*MEYA KAMATA MUKOYAWA YARANMU TUN SUNA JARIRAI*
🤱🏻 *Tambaya:* 🤱🏻
Assalamu alaikum warahmatullah malama dan Allah inason ayimin qarin bayani gameda tumbudi, wanda yara suke tun suna jarirai shin yana sallah ko baiyi ?
Sannan dakuma bayani gameda illar basu nono akwance?
🤱🏻 *Amsa:*🤱🏻
Amin,alaikissalam. Tumbudi ba najasa bane, yana sallah! Akasari asaliyyar halittace na wani yaron , amma kuma yaro mai tumbudi yana nuna alamar zai yi yar kiba, sannan alamace ta qoshi na isassar madarar mama, kuma ba matsala bace. Amma bayar da mama ga jarirai daga kwance yana kawo matsalar ziwon kunne, da rashin jarumta ga yara. Sannan naqas ne ga dora tubalin tarbiyya, domin tun asali sunna bata koyar da jama'amar ta cin abinci daga kwance ba sai dai daga zaune cikin nutsuwa, wanda abincin zai kosar dakai da amfanuwa gareka. Amma ke uwa kin baiwa yaro mama daga kwance, idan ya dore da haka gaba ki fara kai duka! Al hali kece kika gadar masa dabi'ar tun jarinta, iyaye kuji tsoron Allah ku rika dora tarbiyyar yara tun jarintaka, da:
🤱🏻 Jure karanta masu *U'ezukuma bie kalimatillahi tamma, wamin kulli shaidanin wa hamma, wa min kulli aynin lamma* domin itace Annabin tsira ke yawan karantawa jikokin shi biyu.
🤱🏻Kwanci kan dama, sai a tare su da tsumma daga bayan su, da idan suka samu bacci zasu yi bacci mai nutsuwa da shaidanu jinnu koh karar wani abu bata saurin tada su, idan kin aje da bismillah
🤱🏻 Ku rika kunna karatun qur'ani a memakon kade kade domin suna saurare, saurare ga kwakwalwar da bata shagala da matsalolin dunia ba, kuma sabon jini sabuwar halitta irin ta yara ba a manwa. Kamar yadda hadisi yanuna: kamar zanene akan dutse! Uwa makarance ta farko, koh dai ki koyar da darussa masu nagarta ko na banza, domin yara basa kalon maganganunki ayukkanki suke duba.
🤱🏻 Ki mu'amalanci dabi'u masu kyau domin kwaikwayo kike bada wa ga yara, da nan gaba zasu fiki iyawa
🤱🏻 Muamalantar kyawawan lafuzza da sa albarka tun suna tsumma, domin komai kika fada suna ji suna gani irin nasu, gasu da qarfin hardacewa
🤱🏻 Idan sun tasa ku koyar dasu cin abinci da dama da karbar abubuwa da hannu biyu
🤱🏻 Ku koyar dasu fara cin abinci da bimillah, da cin abinci da hannun dama bayan an wanko, da cin abinda ke gaban su. Da cikawa godia idan an gama da kuma side hannu da wanko hannun bayan an kammala. Har dauke kwano
Sannan kuma iyaye ku dena:
🤱🏻 Dena sanya jarirai a tsakiyar uwa da uba, wurin kwancia wanda yana haifar da:
🤱🏻 Rashin kunya da fitsara ga yara
🤱🏻 Da idan sun saba raba su da wannan zai yi wuya idan sun girma
🤱🏻 Wannan na koyar dasu bin kwakkwafin iyaye
🤱🏻 Uba namiji Ya dena sanya 'yar shi tsakankanin cinyoyin shi domin yana gadar da fitsara da rashin kunya ga yara mata
🤱🏻 Uwa mace ki dena bari samari na daukar maki 'ya mace domin zasu bata maki ita baki ankara ba
🤱🏻 Uwa mace ki dena hantara da tsawa ga yar ki mace, domin zata:
🤱🏻 Guje maki idan ta girma
🤱🏻 Zata tsoraceki, da bata iya gaya maki gaskiyar alamarinta tun tana kankanuwa
🤱🏻Kina da ranki zata nemi uwar daki koh ta maida alamurran shawarwarin ta ga media kina ji kina gani ta fandare kuma kece umul aba is
🤱🏻 Idan zaki fita kafarki kafar yar ki mace, komai kunsancin ki da mutum koh ciki daya kuka fito kada ki bada amanar yarki mace
🤱🏻 Iyaye ku dena yiwa yara karya, da sunan wayo
🤱🏻 Ku dena daukar yara marasa hankali, da hankalinsu daidai irin nasu. Sannan sun fi manya basira domin basu da abinda ke daukar hankalin su
🤱🏻 Iyaye ku dena sa in sa tsakaninku, domin kuna baiwa yara bakar tarbiyya da mugun koyi a fakaice
🤱🏻 Ku gane zagi, duka hantara da nuna tsana ba uslubi bane na nagartacciyar tarbiyya face hanyar tabarbarewar tarbiyya
👌🏻 Daga karshe nake buga maku misalin magabata masu dauro alwala kafin su shayar da yaran su, masu shayarwa suna addu'e kunnen 'yayan su, masu sanya 'yayan su gaba gaba ga ayukkan alkhairi, kamar salla, juria akan babu, fadar gaskia har ga yara da maida su tamkar manyan mutane wurin neman shawararsu akan abinda ya shafesu idan basu fadi daidai ba ayi masu gyara, da ake kwabar su tare da fada masu dilin kwabar da hujjar aya koh hadisi! Yã ku taron iyayen da suka haifa aka haifesu, kuji tsoron Allah kuyiwa 'yaya tarbiyya a rage samun *Bara-gurbin-shuwagabanni* domin yara sune manyan gobe!
Ina takaicin yanda wasu yan uwana musamman dattijan unguwa dake saurin yanke hukuncin mutuwar mara lafiya ko wanda Numfashin sa ya dauke ta hanyar bayar da bayanin ya mutu ko ta mutu kai tsaye wanda hakan ke sa yan uwa da makusanta saurin shirye shiryen gabatar da jana'iza kamar yanda addinin musulunci ya tanadar
Wanda a bisa bincike da bayanan wasu jaridu dake fitowa a yan kwanakin nan akan samu wasu mutane dakan fada doguwar suma wanda sukan dauki dogon lokaci kafin su farfado wanda da'ace anyi gaggawar binne su shakka babu da labarin yasha bamban
SHAWARA
Yanada kyau yan uwa su bayar da dama ga masana suyi bincike su tabbatar da mutuwar wanda yake wannan hali kafin kai shi kabari sannan yan uwa su gane Gaskiyar magana ba kowani mai aiki a asibiti bane yake da kwarewa a Fannin rashin lafiya ba kowa da sa kar a baiwa kafinta gyaran mota kowa a bashi aikin sa don zama lafiya
Bawai tun daga bakin kofar asibiti wani yace mara lafiyar ku ya mutu ku juyo gida ku fara hako ba. ku tabbatar mara lafiyar yasamu kulawar likita ko kwararren mai ilmi awannan Fannin kafin kai dan uwan ku ga makwanci
Zaku gaskata ni idan kuka tuna da labarin amaryar nan dake samunaka dake jihar Kaduna wacce cikin kankanin lokaci ta gamu da ciwon ciki cikin abunda baifi awanni 2 zuwa 3 ba labari ya iski angon ta cewar ta rigamu gidan gaskiya kasancewar yan uwan amarya basa kusa Hakan yasa akayi jinkiri tun karfe sha daya na safe zuwa karfe 3 da rabi na yamma inda aka gama tabbatarwa ta mutu ana shirye shiryen kai ta makwancinta ta farfado ashe doguwar suma tayi rashin tuntubar masana a Fannin yasa aka so kai ta kabari tunda sauran Numfashinta
Hakan yasa ni dan uwan ku Yarima Gangariya nake Fatan zamu kiyaye tareda daukar darasi
ALLAH YASA YAN UWA MASU ALBARKA
ZAMU GANE MU KUMA DAUKI DARASI
Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, Kano.
Da yawa Musulmi suna tambayar shin ko ya halatta su karbi kyautar kiristoci a ranar kirsimeti, musamman wandanda suke zaune lafiya tare da su, ko suke aiki a guri daya. Ga bayanin da Malamai suka yi dangane da haka:
1. Baya halatta ga Musulmi ya nuna farincikinsa da wannan ranar, ta hanyar aikawa da gaisuwa ko
kyauta ko furanni, ko makamantan su.
2. Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka yanka da sunan wannan rana.
3. Ya halatta ya karbi kautar da za su bashi a wannan ranar. Kamar yadda ya halatta gare shi ya ci
abin da za su ba shi wadanda ba yankawa ake yi ba. Kamar kayan marmari.
4. Dalili kuwa shi ne:
A) Baihaqi ya ruwaito a cikin littafinsa As-Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad Bn Sirin ya ce: an kawo wa Ali, Allah ya kara yarda a gare shi, kautar idin majusawa Nairuz. Sai ya ce: mene ne wannan kuma? Sai suka ce masa, ya Sarkin Muminai yau ranar idin Nairuz ce. Sai ya ce, to kullum ma su yi 'Fairuz'. Wato ya karba, tare da nuna ya ji dadin kyautar.
B) Ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Al-Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu Barzata Al-Aslamy cewa: yana da makwabta majusawa, kuma a duk ranar bukukuwansu suna aiko masa da kyaututtuka gidansa, sai yakan cewa iyalinsa, yaya abin yake?; idan kayan marmari ne to ku ci, wanda kuma ba kayan maramari bane, to ku mayar musu kayansu.
C) Haka kuma ya ruwaito 5/126 cewa: wata mata ta tambayi Nana A'isha ta ce, muna tare da mata
majusawa masu sana'ar shayar da jarirai, to duk ranar idinsu suna aiko mana da kyauta. Sai A'isha, Allah ya kara yarda a gare ta, ta ce mata, abin da aka yanka domin wannan ranar kada ku ci. Ku ci kayan marmari na itatuwa.
Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna idinsu ba shi da wani tasiri wajen ya hana a karbi kyautarsu. Karbar kyautarsu a ranar idinsu da ranar da ba idin ba duk hukunci daya ne, domin wannan ba shi ne taimaka musu ba akan aikinsu na kafirci. Duba Littafinsa Iqtidha' Siratil Mustaqim 2/52.
Sannan a karshe yana da kyau mu fahimci cewa, Ba ya halatta musulmi ya taimaka da yi musu yanka a wannan ranar. Kuma koda musulmi ne ya yanka musu ba za a ci ba.
Allah ka shiryar da mu tafarkinka madaidaici.
Kowa ya taimaka wajen yada wannan sako a matsayin nasa gudunmuwar
1:- Boye talaucinka har mutane su fara tunanin kai me arziki ne
2:- Boye damuwarka a kan abin da aka yi maka har mutane su fara tunanin wannan abin bai dame ka ba
3:- Danne bacin ranka a inda aka bata maka rai har mutane su fara tunanin duk abin da za a yi maka ba zai taba damunka ba
4:- Yin fara'a ga kowa har mutane su fara tunanin ba ka yin fishi
5:- Zamo na kowa har mutane su fara tunanin ba ka da abokin fada
6:- Ka taimaki duk wanda kake tare da shi har mutane su dinga neman taimako a wurinka
7:- Kayanka ya zamo na kowa ko da kayan kowa bai zamto naka ba. Ta haka ne mutane za su ji dadin zama da kai
8:- Ka zamto mai kawar da kai a kayan wani har mutane su fara tunanin rayuwar duniya ba ta dameka ba
Mu kasance masu hakuri da junanmu domin idan mun mutu mu samu kyakkyawan karshe
Ubangiji Allah ka sa mu dace ka sa mu gama da duniya lafiya