Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

MURMUSHIN ALKAWARI-19
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya (Jikan Baba Sidi Mai Jaka)
.
Salim yace da saurayin mai suna Salo wanda ya kasance shine babban yaronsa wata sa'ar ma tare suka tafiya duk inda zashi.
An gama oga. Salo yace gami da dan rankwafawa kaikace ba sa'ansa bane. Salim ya dauki wayarsa ta tafi da gidanka ya mikawa salo yace. Ga wannan ma duk wanda ya kirani kace bana kusa. Salo ya karbi wayar ya fakaici kallon kyakkyawar fuskar Kalima. Yayi fito sannan ya fice daga falon yana tafiya yana dan tsalle kamar gurgu.
.
Bayan ficewar salo ne sai matasan biyu sukaci suka sha batareda sunyi wata kwakkarar magana ba.
Kina sha'awar yin harkar fim kuwa kalima?
Salim ya tambaya bayan sun gama cin abincin.
Kalima ta sunkuyar da kai kasa tace meyasa kayi min wannan tambayar.
Saboda ina ganin zakiyi bala'in dacewa da shirin fim.... Dole ne ma kyakkyawa kamar ta dace. Kalima tayi murmushi kanta a sunkuye
kaidai ka cika zuga. Salim ya girgiza kai ba zuga bace Kalima Allah fuskarki abar gani ce akan kyamara. Kalima ta sunkuyar dakai na tsawon lokaci can saita dago kai ta dubeshi tace.
Jiya munyi maganar da yayata kuma ta amince fuskar salim ta washe azuciyarsa yana addu'ar Allah yasa ta amince har ta aure shi nan gaba. Kin amince kenan? Kalima ta gyada kai da murmushi.
.
Wannan shine farkon faruwar komai. Tun daga wannan ranar salim yazama bawanta baya jin maganar kowa sai ta Kalima su Samira da sauran yan matan dake karkashin kamfanin fim dinsa duk Kalima tasa ya kore su. Ance a shekarar ne kalima tafara fitowa acikin fim din gaibu fim din dayayi tashen da ba'a taba samun wani fim dayayi koda rabinsa ba. Hakan nan ance salim shine cin kalima shine shanta shine cin yan gidansu jita jita na cewa hatta rubabben gidansu yayar kalima ma saida ya ruguje shi aka sake musu sabo aka dora musu bene. Asaman benen ne kalima ta tare salim ya hada mata kayan alatun duniya adakin sannan ya saya mata kayan sawa sama da kala dari da ashirin ance wai idan akullum kwanan duniya kalima zatasa kaya kala uku iri daban daban saita shekara hudu bata maimaita sa wasu kayan ba. Wannan shiyasa ta zama uwar jarumai mata yan shirin fim. Kulluma suna tare agindinta idan tasa kaya sau daya bata kara sawa saita zabi wata daga cikin yan matan dake karkashinta ta bata har layi yan matan keyi na karbar kayan.
Ranar Tara ga watan satumba shekarar milidiyya ta dubi biyu da hudu salim yayiwa jaruma kalima kyautar sabuwar mota kirar marsandi mai budadden sama. Wannan kyauta dayayi mata gaisuwa ce da rokon iri domin a iya tsawon zaman da sukayi da kalima ya tuntube ta da maganar aure sau arba'in da bakwai amma sai kalima ta shiritar da zancen. Wannan al'amari yafara damun zuciyar salim domin akullum kwanan duniya idan ya kalli kalima saiyaga kamar kara kyau takeyi gashi kuma aduk cikin kowane minti daya sunanta sai kara yaduwa yakeyi aduniyar yan kallon fina finan hausa. Farin jininta na dada karuwa. Salim na fargabar idan yayi wasa yanaji yana gani kwado zaiyi masa kafa ya koma ruwa don tabbas ko ba dade ko bajima wani mai karfin aljihun zai sako kai ya aure kalima yanaji yana gani. Wannan shiyasa salim tunani duk da irin kyautattukan hauka dayakeyi mata saiyaga kamar sunyi kadan dan haka awannan rana ta tara ga wata sai ya sayo mata wannan mota kirar marsandi sannan awashe garin ranar ne yake tambayarta maganar aurensu sai gashi bayan duk wahalhalun dayayi mata abaya ya yada sunanta aduniya ya mayar da ita mutum amma kalima harta sami ikon daga ido ta dube shi tace wai ba aurene agabanta ba.
Kai wannan rashin godiya dayawa yake.... Ai ko alkunya tayi min. Salim yace da kansa sa'ar daya dawo daga dogon tunanin.
Sannu ahankali saiya goge hawayen dake idanunsa awayance sannan ya dauke mutum mutumin karen ruwan ya ajiye agefe guda sannan ya dubi kalima wacce ke can inda yabaro zaune tana taunar cakuleti abinta.
Ni... Zan fiya... Yace da ita muryarsa na rawa zuciyarsa na kuna.
Gida zan mayar dake kokuwa anan zan barki harna dawo. Kalima ta kada masa idanu kafin tace.
Wankin kafa nake son ka kaini. Salim ya danyi shiru.
Kinsan dai sauri nakeyi kuma jirana akeyi... Ba ga motar ki nan ba ki tafi mana ke kadai. Kalima ta zunkuda kafada ta turo baki gaba tace.
Ni naki kai nake son ka kaini. Abinda salim baisani ba shine duk da irin jan ran da kalima keyi masa tana alfaharin duk inda zata aganta tareda fitaccen jarumi salim.... Kuma wani abin ban haushi tana masifar kishinsa kamar bala'i don ko nan da can bata son su rabu don kada ma wata ta sami shiga zuciyarsa.
Haba kalima ga motarki nan tafi aciki mana ki barni ni in tafi gurin shooting din nan.
Kalima ta hada rai ta dubeshi a fusace.
Kaga in bazaka kaini ba shikenan yar motar daka bani jiya har ka fara sa mata ido? To ni banyi niyyar fara fita yawo acikinta ba ta mike tsaye a fusace ta nufi kan kujerar da salim yake ta warci mutum mutumin karen ruwanta afusace ta juya zata fice daga dakin sai wayar salim tayi wani sassanyar sauti. Kalima ta tsaya cak atsakar dakin kamar an soka mata kibiya....