Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Raliya 24

RALIYA-24
.
Dan Sandan dake biye da lado sabon shiga ne
bai kware ba" kuma bai dade da fara aiki ba"
dakyar aka matsa mashi ya biyo tawagar jami'an tsaron da zasu zo aikin kama barayin" don haka a lokacin tsoro yake bin lado yana jin tsoro kada lado ya juyo ya harbeshi"
Dan sandan wani saurayi ne dogo mara jiki"
watanshi biyu da fara aiki" kuma yayi alkawarin
da ya cika shekara daya zaiyi murabus" ya koma makaranta dama kudin shiga jami'a yake nema shiyasa ya gwammace ya nemi aikin dan sanda don haka yayi alkawarin bazai taba sa kan shi cikin hadari a kashe shi a banza ba"
Da gangan yabar lado yayi mishi nisa" da yaga
ya bace ya daina hangoshi" sai ya dawo baya"
yana numfashi dakyar haka ya koma ya sami
ragowar jami'an tsaron su bakwai duk da wani
sajan madugun tafiyar"
ya sharara masu karyar" fada sukayi hannu da
hannu shida barayon da yabi" kuma har ya buge barawon zaisa mashi ankwa ya kamo shi" sai wani a cikin barayin ya biyo ta baya ya kada mishi gindin bindiga akai" da suka ga ya fadi sai suka barshi" daga baya ya taso juwa na dibarshi" dakyar ya iya dawowa".
Sauran 'yan sandan sukayi tayi mashi godiya da jinjina" domin kuwa shi ma yayi iya bakin kokarinsa" a lokacin tuni lado niga yakai gida" kuma harya shiga dakin shi ya fara yunkurin adana kudin shi Dala miliyan hamsin
.
======>++++++++++<=======
.
Alhaji Hashimu " fitaccen manomi ne a garin
kwanar tsamiya" sau da yawa duk lokacin da
Za'a fadi sunanshi anfi hadawa da kirarin da akeyi mashi wato "MAI Abinci Har Bayan Rai dole ne mutane su rika yi mashi wannan kirarin" domin kuwa ance duk shekara yakan noma hatsi buhu dubu takwas da dari biyar"
wata shekarar kuma idan damina tayi albarka
sosai ance har dubu goma yana cikashewa" don haka babu mamaki don ance mashi "Mai Abinci Har bayan Rai domin kuwa ansan cewar indai abinci yake nema" to bai isa yaga bayan buhunan hatsi dubu takwas ba" in da ba mutanen jihar su zai rika ciyarwa ba"
Alhaji Hashimu yana da 'ya'ya majiya karfi" kuma mafi yawancinsu mazane lafiyayyu" a haka sun kai guda ashirin da shida" domin kuwa matan shi hudu" kuma biyu da suka gama haihuwa basu fasa kwatanniya ba" saida kowacce ta dire 'ya'ya goma sha uku a dakinta" kamar suna gasa tara maza hudu mata" su kuma sauran matan biyu wato amare daya tana da 'ya'ya bakwai biyar maxza mata biyu" daya kuma tana da guda biyar maza" biyu mata uku
Wadannan 'ya'ya basu taba tsorata wannan
tsohon manomi ba" domin kuwa kowacce safiya sai an cika wani karamin diro da tuwo" da kuma wato gabjejiyar tukunyar miya" wacce matan shi ke bashi labari idan suna so ya karo kudin magi cewar guga uku tukunyar keci" kuma kullum sai an cika ta fal har baki indai ana so miyar ta ishi kowa da safe
Da rana kuma da yake ana kaiwa 'yan gona
abinci Alhaji Hashimu yafi so a rika yin dambu
akai akai" domin yafi auki" shima dambun sai ancika diro duk da wanda za'a diba a kaiwa manyan 'ya'yanshi dake kaiwa rana fadowa a gona"
Amma kuma a yadda matan shi ke korafi wani
lokacin sunce ko dambun tiya shida akayi Dakyar suke samun sa'a yabasu kudin mai rabin kwalba daya a zuba"
Idan kuma bai ga dama ba" sai a dauki kwanaki
ana abinci babu mai a ciki" hakan an kirga adadin 'ya'yanshi suke rububi suna ci don maganin yunwa"
Babu abinda Alhaji Hashimu yafi so a duniya irin yaga yayi wa 'ya'yansa maza aure" tun suna
shekara sha bakwai a duniya" wani lokaci har
alfahari yake yiwa mutanen yankin cewar" yafi
duk wani mai kudi nunawa yara gatanci" domin
kuwa idan yaro yana dagewa aiki a gona yana
sawa kartin yayyenshi yana wuce su" to dole ne ashekarar ya bashi izni yaje ya nemo aure a kara mishi ta biyu" kota uku" wasu sunce yana da wani matashin saurayi dan shekara ashirin da biyu wanda ke da mata hudu duk yara masu jini ajika. Babu abinda Alhaji Hashimu ya tsana a duniya irin karatun boko" domin kuwa yasha fadawa 'ya'yanshi idan suna aiki a gona cewar da wani ya guji aikin gona ya koma boko" to gara su mutu kowa ya huta"
"boko karyar banza ce yara" ku rabu da wannan
hanyar ku koma gona itace rufin asirin ku a
duniya" wannan shine abinda wannan manomi yayi imani dashi"
A haka 'ya'yanshi da jikokinshi suka taso ba ilmin addini" babu na zamani" idan abokanshi masu banbancin ra'ayi irin nashi suka bashi shawara ya rika mayar da hankali wajen ilmin 'ya'yanshi sai ya kira 'ya'yan yace idan dare yayi su rika daukar alluna suna zuwa wajen wani malami dake da almajirai a kusa da gidanshi"
Domin kuwa daga safe har yamma lokacin gona ne" yana ganin asara ce mutum mai lafiya a gida yana karance karance ga aiki can a gona ba iyaka"
Su kuma 'ya'yan basa tsayawa yin wani karatu
da daddare" suna gama cin abinci zasu bazama gidajen bidiyon dake a kauyen"
Alhaji Hashimu bai damu da haka ba domin kuwa shi a ganin shi indai namiji zai auri mata hudu" kuma indai zai iya zuwa gona tunda asuba ya dukufa aiki saidai a bishi can da abinci"
Kuma ace bazai dawo ba sai rana ta fadi" to
menene matsalar ai rayuwa tayi kyau" mutum
ya wuce gori indai ba zana karya za'ayi ba"
Sannu a hankali zamani yaci gaba da tafiya" sai
kuma aka fara samun 'yan tawaye a cikin
'ya'yanshi da wadanda ke so su shiga
makarantar boko" da kuma wadanda basu son
Zuwa gona" masu son suyi karatun sun dan fara gane dadin ilmi ne a dalilin wani saurayin da ya bude ajin yaki da jahilci na manya a kauyen duk sati kowanne mutum yana bada naira goma ladan aji"
Ba wani nisa akayi da karatun ba" kawai bakake
ya koya musu hadawa" duk wanda ya iya rubuta sunanshi da kuma sunan garinsu" kuma duk wanda ya iya karanta sunan fim a jikin kwalin kaset din da ake kafewa a gidan bidiyo" sai ya kama murna da tsalle"
Nan da nan 'ya'yan manomin hudu suka dinka
kayan makaranta suka shigar da kansu firamaren dake kuyen" basu damu da girman da sukayi acikin yara ba" domin kuwa karatu suke nema ido rufe"
A ranar da aka je gona ba tare da su ba" sai da
Alhaji Hashimu yabi kowannensu da gora zai
buge da kyar mutane suka rike shi suna bashi
hankuri"
Su kuma bangaren wadanda basu son zuwa
gonar sune irin su Ladoga Niga " da kuma wasu yayyenshi biyu" su kuma abokai ke zuga su"
suna nuna musu cewar ya za'ayi babansu yana
da kudi ga gonaki da motoci" ga gidajen da ya
gina lafiyayyu ana haya a kauyen" kuma su rika
wahalar zuwa gona?"
Don haka sai suka zama 'yan tawaye sai dai su
ci tuwo da safe" suyi kwanciyarsu suna jin wakar fina finan Hausa" a rikoda wasu kuma suna wasan karta da kuma kokuwa da abokai.
Da Alhaji Hashimu yayi tarkonsu bai sami sa.ar
kama ko yaro daya a cikinsu ba" sai ya bada
doka a gidanshi cewar duk wacce ta kara basu abinci a bakin aurenta" daga baya da ya sami
labarin kowacce idan uwarshi ke da aiki taba
bashi abinci a boye" sai manomin yasa wata
ranar Juma'a da safe ya gayyaci" 'yan uwa da
abokan arziki aka daka gumbar sadaka da kuma koko da waina da suga" ya tsinewa 'ya'yan baki dayansu"
tsinuwar da yayi musu ai itace ta bisu" domin
kuwa ba' a jima ba Kungiyar su Lado wadanda
basa zuwa gona suka fara shaye shaye da daukar kayan mutane" da kuma miyagun dabi'u na tir da Allah wadai kafin wani lokaci duk suka kori matansu na ladan noma.
Ana kan haka kuma a wata ranar lahadi da yamma Alhaji Hashimu mai Abinci Har bayan
Rai yaje gona da yammaci" ko sallar la'asar
baiyi ba" yana can har dare yayi" ba magriba ba
isha'i yana faman kaftun inda zai dasa wani irin
rake" yana cikin aikin kenan farsin wata na
dibarshi da haske" bai san lokacin da ya dora
kafarshi a jikin wutsiyar wani bakin maciji ba"
wanda ya fito neman abincin dare"
macijin ya juyo da kanshi a fusace ya kaftawa
Alhaji Hashimu sara sau biyu a jere" sannan ya
sulale a guje bayan ya ga tsohon ya fasa
kururuwa ya dafe kafarshi yana dingishi zuwa
inda ya ajiya wani tsohon babur dinshi
(Kawasaki) bai isa wajen babur din ba" ya fadi
kasa kuma bai sake tashi ba daga nan
Sai da safiya tayi da mutane suka fara
sammakon zuwa gonaki sannan aka ganshi a
bakin hanya kiyasai sun cika bakin shi da hancinshi" tuni ya dade da zuwa garin da ba'a dawowa Lokacin da 'ya'yanshi da matanshi suka gama 'yan koke koken al'ada bayan anje anyi jana'idar shi an dawo sai kuma suka fara cuku-cukun lissafin buhunan dake ajiye" domin kada wani yaje ya dauka ba'a sani ba"
A satin da suka fara rigima akan dukiyar da ya
bari" su Lado sune a gaba wajen tayar da jijiyar
wuya suna zage-zage"
kwana goma bayan mutuwarshi aka gaggauta
aka raba gado" babu wanda ya sake komawa
takan wani mamaci tunda dai ba addu'a
'ya'yanshi suka iya ba" noma kawai ya koya
masu" kuma shi zasuci gaba da yi suna ajiyewa suna saran zaifi kowacce shekara tsada
Lado yafi kowa jin dadin wannan mutuwa acikin 'ya'yan mamacin" domin kuwa raba gadon ke da wuya yaje ya sayo sabon babur
(Jencheng)
Sannan kuma duk ranar kasuwan garin idan ta
Zagayo sai ya fitar da buhuna goma a cikin
buhuna dari biyu da arba'in da ya samu anashi
rabon" A cikin wata bakwai ya karar da buhunan ya kashe kudin baki dayansu" daga baya kuma yasayar da babur din da yake yiwa samarin kauyen barazana dashi" yawancin 'ya'yan Alhaji Hashimu sun fuskanci irin wannan matsalar" domin kuwa
basu iya wata sana'a ba" gashi kuma wande ke
matsa masu fita gona tun da Asuba ya fadi" suka shiririce suka kashe dan abinda suka samu na gado"
wasu suka sayar da gonakinsu" masu motoci tuni sunci kasuwa a birni sun kashe kudin"
Rayuwarsu ta kuntata" wasu suka fita birni
neman kudi suna aikin wahala" wasu kuma suna sakin matansu" domin su ragewa kansu aiki"
Abu daya lado ya bari bai sayar ba a cikin kayan gadonshi" wani gidan ne a kusa da kasuwar garin kuma shidin ma wani kansila dake a garin ya so ya saya mahaifiyar lado mai suna HAIRE ita hanashi sayar da gidan"
Tace dashi.