyaye
suka lullube" bayan wani lokaci sai ya fito ya
sake maida hankali domin tserewa mafadaciyar kurar da ta bashi tsoro
Bai san iyakar awoyin da yayi yana gudu a cikin
daji ba" ya dai tsinci kanshi ne a bakin wani
kauye da motoci ke bi suna wucewa wacce ta
ratsa ta cikin wani karamin labi da fulani kebi
suna wucewa da shanun su.
Rambo ya tsaya a jikin wata karamar bishiya mai yawan reshuka" bayan wani lokaci yana nan tsaye yana mayar da numfashi sai ya yanke shawarar sake hayewa saman bishiyar ya boye kudin shi.
Rambo ya hau saman bishiyar tare da akwatin
kudin ya makale a jikinshi" ya dora akwatin akan wani reshe ya kwantar dashi sannan ya fara shawarar fita neman abinci.......