Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

MURMUSHIN ALKAWARI-15
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Da ace ban hadu da salim ba babu wanda zan iya aura aduniya sai kai.... Kuma... Ta sake fashewa da kuka yanzu ma ina kaunarka Nafiu.
.
Adaidai lokacin ne direban motar yafara danna hon. Cikin sauri Lari ta nufi motar nafiu na biye da ita abaya suna zuwa saita juyo ta dubeshi tace.
To nafiu sai watarana nagode tana shiga motar sai hawaye suka zubo akan kumatun nafiu. Lari ta juyo ta cikin gilashin motar tayi masa kallon karshe.
Lari ta dago masa hannu sa'ar da motar tafara tafiya. Nafiu yayi kokarin shima ya daga mata hannun amma sai yaji hannun yayi masa nauyi. Wani zazzafan hawaye ya zubo akan kumatunsa. Ya riga yasan laifi ya aikata babba ya taimaka yarinyar mutane ta shiga duniya... Allah ya tsareta yace cikin zuciyarsa.
Data auri Ja'e ya sake maimaitawa kansa gara ta shiga uwa duniya: wannan shi ya dan lallami zuciyarsa domin a tunaninsa akalla dai yana da hujja ko da kuwa rarrauna ce. Koda motar tafara tafiya sai Lari tajuyo domin tayi masa kallon karshe Nafiu ya ganta itama ta ganshi azuciyarta tayi fatan Allah ya sake hadasu awata rana awani zamani haduwa ta farin ciki ko ta rama masa alherin dayayi mata. Abinda bata sani ba shine BAZATA SAKE GANINSA BA HAR ABADA.
.
UKU 3
KANO
JUMA'A 10 SATUMBA 2004
.
Sidi mai jaka ya dubi agogonsa lokaci guda ya share gumi da gefen hannun ribabbiyar rigarsa.
Kai! Lallai wannan zamani lokaci na gudu dubi Nas har karfe goma sha biyu saura yan mintuna.
Gaskiya ne Nace dashi.
Ina ganin ai saikayi sauri ko ma gama kafin azahar. Na danyi shiru.
Kada dai kace min wannan shine karshen zaren wannan labarin?
Sidi mai jaka yayi murmushi ya dauki busasshshiyar kafarsa daya ya dora akan yar uwarta sannan ya harari kwanon tubanin cikin farin ciki domin duk dayake ya cinye sama da rabin tubanin amma har yanzu da saura akalla dunkule ashirin acikin kwanon.
Kaima kasan ai karshen zaren labarin kenan tunda dai lari ma ta nufi Kano. Sidi mai jaka yace dani yana kokarin sake canko tubani.
Nayi mamakin irin yadda wannan tsoho yake hadidiyar wannan abun batareda ya nemi ruwan sha ba. Meyiwuwa irin cikin rakumine dashi. Nace cikin raina.
Sidi mai jaka yaja wata doguwar hamma kamar zai yaga baki dakyar ya samu bakin ya rufu.
Nas yanzun nan bada dadewa ba zan fara saka maka zaren labarina na uku wanda atsakiyarsa ne zan daura ma wadannan zararrukan labarin biyu da muka riga muka saka. Amma kafin wannan lokacin ina son ka bani aron zuciyarsa mu koma nan kano. Cikin wata katon gida dake cikin Nassarawa gidan da aka kashe masa kudi kamar ba'a so domin tunda nake jin labarai iri daban daban ban taba jin labarin almubazzarin gida ko kuma ince gidan da aka yiwa almubuzzaranci ba kamar wannan.
Cab! Nace dashi baki bude wannan wane irin gidane kuma ? Gidan wanene? Sidi mai jaka yayi gyaran murya sannan ya dubeni da murmushi yace.
Kafin nafada ma ko gidan wanene ina son na fara zayyana maka hoton wannan gidan sannan saimu koma cikin kayataccen dakin shakatawar muga abinda ke faruwa.
Ina sauraronka. Nace dashi dan tsohon yayi shiru na dan lokaci yana susar farin gashin gemunsa idanunsa na kallon sama me yiwuwa ganyen bishiyar durumin damuke zaune a karkashi yake kllo. Babu mamaki kuma zararrukan labarin yake jajjonawa kafin yafara sako min shi amike. Tsahon lokaci yana cikin wannan hali kamar mai mafarkin rana can sai ya dube ni yace.
Nas wannan gida danake baka labari acikin nassarawa yake nan garin kano gidan yar karamar aljannar duniya ce wacce kayatuwarsa tasa har mutane suke tunanin ba karamin karambani bane ace wai jarumin finafinan hausa ne ke zaune agidan. Mutane da yawa na ganin cewa ko wani babban mai mukami ne acikin gwamnati ya mallaki wannan gida dole ne asashi sahun almubuzzarai.
Ance wai asalin wanda yasa aka gina wannan gida wani bature ne dan kasar burtaniya da aiki yakawo shi garin na tsahon shekara biyar.
Tun daga can yazo da tsarin gidan azane a takarda dan haka da aka tashi za'a gina gidan sai aka sami katon fili wanda ya ishi ayi filin wasan kwallon kafa har guda uku akayi ginin gidan atsakiyar filin sannan sai aka zagaye shi da alatun duniya. Ance idan kana tsaye atsakiyar babban dakin shakatawar gidan zaka sami kanka kana mai fuskantar kofofi guda hudu kudu da arewa gabas da yamma. Wadannan kofofi duk na katako ne kirar kwararru wanda akayi masa ado da ruwan gwal. Idan ka bude kofar dake bangaren kudu zaka sami kanka kana mai fuskantar wata katuwar baranda kirar zamani irin salo na kasar SIN.
Wannan baranda kai tsaye filin fakin din motoci na gidan take kallo dake farfajiyar gidan.
Idan kuwa ka bude kofar arewa dake falon zaka sami kanka kana mai fuskantar wani katon lambu ni'imtacce wanda ke shake da bishiyoyi iri iri na ya'yan itatuwan alfarma dangin zaki. Saidai ka shiga kawai ka dauko abinda kake son sha ka dawo cikin falon ta kan wata matattakalar bene guda shida wacce ke lullube da shudin kishin.
Idan ko ka bude kofar dakin shakatawar ta gabas zakayi ido biyu ne da katon filin wasannin motsa jiki wanda