MURMUSHIN ALKAWARI-21
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Falmata ta sauko daga kan gadon sa'ar da ta tabbatar da cewa sakonta na biyu ya tafi izuwa wayar Salim sannan saita nufi tagar dakin ta leka. Daga inda take tsaye yana iya hangen salim tsaye akusa da wasu jerin kyawawan fulawowi gajeru wata budurwa gwanar iya sa hoda da jan baki akusa dashi.
Shegiya nacacciya. Falmata tace tana murmushi. Kusan mintuna talatin kenan falmata na lekensu ta tagar dakin kuma ta lura a iya tsawon mintuna talatin din nan duk inda salim zai motsa wannan budurwa na biye dashi kamar inuwa. Da farko falmata bata gane budurwar ba sai daga baya data yi nazarin fuskar da kyau sai falmta ta fahimci budurwar amatsayin Kalima. Jarumar data sha ganinsu tare da salim acikin finafinan hausa da dama.
Falmata na nan gindin tagar dakin tana lekensu zuciyarta na tafasa da wutar kishi. Ayanzu kam duk duniya babu wacce ta tsana kamar kalima da zata mutu ma alokacin to da haka tafi so. Jaruman biyu na nan tsaye can sai falmata taga kalima ta dora hannunta a kafadar salim. Falmata ta zabura ajikin tagar dakin sa'ar dataji wani abu mai kamar kibiya ya soki zuciyarta.
Kadan ya rage ta fada waje ta cikin tagar dakin.
Bi ahankali yarinya falmata kada ki kashe kanki a banza abinda ko saninki ma baiyi ba. Wata zuciyar ce ke cewa da falmata haka.
Falmat tayi ajiyar zuciya sannan ta dubi fuskar wayar tafi da gidanka tayi tsaki wannan shegen sakon ma haryanzu yaki zuwa gare shi. Mintuna goma suka shude falmata na nan tsaye tana lekensu can saitaga wani farin saurayi mai gashi duguzunzum yazo ya tsaya agabansu salim. Sukayi dan kus kus da saurayin sannan sai taga salim ya kama hannun kalima sun nufi wani bangaren kayataccen gini dake fuskantar ginin da take ciki. Falmata ta lumshe idanunta ta daina ganinsu ji takeyi kama zuciyarta zata fasa kirjinta ta fito saboda masifar kishi.
Bayan wasu yan dakiku saita bude idanunta. Gurin babu kowa sai wani dan siririn lebura mai dan karamin kai kamar kwakwa ke sintiri agurin dauke da wani shudin bokiti na roba. Falmata ta kurawa inda ta tabbatar da cewa nan su salim suka shiga idanu. Kana sai ta juyo zuwa tsakar dakin ta nufi akwatin kayanta na musamman data tanada dan wannan muhimmiyar rana datake fatan yin ido da ido da babban masoyin zuciyarta Salim.
Sa'ar da falmata tagama sa kayan saita nufi madubi ta zauna sannan tafara dube dube da goge goge duk kuwa da cewa dazu saida tayi sama da sa'a guda tana kwalliya.
Falmata ta sake kallon kanta ajikin madubin ta juya hagu ta juya dama saitayi wa kanta murmushi domin tasan duk duniya babu namijin da zai ganta yawun bakinsa bai kafe ba. Cikin sanda tana tafiya kamar hawainiya saita bude dakin sannan ta wuce zuwa falo daga nan kuma tabi ta tsakanin jerin shuke shuken da ke kofar dakinta na musamman ta nufi inda su salim suka tsaya dazun. Sa'ar data isa gurin saita jingina bayanta adaidai da inda salim ya jingina bayansa lokacin daya tsaya agurin.
Adaidai lokacin to leburan nan mai sintiri ya dawo zai wuce ta gurin dauke da bokitin robarsa ahannu nan take sukayi ido biyu da falmata mutumin yaji numfashinsa ya tsaya cak. Domin ya dauka aljana ce ta bude masa idanu.
Shekarunsa ashirin yana aiki a otal daban daban amma tun dayake bai taba ganin mutum da kyawun aljanar dake gabansa ba.
Mu...tum.. Ko aljan? Ya tambayi falmata a tsorace. Falmata ta dubeshi a fusace tace.
Shashashan banza ka taba ganin aljan ba kofato? Bace min da gani bakinka ya isheni da wari. Dan siririn mutumin ya zuga aguje har sa'ar daya isa wajen karbar baki bai yarda cewa ba aljana yagani ba.
.
**** ***** ***** ***** ********
.
Salim ya share gumi daga kan kyakkyawar fuskarsa adaidai lokacin da dan gajeren daraktan mai kai kamar masaki ya dakatar da daukar shirin fim din. Kusan mintuna arba'in kenan suna daukar bangarorin fim din babu ko kakkautawa. Mutum takwas ne acikin dakin daga cikinsy akwai darakta, mai daukar hoton kyamara, sai me yiwa jarumai kwalliya dakuma mai kula da sa kayan jarumai sauran mutum hudu din duk jarumai ne. Duk wanda ka kalla acikin mutum takwas din sai gumi yake yana naso kamar waina saboda zafi sakamakon na'urar sanyaya dakin da aka kashe da gudun kada sautinta ya shiga cikin abin daukar maganar magana sannan kuma bugu da kari ga hasken fitilar mai mugun haske da feso zafi wacce take amfani wajen haskaka dakin da kuma fuskokin jaruma domin asami hoto mai inganci da haske ba duhu.
Kai nifa zafin nan ya ishe ni zanyi waje na dan sha iska. Salim yace yana goge zufa daga goshinsa.
Kana iya zuwa kasha iska kafin adan jima na tura akirawo ka. Dan gajeren daraktan ne ke magana batareda ya dubi salim ba idanunsa akan takardar dake dauke da labarin dim din da sukeyi.
Yawwa dan dagizge. Salim yace da dan gajeren cikin murmushi sannan ya nufi kofa aguje domin yasan inda ya tsaya jifansa zaiyi da duk abinda yafara zuwa hannunsa.
Zaka dawo ne ka sameni... Dan banza da tsayi kamar hanya. Daraktan yace adaidai lokacin ne Kalima ta mike tsaye zumbur zatabi bayan salim.
Ina kuma zak
Tags
# adabin hausa
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
adabin hausa
Category:
adabin hausa