Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

MURMUSHIN ALKAWARI-13
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Zuciyarta ta harba sa'ar datayi ido biyu da saurayi mai tabarau koda ta sake kallon hoton da kyau sai taga ai da irin tabaran daya bata ma ya dauki hoton.
.
Shine... Wallahi... A ina ka sami hotonsa?
Lari ta tambaye shi hawaye na kokarin sake kubuce mata nafiu ya dubeta yace.
Wanene baisan salim ba? Ai sai in mutum baya kallon finafinan hausa. Lari ta zabura ta mike tsaye jikinta na rawa tace.
Dan Allah ina zan sake ganinsa a... Ina yake. Nafiu ya dauki sandarsa sannan shima ya mike ya dubeta cikin damuwa yace.
Gara ma ke kinyi sa'a Allah ya nuna miki shi a zahiri ni in ba'a talabijin ba ko a hoto sai ko a mafarki amma ban taba ganinsa azahiri ba.
Kana nufin kenan ba ka taba ganinsa ba? Lari ta tambaya cikin karyayyiyar murya Nafiu ya girgiza kai.
Mutumin KANO ne. Ya danyi shiru yana duban lari cikin damuwa.
Amma inayi miki fargabar cewa kin dauko dala ba gammo domin salim ba karamin mutum bane kuma tun da nake arayuwata ban taba ganin mutum da farin jinin salim ba idan baki sani ba to yau ki sani duk kusan yan matan garin nan dake kallon finafinan hausa kaunarsa sukeyi. Sau da yawa zakiji suna zaginsa saboda hassada amma ina tabbatar miki da cewa azuciyarsu basuda wani abin kauna kamarsa ance dayawa daga cikin matan masu karancin tunani da hankali sun sha rabuwa da mazajensu saaboda shi.
Wannan shi yasa nace kin dauko dala babu gammo tunda yan matan birni ma wayayyu yaya suka kare dashi ballantana ke... Bayan kuma naji suna cewa wai yanada shegen girman kai kamar ibilishi. Lari taji kafarta ta fara rawa.
Indai a kano yake sai na nemo shi koda zan zagaye fadin garin ina tambaya. Inason kuma ka sani cewa ni sa'ar dana hadu dashi bai nuna min wani girman kai ba ko kankane domin shi ya kirawoni ya saye nonona muka dade muna hira dashi yayi min kyautar naira dari bakwai sannan daga karshe dana fasa masa sunana yace wai sunan na da dadi. Nafiu yayi tsaye yana kallonta sororo baki bude domin duk abinda take fada ta bayan kunnensa yake bi. Yasha jin a birni ana zancen girman kan salim in kuwa abunda ake fadi gaskiya ne yasan babu abinda zai hada salim da lari to amma kuma me zaisa tace sun hadu da salim in basu hadu din ba?
Wai Allah lari da gaske kike kin ganshi da idonki? Nafiu ya tambaya akan shakka lari ta dauko tabaran dake gurinta ta mikawa nafiu tace.
Kaga wannan tabaran ma shi ya bani in kuma baka yarda ba sake duba hoton zakaga da shima ya dauki hoton. Nafiu ya karbi tabaran cikin mamaki sannan ya bude bangon littafin ya sake kallon tabaran dake fuskar saurayin sannan ya dubi na hannunsa. Ko shakka babu irinsa daya. Tsahon lokaci yana kallon hoton sannan saiya dago kai ahankali ya dubeta.
Yanzu wane irin taimako kikeso agareni?
Ya tambayeta yanzu kam ya tabbata duk abinda ta fada gaskiyane.
Babu abinda nake so kayi min saika rufa min asiri sannan yau da daddare ka rakani nabar garin nan zuwa kano. Nafiu ya girgiza kai yace.
Ke lari baki taba zuwa kano ba tunda kike bazaiyu ba yau tashi daya ki shiga garin cikin dare lari ta dada matsawa kusa dashi ta tausasa murya.
Da'a aura min ja'e maketaci dana bar garin nan cikin dare wanne kafi so? Nafiu ya danyi jim cikin rudani ya riga yasan cewa ja'e macuci ne babba azzalumi. Ba lari dayake kauna ba ko akuyar dayake kiwo bazai so ta auri Ja'e ba don haka saiya dubi lari yace muryarsa na rawa..
Gara.... Ki Gudu... Da Ki Auri JA'E.
.
**** **** **** ***** **** *****
.
SIDI mai jaka yayi shiru sa'ar dayazo nan sannan ya dubeni yace Nas ina fatan kana biye dani akan wannan dogon zaren labari. Na gyada kai nace.
Kwarai kuwa baba amma ni nakasa gane irin wannan wauta ta yan mazan zamani yaya baki taba zuwa gari ba bakisan kowa agarin ba zaki tafi neman wanda shime yiwuwa ma tu agurin da kuka hadu ya manta dak? Sidi mai jaka ya canko wasu dankwala dankwalan tubanai guda biyu ya jefa abaki. Idanunsa suka fara diga kamar kuturu saboda yaji amma duk da haka dattijon bai nemi ruwa ba. Azuciya nace lallai idan naci gaba da kawo tubanin nan watarana sai nayi kisan kai.
Ai Nas kayi mamakin al'amarin na irin wadannan mata domin yadda suke kaunar jaruman shirin fim abin ya wuce tunanin mutum amma banga laifinsu ba domin irin yadda matasan jaruman ke kwaikwayon abu ashirin fim saika rantse da Allah da gaske ne wannan shike rudar wadannan mata amma fa nas kada kayi kuskuren fahimtar zaren labarin nan kaga Lari kaunar salim takeyi tsakani da Allah badon jarumtakarsa ta shirin Fim ba.
Hakane nace dashi.
Yawwa Nas. Bari to nayi sauri na karasa maka wannan zaren labarin kafin na dauki na karshe wanda daga shine zan hada maka zararrukan guda uku guri guda na kullesu.
Ina sauraron ka baba sidi. Nace dashi sannan na gyara zama.
Yawwa nas to adaren wannan rana saia aka yi rashin sa'a domin tun da magariba aka kece da ruwa kamar da bakin kwarya. Wannan ita tasa nafiu bai sami damar zuwa gidansu Lari da karfe takwas ba kamar yadda sukayi alkawari sai karfe tara saura. Nafiu ya jinkirta zuwansa tun farko ne domin a tsammaninsa