Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

*'YAR UWA KI YI HANKALI DA USTAZAN SOCIAL MEDIA!!!*

Allah Sarki,

*Ustazu bawan Allah.*
...
...
A duk lokacin da aka ambaci kalmar *ustazu* musamman a nan kasar Hausa, abin da zai fara zuwa maka a zuciya shi ne ai wani mutum ne bawan Allah mai taka tsan-tsan wajen kiyaye dokokin Allah da yin riko da sunnar Annabi (ﷺ), ustazu mutum ne Mai addini da natsuwa tare da kyawawan dabi'u, da gudun duniya tare da kawar da kai daga dukkan abin da zai jawo masa fushin Ubangiji. Wannan wani dan description ne na yi na ustazu. To amma meyasa na ce a yi hankali da *Ustazan Social Media.?*

Hakika 'ya mace wajibi ne ta kasance mai taka tsan-tsan a fili da kuma a wannan saha ta yanar gizo, namiji ba abin ki sakankance da shi bane a wannan saha domin hausawa su kan ce *Sanin halin mutum sai Allah!*

Ba kowani mai wa'azi da yin post a social media bane yake kasancewa mutumin kirki, ilimi daban, tarbiyya daban. Dayawa wasu a tunaninsu ai duk wanda ke fadakarwa a social media to a bayyane ma mutumin kirki ne, Eh, wajibi ne mu kyautata zato a gare su, amma wallahi da kun san abin da wasunmu suke aikatawa da ko hanya ba za ku so mu hada da ku ba. Kedai kawai roki rufin asirin Ubangiji.

Dayawa wasu mutane da suka dan taba karatun addini su kan bude groups a social media suna posting da sunan tunatarwa da fadakarwa, sai dai daga cikinsu akwai *Bata gari,* wato ustazan Qarya 'yan social media masu yin hakan don su jawo hankulan 'yan mata zuwa gare su, domin a tunaninsu 'yanmatan za su sakankance da su ganin cewa su mutanen kirki ne. A haka za su samu mace a yi ta soyayya, shi kuma a zuciyarsa kawai burinshi ya samu wadda za ta dinga yi masa kalaman soyayya idan yana online, amma da zarar ya sauka shikenan ya mance da labarinta, ita kuma tana can ta saki baki tana murna ai ta hadu da mutumin kirki, amma Wallahi wani da za a tsananta bincike sai a same shi da 'yanmata sun kai goma a social media, kuma dukkansu ya fadi masu ne zai aure su, su kuma a tunaninsu ai ustazu ba zai yi masu karya ba. Qalubale 'yar uwa! Ki shiga taitayinki, ba kowa ake sakankancewa da shi ba, domin daga lokacin da kika fara masa maganar ya turo magabata a yi magana, nan fa za ki ji kame-kame, a bullo ta can a bulle ta can, a haka dai zai samu ya sulale, ko ya kirkiro laifin da zai yi block dinki a bata, shikenan ustazu ya gudu, bayan kuma ya sa ki kin kori samarinki, this is not an estimate, I'm telling you what is exactly happening on social media.

Don haka idan kin kasance a group na fadakarwa, to ki tsaya a karanta karatun da aka turo ko yin tambaya, ko wata magana mai amfani gwargwadon iko, kada ki ce dole sai kin yi soyayya da admin ko wani mutumin kirki a social media, ba wai babu su bane, amma a ganina ai su mutanen kirkin ba rasa su aka yi ba a cikin gari, idan kika kwallafawa ranki soyayyar social media, to lallai ina jiye maki tsoron kamuwa da ciwon zuciya!


Shawarata a gare ki shi ne, idan mutumin da aka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo neman aurenki, to ki aure shi.

Ku lura fa, Annabi (ﷺ) ba cewa ya yi mai addini da dabi'u ba kadai, A'a, sai wanda aka (yarda) da addinin nashi da dabi'unsa.

Allah Ya sa mu fi karfin zukatanmu 👏


*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*