Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

MURMUSHIN ALKAWARI-17
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima A. Gangariya
.
Amma BA SO irin na aure ba... Bansani ba ko nan gaba idan ka dage da addua'a me yiwuwa kafara shiga raina amma ayanzu kam ba aure ne agabana ba. Tana gama fadin haka saita mike tsaye ta wuce kai tsaye zuwa kan kujerar daya baro ta barshi shi kadai zaune dauke da mutum mutumin kare.
Salim yaji kansa yafara juyawa kamar ana yi masa wasa da gare gare acikin kwakwalwa.
Yanzu ashe duk bayan mutuncin danayiwa yarinyar nan haka zatayi min? Ya tambayi kansa ga mamakinsa saiyaji wani zazzafan hawaye ya subuce masa cikin sauri saiya sunkuyar da kansa kasa ya boye fuskarsa ajikin mutum mutumin karen ruwan domin baya son kalima ta fahimci cewa kuka yakeyi dominta.
Sannan ahankali sai zuciyarsa ta hasko masa hoton yammacin da aka tashi da muku mukun sanyi ranar wata lahadi da daddare ranar daya tsinci Kalima agefen titin gidan zoo a tsugunne jikin wani tsohon gini jikinta na rawar sanyi kamr kaza. Salim bazai taba mantawa da ranar ba. Su hudu ne suke tafiya acikin marsandin salim akwai abokinsa Faruk wanda ke zaune agaban motar saikuma wasu yan mata guda biyu dake zaune bayan motar dukkaninsu jaruman shirin fim ne. Salim na kokarin tsallaka titi kenan sai fitilar motarsa ta hasko masa wata budurwa ita kadai atsugunne jikin wani kangon gini da ba'a kammala ba. Tana sanye da kodaddiyar atamfa amma kyawunta bai bari salim ya lura a tsummar atamfar ba.
Wannan fa? Salim ya tambayi faruk sa'ar daya hangi yarinyar. Faruk ya zunkuda kafada yace.
Waya sani... Me yiwuwa wata wahalliyar ce tabaro garinsu ta taho neman shiga fim. Ka san kullum abin sai karuwa yake. Salim ya dada haska budurwar dake tsugunne sannan ne to yaji gabansa yafadi Ras!! Domin hasken fitilar tasa ya dauko masa tsantsar kyawun daya dade baiga irinsa ba aduniyar fim.
Kai! Faruk amma ba akwaita kaga fuskarsa sai sheki takeyi...
Maza dai ka dauki aljana uban dauke dauke daya daga cikin yan matan dake bayan motar mai suna SAMIRA tace dashi. Itama kamar sauran daruruwan mata ta dade tana kaunarsa amma aboye domin tasan koda ta bayyana ra'ayinta ma abanza. Salim ya dauke kan motar ya nufi gindin tsohon ginin.
Ina kuma zaka naga ka dauke kan motar?
Mu da muke sauri salim mu fa ake jira kasan kuma shegiyar mitar SALLAU. Salim yayi murmushi yace.
Jikina ne yake bani cewa yanzun nan zan tsinci dami a kala. Faruk ya dubeshi cikin mamaki sannan ya sauke gilashin motar dake bangarensa yace.
Kana nufin gurinta zaka? Ya nuna budurwar dake rabe ajikin bango. Salim ya gyada kai.
Fuskarta tayi min ina ganin zatayi kyau idan aka dora mata kyamara waya sani ma ko ita zansa a cikin fim dina na GAIBU. Faruk ya muskuta acikin motar ya dubi salim cikin damuwa.
Gaskiya salim yakamata ka rage yawan kwashe kwashe ku yakamata ku ringa yiwa na kasanku fadan yin haka amma gashi kana kokarin aikatawa..... Kawai daga ganin yarinya bakasan daga inda take ba. Mutumiyar kirki ce munafukace baka sani ba babu wani bincike saika fara kokarin janyota jikinka... Salim yayi tsaki.
Duk wanan surutun dakakeyi shirme ne da yaushe na hadu da ita da har zan binciketa... Amma tunda bincike kake so muyi bari inje to na binciketa. Kafin faruk ya farga har ya taka birki adaf da yarinyar ya bude kofa ya fice abinsa.
Dan Allah rufe mana gilashin motar nan sanyi mukeji yan matan biyu dake bayan motar sukace da faruk a fusace ba sanyi ne ke damunsu ba. Halayyar salim ce ke damunsu.
Faruk yabi salim da kallo sa'ar daya nufi inda budurwar take zuciyarsa na kuna wannan shine abinda ke hada shi da abokinsa salim taurin kai da kuma rauni akan mata gashi idan yayi niyya babu wanda ya isa ya hana shi yin abu.
.
Budurwar ta daga kai ta kalli salim atsorace sa'ar dataji shi tsaye akanta kamar an jefo shi sannan ba'a dade ba sai fuskarta ta washe cikin farin ciki. Salim yaga kamar ma kaya kyau tayi sa'ar datayi masa murmushi.
Hakan yayi masa dadi domin tabbas yasan ta gane shi.
Salim ne ko? Ko ba shi bane? Salim ya jefeta da murmushinsa na kwararren jarumi.
Nine mana duk garin nan wake da irin wannan fuskar idan ba ni ba. Ya danyi shiru lokaci guda kuma ya sanya hannayensa biyu cikin aljihunsa kamar yadda yasabayi ga al'ada.
Daga ina kike? Me kuma kikeyi anan ke kadai bakya jin sanyi ne?
Inajin sanyi mana ta mike tsaye da murmushi
tafiya ma zanyi tun dazu nake nan ina kallon yan fim ta danyi shiru sannan saita dube shi da murmushi tace.
Amma kallon ma ai ya kare tunda na ganka har mun gaisa. Adaidai lokacin sai wata mota kirar honda ta wuce ta kusa dasu hasken fitilar motar ya haskawa salim surar wannan budurwa mai sanye da kodaddiyar atamfa. Salim yaji zuciyarsa ta harba yawun bakinsa ya kafe sa'ar dayaga kyawunta ya bayyana afili. Tun ma bata sha diresin ba kenan fa. Yace azuciyarsa.
Yanzu daga nan ina zaki? Salim ya tambayeta. Budurwar ta haskake shi da fararen idanunta tace.
Uhm... Daga nan GAMA zani can nake da zama.
Gama? Kina nufin A Birget kike? Budurwar ta gyada kai.
Acan nake amma ban dade da zuwa garin nan ba yau kwanana tara da zuwa guri