*≈ BARKA DA YAU ≈ (06)*
Don war-ware matsalolin mu ....
Mai Gabatarwa: Mukhtar Yusuf Shamees
*KISHI KUMALLON MATA*
*INJI MALAM BAHAUSHE*
Shin ya kishi yake a gurin matan kwarai? Bari mu dan lek'a
gidan da yafi kowane gida daraja, kuma mai gidan yafi kowane
dan adam daraja da matsayi, Matayensa kuwa suka fi kowace
mace dacen miji Allah ya k'ara yarda agaresu.
Ummuna Aisha da Ummuna Zainab Allah ya k'ara yarda a garesu
sun kasance ko wacce tana jin itace, Ummuna Aisha tana kishi
da Ummuna Zainab haka itama Ummuna Zainab din tana kishi da
Ummuna Aisha, Ummuna Aisha tana jin ai ita ce ta gaban goshi
kuma ita ce a ka auro tana budurwa, ita ma Ummuna Zainab ba
a barta a baya ba domin kuwa mace ce mai matsayi kuma
kyakkyawa, ta kasance tana alfahari da cewa: aurenta ba irin na
sauran mata bane, domin kuwa ita Allah ne da kansa ya aurar
da ita ga Manzon Allah (SAW) daga can saman Al'arshi. Don
haka itace suka fi fafatawa da Ummuna Aisha gurin kishi a cikin
Matayen Manzon Allah (SAW) Allah ya k'ara yarda a garesu.
Duk da kishin da yake tsakaninsu kowacce tana jin ita ce kuma
kowacce tana son ta zama ita ce Sarauniya a birnin fadar zuciyar
mai gida, amma kishin bai rufe musu idanu ba, kuma bai hana
su fadin alkhairi a kan junansu ba, tsoron Allah da tsantseninsu
abin burgewa da ban sha'awa.
Lokacin da hadithatul ifki ya afku(k'azafin da akayi wa Ummuna
Aisha), Manzon Allah ya nemi shawarwarin mutane da jin ta
bakinsu game da Ummuna Aisha, cikin wadanda ya tuntuba har
da Ummuna Zainab (RA) tace: Ya Manzon Allah ina kiyaye
gani na da ji na(bazata fadi abin da bata ji ba, kuma bazata ce
ta ga abin da bata gani ba) ban san komai game da Aisha ba
sai alkhairi, Aisha ai mutuniyar kirkice.
Ita da kanta Ummuna Aisha take cewa: Ita kam Zainab Allah ya
tsareta da addininta, bata ce komai ba sai alkhairi. Allah ya
tsareta da tsantseni.
Ummuna Aisha take cewa:Manzon Allah (SAW) ya ce wa
matayensa "wacce ta fiku tsayin hannu ita zata fara bi na(bayan
mutuwa), sai muka kasance in mun hadu muna gwada tsayin
hannayenmu a bango, ba mu gushe ba muna haka har Zainab ta
rasu, ta kasance bata da tsayi, Allah ya mata rahama bata fimu
tsayi ba, a sannan muka gane ashe abin da ya ke nufi shine
yawan SADAKA.
kuma tace: Ban taba ganin wata mace mai alkhairi a addini da
tsoron Allah, gaskiyar zance, sada zumunci, da girman sadaka
kamar Zainab ba.
Shin haka muke?
Daga
*MIFTAHUL Ilmi*
→ Ga ma su sha'awar shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta whatsApp.
Tags
# Zamantakewar Aure
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
Zamantakewar Aure
Category:
Zamantakewar Aure