MURMUSHIN ALKAWARI-14
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
A tsammaninsa za'a tsagaita ruwan to amma ganin ruwan sai karuwa yakeyi shiyasa shi biyowa cikin duhun daren ruwa na dukansa ya shiga rigarsu Lari.
Sa'ar da nafiu yakawo rigar saiya dabarbarce ya rasa abinda ya kamata yafari domin ayadda suka shirya a yammacin ranar sun yanke cewa zai sami lari ne agindin wata katuwar bishiyar mangwaro dake arewa da garken shanunsu to amma ruwan saman da ake ketawa ayanzu kamar da bakin kwarya shiyasa shi cikin wasi wasi domin yasan abune mai wuya lari ta iya jiransa cikin wannan uban ruwan da ake shekawa.
Nafiu yayi tsaye cikin duhun jikakken daren ruwan na dukansa babu ko kakkautawa lokaci lokaci yakan sa hannunsa ya share ruwan dake zuba akan fuskarsa daga inda yake tsaye yana iya hangen duhu duhun bukkokin dake rigar sannan lokaci lokaci yakanji bololon kukan shanu jifa jifa. Nafiu yaji dadin duhun daren dakuma ruwan da akeyi ba don komai ba kuwa sai don tunanin cewa muddin ja'e ya fuskanci abinda yake niyyar aikatawa to kashinsa ya bushe. Tsahon lokaci nafiu na tsaye agurin can sai wata zuciyar tace dashi zzagaya mana zuwa gindin bishiyar mangwaron dake bayan gidan jikinsa na rawa ya juya zai nufi gindin bishiyar mangwaron sannan ne to yaji siririyar muryar a bayan.
Nafiu. Cikin sauri ya juya a dan tsorace adaidai lokacin daya hangi duhunta tana fitowa daga bayan rumbun dake daf dashi. Muryarsa na rawa ya gyara sandar dake hannunsa.
Lari... Ya kira sunanta cikin sauri ta matso inda yake hannunta na dama dauke da kullin yan tsummokaranta sai digar ruwa sukeyi kamar algararar goro haka nan itama ajike take jagaf kayan dake jikinta sun manne ajikinta sirirantarkar ta tafito fili.
Tun dazu nake jiranka har na fara tunanin ko bazaka zo ba. Nafiu ya girgiza kai.
Kema kinsan ai dole na zo bazan iya saba miki alkawari ba. Ya danyi shiru sannan saiyace.
Anya kuwa lari bakya bar tafiyar nan ba sai gobe kinga dare yayi ga ruwa kuma zaki tafi bakon gari me yiwuwa tun daga nan har can kanon ruwa akeyi kinga kuma sai kusan asuba zaku sauka a kano.
Lari ta gyara kullin dake hannunta ya lura da cewa jikinta sai rawar sanyi takeyi.
Ni dai in zaka taimakeni ka taimakeni Nafiu amma nayi alkawarin yau bazan kwana a rigar nan ba. Tana gama fadin haka saita juya ta fara tafiya nafiu yabita abaya sukaci gaba da tafiya sannu ahankali har suka kawo dab da rigarsu nafiu adaidai lokacin ne ya juyo ya dubeta yace.
Dan jirani ina zuwa. To kada ka dade kaga dare yana karati.
Aka saki wata katuwar aradu. Kasa ta girgiza sararin samaniya ya haskake amsa kuwwar tsawar ya watsu acikin dajin lari ta matsa aguje ta rike hannun nafiu a firgice.
Na shiga uku tace a tsoace idan har akwai abinda take tsoro to araduce don tun tana karama ta kashe yayanta agurin kiwo bayan dan lokaci sai lari ta saki hannun nafiu tace.
Jeka ka dawo cikin sauri nafiu ya nufi rigarsu ba'a dade ba sai lari ta hango shi hanye da jaki.
Wannan fa me zakayi da jaki? Lari ta tambaya nafiu ya dubeta da murmushi yace.
Kawo miki nayi ki hau domin tafiyar nada dan nisa zuwa cikin gari ga kuma cab. Lari taji tausayinsa ya kamata saboda ganin ganin irin wahalhalu da kuma soyayyar dayakeyi agareta duk kuwa da cewa yasan bashi take kauna ba.
Na...gode nafiu abin kawai datace dashi kenan sannan saita kama jakin nafiu ya taimaka mata ta hau.
.
Karfe tara da yan mintuna na dare suka isa babbar tashar motar ta garin yola suna digar ruwa suna isowa suka sami mota fijo mai zuwa kano mutum daya kawai ake jira.
Sa'ar da suka isa gindin motar sai mutanen dake cikin wata rumfar kwano suna fakewa ruwa suka zubo musu idanu cikin mamaki.
Oh! Ga wata kyakkyawar bafulatana tasha dukan ruwa wani mai shayi dake fakewa ruwa acikin rumfar yace.
Lari ta sauko daga kan jakin sannan ta dubi nafiu adaidai lokacin da sauran fasinjojin dake fakewa a rumfar suka fara shiga motar domin sun fahimci cikon fasinjansu daya ya bayyana.
Nagode... Nagode nafiu lari tace idanunta na zubar zubar da hawaye cikin sauri nafiu ya dauke kansa gefe guda sannan ya lalubi aljihunsa ya dauko kullin wata leda fara ya kunceta daga ciki ya dauko laya da kudi ya mika mata yace.
Ga wannan layar maganin tsautsayi ce in dai kina tare da ita babu abinda zai taba samunki in Allah ya yarda wannan kuma kudin dubi biyar ne kawai kiyi hakuri lari Wallahi su kenan nake dasu daka da waje suma tunkiyata na sayar dazu da yamma....
Lari ta dauki layar sannan ta mika masa kudin tana girgiza kai tace.
Haba Nafiu ai wahalar tayi yawa layar dai na karba amma kudin ka rike abinka wannan taimakon ma dakayi min ya isa bazan taba mantawa dakai ba. Nafiu ya girgiza kai yana kallon motar dake gabansu.
Kada kiyi min haka Lari saboda kawai na baki kudin nan na sayar da tunkiyata. Dazu domin nasan idan kinje birni zaki bukace su... Kuma wannan itace kyauta ta takarshe agareki. Lari taji hawaye ya subuce mata tausayinsa ya dada kamata.
Nafiu nagode. Ta fashe da kuka bazan taba mantawa dakai ba inason kuma kasani cewa da ace ban hadu da salim ba..
Tags
# adabin hausa
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
adabin hausa
Category:
adabin hausa