Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Me yakamata mu koyawa yaranmu tun suna jarirai

*MEYA KAMATA MUKOYAWA YARANMU TUN SUNA JARIRAI*

🤱🏻 *Tambaya:* 🤱🏻
Assalamu alaikum  warahmatullah malama dan Allah inason ayimin qarin bayani gameda tumbudi, wanda yara suke tun suna jarirai shin yana sallah ko baiyi ?
Sannan dakuma bayani gameda illar basu nono akwance?

🤱🏻 *Amsa:*🤱🏻
Amin,alaikissalam. Tumbudi ba najasa bane, yana sallah!  Akasari asaliyyar halittace na wani yaron , amma kuma yaro mai tumbudi yana nuna alamar zai yi yar kiba, sannan alamace ta qoshi na isassar madarar mama, kuma ba matsala bace. Amma bayar da mama ga jarirai  daga kwance yana kawo matsalar ziwon kunne, da rashin jarumta ga yara. Sannan naqas ne ga dora tubalin tarbiyya, domin tun asali sunna bata koyar da jama'amar ta cin abinci daga kwance ba sai dai daga zaune cikin nutsuwa, wanda abincin zai kosar dakai da amfanuwa gareka. Amma ke uwa kin baiwa yaro mama daga kwance, idan ya dore da haka gaba ki fara kai duka! Al hali kece kika gadar masa dabi'ar tun jarinta, iyaye kuji tsoron Allah ku rika dora tarbiyyar yara tun jarintaka, da:

🤱🏻 Jure karanta masu *U'ezukuma bie kalimatillahi tamma, wamin kulli shaidanin wa hamma, wa min kulli aynin lamma* domin itace Annabin tsira ke yawan karantawa jikokin shi biyu.

🤱🏻Kwanci kan dama, sai a tare su da tsumma daga bayan su, da idan suka samu bacci zasu yi bacci mai nutsuwa da shaidanu jinnu koh karar wani abu bata saurin tada su, idan kin aje da bismillah

🤱🏻 Ku rika kunna karatun qur'ani a memakon kade kade domin suna saurare, saurare ga kwakwalwar da bata shagala da matsalolin dunia ba,  kuma sabon jini sabuwar halitta irin ta yara ba a manwa. Kamar yadda hadisi yanuna: kamar zanene akan dutse! Uwa makarance ta farko, koh dai ki koyar da darussa masu nagarta ko na banza, domin yara basa kalon maganganunki ayukkanki suke duba.

🤱🏻 Ki mu'amalanci dabi'u masu kyau domin kwaikwayo kike bada wa ga yara, da nan gaba zasu fiki iyawa

🤱🏻 Muamalantar kyawawan lafuzza da sa albarka tun suna tsumma, domin komai kika fada suna  ji suna gani irin nasu, gasu da qarfin hardacewa

🤱🏻 Idan sun tasa ku koyar dasu cin abinci da dama da karbar abubuwa da hannu biyu

🤱🏻 Ku koyar dasu fara cin abinci da bimillah, da  cin abinci da hannun dama bayan an wanko, da cin abinda ke gaban su. Da cikawa godia idan an gama da kuma side hannu da wanko hannun bayan an kammala. Har dauke kwano

Sannan kuma iyaye ku dena:

🤱🏻 Dena sanya jarirai a tsakiyar uwa da uba, wurin kwancia wanda yana haifar da:

🤱🏻 Rashin kunya da fitsara ga yara

🤱🏻  Da idan sun saba raba su da wannan zai yi wuya idan sun girma

🤱🏻 Wannan na koyar dasu bin kwakkwafin iyaye

🤱🏻 Uba namiji Ya dena sanya 'yar shi tsakankanin cinyoyin shi domin yana gadar da fitsara da rashin kunya ga yara mata

🤱🏻 Uwa mace ki dena bari samari na daukar maki 'ya mace domin zasu bata maki ita baki ankara ba

🤱🏻 Uwa mace ki dena hantara da tsawa ga yar ki mace, domin zata:

🤱🏻 Guje maki idan ta girma

🤱🏻 Zata tsoraceki, da bata iya gaya maki gaskiyar alamarinta tun tana kankanuwa

🤱🏻Kina da ranki zata nemi uwar daki koh ta maida alamurran shawarwarin ta ga media kina ji kina gani ta fandare kuma kece umul aba is

🤱🏻 Idan zaki fita kafarki kafar yar ki mace, komai kunsancin  ki da mutum koh ciki daya kuka fito kada ki bada amanar yarki mace

🤱🏻 Iyaye ku dena yiwa yara karya, da sunan wayo

🤱🏻 Ku dena daukar yara marasa hankali, da hankalinsu daidai irin nasu. Sannan sun fi manya basira domin basu da abinda ke daukar hankalin su

🤱🏻 Iyaye ku dena sa in sa tsakaninku, domin kuna baiwa yara bakar tarbiyya da mugun koyi a fakaice

🤱🏻 Ku gane zagi, duka hantara da nuna tsana ba uslubi bane na nagartacciyar tarbiyya face hanyar tabarbarewar tarbiyya

👌🏻 Daga karshe nake buga maku misalin magabata masu dauro alwala kafin su shayar da yaran su,  masu shayarwa suna addu'e kunnen 'yayan su, masu sanya 'yayan su gaba gaba ga ayukkan alkhairi, kamar salla, juria akan babu, fadar gaskia har ga yara da maida su tamkar manyan mutane wurin neman shawararsu akan abinda ya shafesu idan basu fadi daidai ba ayi masu gyara, da ake kwabar su tare da fada masu dilin kwabar da hujjar aya koh hadisi! Yã ku taron iyayen da suka haifa aka haifesu, kuji tsoron Allah kuyiwa 'yaya tarbiyya a rage samun *Bara-gurbin-shuwagabanni* domin yara sune manyan gobe!