Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Ko kasan ka'idodin rubutu a Hausa
Ka'idodin rubutu a Hausa sune;
SUNAYEN YANKA
Ana fara rubuta sunan yanka ne da babban Baƙi misali;
1. Abubakar ba abubakar ba
2. Dauda ba dauda ba
3. SUNAN ALLAH
i. ALLAH ba allah ba
4. Arrahman ba arrahman ba

SUNAYEN GARURUWA
1. Gombe ba gombe ba
2. Zariya ba zariya
3. Bauchi ba bauchi ba
4. Abuja ba abuja ba
5. Yobe ba yobe

SUNAYEN RANEKU
1. Alhamis ba alhamis ba
2. Juma'a ba juma'a ba
3. Asabar ba asabar ba
4. Lahadi ba lahadi ba
5. Litinin ba litinin ba
6. Talata ba talata ba
7. Laraba ba laraba ba

SUNAYEN MALA'IKU
1. Jibril ba jibril ba
2. Ridwan ba ridwan ba
3. Mika'il ba mika'il ba
4. Maliku ba maliku

SUNAYEN SARAUTU
1. Sarki ba sarki ba
2. Waziri ba waziri ba
3. Galadima ba galadima ba
4. Tolba ba tolba ba
5. Chiroma ba chiroma ba
6. Yarima ba yarima ba
7. Sarauniya ba sarauniya ba

SUNAYEN WATANNI
1. Janairu ba janairu ba
2. Febrairu ba febrairu ba
3. Afrilu ba afrilu ba
4. Satumba ba satumba ba

AMFANI DA WAKILIN SUNA DA DIRKA.
AMFANI DA WAKILIN SUNA DA DIRKA
A harshen Hausa Akwai dirka iri biyu (2)
Ne da Ce.
Ne : Ana amfani dashi ga namiji
Ke: Ana amfani dashi ga mace.
To sau da Yawa zaka ga masu rubutu basa iya banbance yadda ake rubutasu. To ba'a hada wakilin suna da dirka!
MISALI:
1. Ni ne ba nine ba
2. Ni ce ba nice ba
3. Kai ne ba kaine ba
4. Shi ne ba shine ba
5. Ita ce ba itace ba
6. Mu ne ba mune ba
7. Ku ne ba kune ba
8. Su ne ba sune ba
* Na farko shi ne daidai.

AMFANI DA WAKILIN SUNA DA AIKATAU.
To sannan akwai kuma inda ake amfani da wakilin suna da aikatau, wato aikatau shi ne yin wani aiki.
Shi ma a wannan da yawa zaka ga mutane basa iya rabewa tsakanin wakilin suna da aikatau. Misali: Na ci
Sai kaga mutun ya hade shi, to ba´a hadewa. MISALI:
1. Na ci ba naci ba
2. Ka ci, ba kaci ba
3. Kin ci, ba kinci ba
4. Ya ci, ba yaci ba
5. Ta ci, ba taci ba
6. Mun sha, ba munsha ba
7. Kun sha, ba kunsha ba
8. Sun sha, ba sunsha ba
9. Na je, ba naje ba
10. Kin je, ba kinje ba
11. Kun je, ba kunje ba
12. Sun je, ba sunje ba
13. Na yi, ba nayi ba
14. Ka yi, ba kayi ba
15. Kin yi, ba kinyi ba
16. Ta yi, ba tayi ba

WAKILIN SUNA DA LAMIRIN LOKACI.
Sannan Kuma Akwai Wakilin suna da lamirin Lokaci
To Sukuma Wadannan hadasu akeyi.
Amma Sai kaga Wasu suna rarrabawa. Suma bari muka wo Ire-irensu.
Misali:
1. Ina wasa, ba I na wasa ba
2. Kana ba ka na
3. Kina, ba ki na ba
4. Suna, ba su na na
5. Tana, ba ta na ba.

LOKACI SABAU DA WAKILIN SUNA.
"To San nan akwai abinda ake kira kuma Lokaci Sabau da wakilin Suna to Shima wan nan hadeshi akeyi Shima ga misalinsa:
Misali:
1. Nikan je, ba ni kan je ba
2. Kakan je, ba ka kan je ba
3. Yakan je, ba ya kan je ba
4. Takan je, ba ta kan je ba
5. Kukan je ba Ku kan je ba

HARDADDUN KALMOMI.
Sannan akwai Hardaddun kalmomi, su kuma wadannan ana amfani ne da karan-dori wajen rarrabesu. To zaka ga wasu kawai suna rubutasu ne ba tare da sun sanya karan dorin ba.
Su ma bari muga misalensu.
MISALI:
1. A-Kori-kura ba, akorikura ba
2. Babba-da-jaka
3. Ba-ji-ba-gani
4. Ci-rani
5. 'Yan-ba-ni-na-iya
6. Fadi-ka-mutu
7. Ci-ma-zaune
8. Gaya-wa-jini-na-wuce