MURMUSHIN ALKAWARI-18
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima A. Gangariya
.
Gama ? Kina nufin kice a birget kike? Budurwar ta gyada kai.
Acan nake amma ban dade da zuwa garin nan ba yau kwanana tara da zuwa agurin yayata nake.
Salim ya gyara tsayuwa idanunsa akan fuskarta azuciyarsa yana cewa lallai wannan kyakkyawa ita zata dace da fim din Gaibu tunda bakuwar fuska ce.
Daga wane gari kika zo?
Jama'are! Ta amsa masa kai tsaye sannan saita ja da baya.
To ni zan tafi sai mun sake haduwa.
Hakan kawai datayi shiya burge salim yakuma dauki kaunar yarinyar kai tsaye ya jefa cikin zcuiyarsa domin dan jan ajin datayi afakaice ya burge shi.
Sabanin sauran matan dake nace masa idan sun fara ganinsa ita wannan so take ta rabu dashi cikin gaggawa.
Idan baki damu ba ai sai mu rage miki hanya.
Budurwar ta rike baki cikin mamaki gamida wata yar zabura.
A'a wane ni salim ya rakani har gida ai ban isa ba. Hakan datace ya dada burge shi akaro na biyu.
Ai kinfi da haka... Ranki ya dade zo kawai mu tafi salim yace sannan sai kawai ya juya ya nufi motar. Budurwar tayi kamar bazata bishi ba saikuma taga salim ya juyo ya daga mata hannu.
Jikinta na rawa ta nufi motar sannan saitaji gabanta ya fadi ras! Sakamakon yan matan biyu data gani zaune abayan motar suna cin cingam ko waccensu tasha ado tana kamshin turare.
Shiga baya mu tafi. Salim yace da ita da murmushi sa'ar daya bude mata kofar. Budurwar ta shiga bayan motar a tsorace. Salim ya mayar da kofar ya rufe.
Koda salim yaja motar suka fara tafiya sai budurwar ta dubi yan matan biyu a tsorace tace.
Sannunku! Yan matan biyu suka marmatsa gefe guda lokaci guda sukayi mata kallon kare a karofi suka dauke kai gefe guda kana sai duk ruka rufe hancinsu da gefen gyalensu domin wai su nuna mata cewa jikinta fa wari yakeyi.
.
**** **** **** *** **** *** ****
.
Lokacin da suka karasa kofar gidansu budurwar sai salim ya fita daga cikin motar ya bude mata sannan suka koma gefe guda budurwar ta harde hannayenta akirjinta sannan ta dubi jarumi salim da fararen idanunta wadanda ke haskawa ko acikin duhun dare. Sannan saitace da shi A tausashe.
Nagode salim saikuma ko in mun sake haduwa. Salim ya girgiza kai.
Ina tsammanin gobe ma zamu sake haduwa akwai maganar danake son muyi dake.
Budurwar taji kamar a mafarki dan haryanu ta kasa imani da cewa wai yau itace tsaye tareda jarumin jarumai salim suna hira harma yana son sake haduwa da ita. Hakika wannan abin ta bada labarine idan ta koma garinsu.
Dan Allah da gaske kake zaka dawo goben? Ta tambaya baki bude. Salim ya gyada kai yace.
Zan dawo mana ko bakya sha'awar shirin fim? Budurwar taji wani dadi ya kamata cikin sauri ta gyada kai.
Ina sha'awa mana... Abin kenan fa dayasa nazo garin nan... Amma ina fargabar kamar bazanyi kyau da shirin fim ba. Salim ya dubeta ya fashe da tattausar dariya yace.
Kibari sai ranar da muka shirya ki sannan ki dubi kanki a madubi saiki yankewa kanki hukunci.
.
Washegari karfe goma sha daya na safe salim yazo daukar budurwar datace sunanta KALIMA.
Sa'ar data fito sai salim ya sami kansa yana mai numfashi dakyar ashe tafi kyau da rana nesa ba kusa ba. Salim ya dubi shudin leshin dake jikin kalima saiya ga kamar an rigar ta danyi mata yawa. Azuciyarsa yace me yiwuwa ma na yayarta ne ta aro. Duk da haka dai kayan sunyi mata kyau in banda takalmin ta da ya karkace gefe guda kamar tsohon kwale kwale.
Shiga mu tafi salim yace da ita cikin murmushi yana kallonta ta saman tabaransa.
Ina zamu? Kalima ta tambaya.
Gidana zamuje ki gani.... Ko tsorona kike?
Kalima ta girgiza kai tace haba dai tsoro saikace wani dodo? Ta bude gidan gaba na motar ta shiga sannan saita dubeshi da murmushi.
Jiya nafadawa yayata mun hadu dakai kai kawoni gida tace wai karya nake. Salim yayi murmushi batareda yadubeta ba sai ya sakawa motar giya suka tafi abinsu tattausan kidan sabuwar wakar fim din gaibu na tashi a hankali.
Kalima ta rufe idanunta gamida ajiyar zuciya hakika wannan mafarki ne ba gaskiya bane.
.
Lokacin da suka shiga kayataccen falon gidan kalima tayi mutuwar tsohuwa atsaye tana kallon duniyar da bata taba ganin irinta ba ko a mafarki.
Zauna mana. Salim yace da ita kalima ta dubi kujerun masu numfashi taga sai sheki sukeyi kamar ba'a taba zama akansu ba.
A.... Nan zan zauna? Kalima ta nuna daya daga cikin kujerun a tsorace. Salim ya gyada mata kai da murmushi. Kalima ta zauna ahankali kamar wacce ke kokarin zama abakin rijiya salim ya nufi kodar dakin shakatawar ta arewa ya bude kofar nan da nan sassanyar iska mai dauke da kamshin ya'yan itatuwa da furanni ta buso cikin falon. Kalima ta hangi cikin lambun baki bude.
Ina fatan kinji dadin zuwa. Salim yace sa'ar daya zauna kusa da ita. Adaidai lokacin ne to wata kofa ta bude sannan wani dogon saurayi fari dan gaya mai tarin suma duguzunzum kamar kayar bushiya ya shigo falon dauke da farantin kayan shaye shaye da tande tande ya ajiye akan dogon teburin mai shan kwai dake gabansu.
SALO dan Allah duk wanda yazo nemana bana nan. Salim yace da saurayin mai suna Salo wanda ya kasance shine....
Tags
# adabin hausa
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
adabin hausa
Category:
adabin hausa