MURMUSHIN ALKAWARI-16
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Zakayi ido biyu ne da katon filin wasannin motsa jiki wanda ke dauke da kowace irin na'ura da mutum ke bukata na game da motsa jiki kofar karshe dake kallon yamma itace zatayi maka jagora kai tsaye zuwa katon ramin wanda na zamani wanda aka gina shi da fasalin shan zuciya an zagaye shi da furanni da kuma kujeru da yan kananan gadaje na hutawa da kuma lemomin alfarma da kan iya kare ka daga hasken rana idan ka bukaci hakan.
Sidi mai ja yayi shiru yana mayar da numfashinsa.
Idan nace zanci gaba da fasalta maka tsarin wannan gida sai munyi kwana uku ban gama ba domin da zan fara tsara maka yanayin bandakin kawai dake gidan sai mukai har magariba bankai ga siffanta ma kyawun shawar dake feso ruwan wanka a bandakin ba. Don haka abinda nake so dakai Nas shine ka biyo ni sannu ahankali mu koma cikin dakin shakatawa domin muga wainar da ake toyawa.
To ai kuma baka fada min ko gidan wanene ba. Na katse shi idi mai jaka yayi murmushi yace. Haba nas wa kake tsammanin zai mallaki wannan gida azuciyarka idan ba salim ba.
Salim! Na kira sunan cikin kaduwa.
Kwarai kuwa salim. Gidansa ne akalla dai yan mujallar fim sunce wai gidansa ne to amma jita jita na cewa wai haya yakeyi agidan to koma dai menene bari mu shiga falon gidan mugani.
To baba sidi.... Ina sauraro. Nace sannan na dada gyara zama domin ga alamu yanzu ne ma za'a fara labarin.
Sidi mai jaka ya mika busashshen hannunsa zuwa cikin kwanon tubanin ya damko wani kato mai kama da kwado ya jefa abaki ya tauna sau uku sannan ya hadiye mukut. Kamar maciji kana ya dubeni yace.
Nas acikin wannan dandasheshen dakin shakatawa na alfarma fitacciyar jaruma Kalima ce zaune akan wata kujerar alfarma dake daf da tagar dake kusa kofar arewa tana kallon ya'yan itatuwa dangin zaki dake cikin lambun.
Jaruma kalima doguwa ce wankan tarwada shekarunta ashirin da uku amma zaka iya kuskurenta asha shida domin ko kusa ko alama yawan shekarunta bai fito fili akan fuskarta ba. Me yiwuwa kwarewa ce da iya sa hoda babu mamaki kuma jin dadi ne yayi mata yawa.
Kalima sanye take da Jar riga shat da shudin wando jeans wadana sukayi matukar dame jikinta kanta babu dankwali sai bakin gashinta a fili yana sheki da daukar idanu kamar fasassun kwalabe acikin rana. Takalmin dake sanye akyawawan kafafunta launin madara ne mai tudu kamar dutsen guga daga nesa idan ka hange shi saika dauka jirgin ruwane na wasan yara. Kalima ta dora kafarta daya akan daya sannan rungume akirjinta wani katon mutum mutumine na karen ruwa mai gashi tana wasa dashi. Kwalin alewa cakulet adaf da gwiwar hannunta lokaci lokaci saita dauki cakulet ta jefa baki tana tauna abinta sannan saita dubi mutum mutumin karen ruwan tayi masa murmushi kai ka rantse da Allah me raine to amma fa duk abinda take jarumi salim na gefe guda yana kokarin sa takalminsa kuma yana lura da ita.
Ya batun maganar mu? Salim yace a tausashe batareda ya dubeta ba baikuma tsaya dasa takalminsa ba. Kalima ta shafi karen ruwan dake cinyarta sannan ta jefa dunkulen cakulet abakinta ta kalli cikin lambu ta taga.
Wacce maganar kenan? Salim yagama sa takalmin ya dago ya dubeta cikin damuwa yace.
Haba kalima yanzu ashe munyi ta magana daya kenan kamar karatu?
Kalima ta sauke kafarta dake kan daya sannan ta limshe idanu kana ta bude su lokaci guda kamar idanun yar tsanar roba.
Nifa na riga na fada ma salim bashine agabana ba.
Ba Menene agabanki ba? Salim ya tambaya yana dubanta.
Aure. Ko ba shi kake nufi ba? Salim ya sunkuyar dakai kasa cikin takaici na tsawon lokaci sannan saiya dago kai ya dubeta yace a tausashe.
Idan kikayi min haka bakiyi min adalci ba Kalima. Kalima ta juya idanunta sama tace.
Oh salim kenan kaine dai bakayiwa kanka adalci ba don yanzu ina ganin aikayi hankalin da ya kamata ka banbance tsakanin soyayya da abota.... Koda yake dai nasan kai ka wuce abokina ma saidai ko ubangidana ko kuma ince babana aduniyar fim.
Salim ya mike daga inda yake zaune sanan ya nufi kan kujerar da take zaune ya zauna kusa da ita lokaci guda kuma ya dauke mutum mutumin karen ruwan dake kan cinyarta ya dora shi akan cinyarsa. Sannan saiya dada tausasa muryarsa yace.
Yanzu ashe kalima ba kya tausayawa zuciyata ba ? Kina ganin abinda kikeyi gareni shine hanyar data dace ki yaba alherin danayi miki abaya?
Yanayin fuskar kalima ya sauya nan da nan kamar yadda kalanzir kan sauya yanayin ruwa.
Kada kayi min gori salim kada kuma ka zargeni da rashin godiya nasan cewa ka taimakeni iya taimako ka mayar mutum aduniyar fim adalilinka nayi suna aduniya kowa yake son ganina amma inason ka sani cewa bamu yi yarjejeniya da kai cewa idan ka taimakeni zan aure ka ba ko munyi ? Salim yaji wani tsini mai kamar kibiya ya soki zuciyarsa.
Bazan ce bana sonka ba salim. Kalima taci gaba da cewa musamman ma idan na tuna da irin taimakon dakayi min arayuwata amma ina son ka sani salim agaskiya ni bazan munafarce ka ba tun kafin mu had dakai nake bala'in sonka amatsayinka na kwararren jarumin fina finan hausa amma BA SO BA..
Tags
# adabin hausa
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
adabin hausa
Category:
adabin hausa