Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

MURMUSHIN ALKAWARI-25
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima A. Gangariya
.
Na gane ki..... Tayaya zan manta dake LARI.
.
BIYAR 5
Sidi mai jaka yayi wata doguwar hamma kamar zai yaga baki lokaci guda kuma ya dubi kwanon tubanin cikin takaici domin duk yawan tubanin nan ya hadiddiye shi bai fi dunkule biyar ba acikin kwanon.
Kai... Wallahi nafara Jin barci Nas. Sidi Mai Jaka yace lokaci guda kuma ya dada dame baki kamar kada ya dada yin wata hammar akaro na biyu.
Amma dai ko barci kake ji zaka karasa min ko baba Sidi? Na tambaye shi cikin kaduwa domin ba karamin aikin Sidi mai jaka bane ya ajiye labarin anan sai kuma mun sake haduwa idan kuwa yayi haka ba karamar gamawa dani yayi ba domin yanzu ne ma labarin ya faro dadi.
Kada ka damu Nas. Baba Sidi yace dani yana duban agogo
Sai yanzu ma sha biyu tayi bari nayi sauri mu gani ko na karasa maka kafin lokacin Sallar azuhur.
Yawwa baba Sidi nagode. Nace dashi. Sidi mai jaka ya dube ni kana ya tura busassun yan yatsun sa cikin farin gashin sa yace.
Kaga Nas sannu a hankali na hade maka zararrukan labarin nan guri guda ko? Na gyada kai bance komai ba.
Yawwa to bari kuma mu shafawa zararrukan labarin kala mu ga abin da zasu bamu. Ya danyi shiru kana saiya dubeni yace.
.
A daidai lokacin da duk wannan ke faruwa a gidan jarumi salim. Falmata na can dakinta kwance cikin zullumi domin ta fahimci cewa ita da sake fita waje da hasken rana sai baba ta gani dole ne ta fara halin Mujiya.
Al'amarin daya jefata cikin zullumi yafara ne tun adaren jiya bayan ta fito daga wanka zuciyar ta fari fat domin ga dukkan alamu mafarkin data dade ta nayi shekara da shekaru ya kusa zama gaskiya.
A tunanin falmata sa'ar data fara kokarin gabatar da kanta ga salim ta cikin waya ta dauka saita dade tana tarairayar sa kafin ma ya yasami damar kula ta. Amma ga mamakin ta sai taga ashe ma salim din arahar gani ne dashi kamar rana koda yake sa'ar data dawo dakin bayan sun rabu da salim ta sake duban kanta ajikin madubin saita yiwa kanta murmushi tace da kanta.
Banyi mamaki ba don na ruda shi.... Domin ni kaina idan na dubi kaina rudewa nake.
Falmata ta riga tasan tagama kame zuciyar salim abin kawai take bukata shine sake haduwa gobe ko shakka batayi rabuwar salim da wannan nacacciyar mai fuska kamar robar yazo karshe.
Da wannan kwarin gwiwar falmata ta fito daga wanka daure da tawul a kirjinta kamar yadda ta saba ga al'ada kafin ta nufi kan gado sai taga yadace ta saurari wakokin Fina finan salim.
Ko ta dada samun kwanciyar hankali tana rausaya ta nufi inda yar redion ta yake wacce ta zo da ita cikin akwatin kayan ta tare da kasa kasan wakokin fim din salim sa'ar data dauko rediyon ne wata zuciya ta ce da ita tun fa da kika zo garin nan baki saurari gidan rediyon su ba.
Wannan tunani shiyasa falmata kunna rediyon kunnawar ta keda wuya sai ta ji wakar wani fim din salim data taba gani na tashi a rediyon cikin sauri falmata ta dauki rediyon ta karo sauti sannan ta kwanta rigingine akan gadon rediyon a ruwan cikin ta idanunta a lumshe ta ci gaba da jin daddadan sautin da a zuciyar take tsammanin muryar babban masoyin ta salim ce tana nan cikin wannan hali kwatsam sai aka dakatar da wakar sannan ne to zazzakar muryar mai labaran ta bayyana inda ya kira shirin da sunan INDA RANKA.
Falmata tayi tsaki zata kashe rediyon sai ta ji mai labaran yafara karanto kanun labaran kamar haka.....
....... WATA MATA MARAR IMANI TA SOKE CIKIN MIJINTA DA WUKA YA SHEKA BARZAHU A YANZU HAKA JAMI'AN TSARO NA NAN SUNA NEMAN TA RUWA A JALLO DOMIN SUYI MATA TAMBAYOYI.... WAKILIN MU DA KE BARNO ZAI ZO MUKU DA CIKAKKEN LABARIN......
.
Falmata tayi jifa da rediyon zuwa tsakar dakin rediyon ta rabe biyu. Falmata ta lumshe idanu jikinta yafara yawa kamar mazari. Har garin Allah ya waye batayi barci ba.
Washe gari tun da sassafe ta aika a sayo mata jaridu. Ba karamar kaduwa tayi ba sa'ar da taga uku daga cikin jaridun shidan da aka kawo mata dauke suke da manya manyan hotunan ta a gefen hoton jaridar farko an rubuta kamar haka
...... SHIN KO KUN GA WANNAN?
IDAN KUN GANTA KUNA IYA SANAR DA OFISHIN JAMI'AN TSARO MAFI KUSA DAKU DOMIN ANA BUKATAR YI MATA TAMBAYOYI DA SUKE DA ALAKA DA KASHE MIJINTA CIKIN RASHIN IMANI.
A cikin sauran labarin ne falmata ta karanta hirar da yan sanda suka yi da mijinta saifullahi asibiti ashe ma saida ya kwana biyu a asibiti kafin ya mutu.
Wannan shi ya rusa duk wani mafarki na falmata yanzu kam tana riga tasan ko acikin otal din bata isa tayi yawo da rana ba domin hoton ta ya gama gari.
Dan haka a yanzu da falmata ke kwance akan gadon hawaye na zuba daga idanunta tasan cewa haduwa da salim a yanzu Abune Mai wahala domin bazata iya fita da rana ba ana farautar ta kamar mujiya. Don haka saita yanke shawarar ta buga masa waya ta sanar dashi cewa bazata sami damar zuwa ba saida magariba hannun ta na rawa ta daddanna lambobin salim sannan ta kara a kunne tana jiran salim ya dauki wayar sannan ne to ta tambayi kanta da kanta tambaya mai tsada. SHIN KWANA NAWA ZA'A DAUKA KAFIN SU KAMANI?
Ta riga tasan ko ba dade ko ba jima kudin dake jikinta zasu kare kuma jami'an tsaro zasu cimmata falmata ta fashe da kuka jikinta na rawa kamar mai zazzabi ba kamun ne yasa ta kuka ba tunanin rabuwa da salim ne ke damunta.
.
******** ******* ********* ******* ****** ******
.
KU DAKACI BABA SIDI MAI JAKA