Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

RALIYA

RALIYA-01
.
SHIMFIDA
.
KANO 2003
.
AL”AMARIN ya fara samo asali ne tun a
yammacin wata laraba” wacce tazo daidai da
mako biyun karshe” na wani zangon karatu a
jami'ar Bayero dake birnin kano” duk inda mutum
ya duba a cikin makarantar dalibai ne birjik” suna ta yawace-yawace kamar kwari” suna hada-hadar
ganawa da malamai domin an riga an saba duk
lokacin da jarrabawa ta karato” to ba sauran
sukuni malamai sun shiga aiki kenan” tun safe
har dare”
.
Wadansu dalibai kuma suna zazzaune suna ta
faman karanta littatafai da takardun kasidun
darasi” da yawa duk suna warwatse ne a cikin
ajujuwan makarantar” wadansu kuma wadanda
basu son yawan hayaniya da cikowar mutane”
suna can saman benaye suna yin nasu karatun”
duk wanda ya shigo cikin makarantar yasan
cewar yanzu ba lokacin wasa bane” musamman
kuma da aka ji an fara kishi kishin cewar a
wannan shekarar za'ayi tankade da rairaya mai
tsanani” shi yasa ba banza tasa dubban daliban
suka dukufa karatu ba” suna bitar darussan
gindin wata katuwar bishiya” wata kyakkyawar
budurwa ce ke xaune rike da nata littafin” ‘yar
kimanin shekaru ashirin da hudu a duniya bayan littafin dake a hannunta” a saman bishiyar da
take xaune a karkashinta” wasu tsuntsaye ne”
‘yan gida daya masu kama daya su kimanin
ashirin jikinsu yana ta sheki a cikin ganyayen
bishiyar” tun xaman wannan budurwa a wurin”
tsuntsayen keta faman rera mata wakoki iri-iri a
cikin wani yare mai wahalar ganewa”
To amma kuma ko sau daya budurwar bata daga
kai ta dubi wadannan tsuntsaye ba” kuma ga
alama aikin banxa suke yi” domin kuwa koke-
koken su da wakoki basu sami karbuwa a xuciyar budurwar ba” wasu daliban idan suka ga haka”
zasu yi tsammanin duk saboda tsabar karatu
wannan budurwar tayi xuru a xaune bata ji bata
gani” to amma kuma a xahiri ba haka abin yake
ba” domin kuwa tana dai dakon littafin ne a
hannunta amma idanunta bashi suke kallo ba”
Hankalinta ya tafi can wata duniya mai nisa” ita
kadai tasan abinda take nunani a ranta” sai kuma buwayi gagara misali” masanin sirrin boye
.
“RALIYA” Sunan ta da wannan sunan kowa yafi
saninta tun tana karama” to amma kuma a yanxu
data girma ta xama ‘yar jami'a akwai wadanda
ke kiranta da Diamond ba haka kawai yasa
wasu dalibai ke kiranta da wannan suna ba”
akwai hujjoji kwarara”
Da farko dai Allah ya halicci “RALIYA” da
tsabagen kyau fiye da duk yadda xa.a misalta ta
domin kuwa idan mutum ya hangota daga nesa”
zai sami kanshi yana kallon fara ce sol” to amma
kuma da zaran ta matso kusa” sai ta rikida ta
koma ita ba fara ba sannan kuma ba baka ba”
fuskarta ‘yar matsakaiciya ce doguwa” wacce
bata cike kauri ba shiyasa ko a wanne lokaci ko
barci take yi” tana nan da annurinta” “RALIYA” ta more lallausar fatar jiki kamar kwalba” sannan
kuma Idanunta ba manya-manya bane” kuma ba
kanana bane” sun dan shige ciki kadan” da xaran
ta kalli namiji dasu sai yaji duk gwiwarshi ta saki
babu kwari ko laifi tayi ma sauyinta sai dai yayi
bambami a bayan fage” amma ba dai ya tare ta
gaba da gaba ba”
.
Tsarki da godiya sun tabbata ga Ubangijin
Al'arshi gwanin tsara halittu” domin kuwa babu
wanda zaiga “RALIYA” ya dauka cewar
bahaushiya ce” saboda tafi kama da irin ‘yan
matan turawan yammacin duniya da ake gani a
hotuna da mujallu” bata cika kama da ‘yan matan
nahiyar bakaken fata ba” to amma kuma a zahiri
cikakkiyar bahaushiya ce ‘yar asalin jihar kano”
wacce ta taso a wani kauye kilomita hamsin daga birnin kano a karamar hukumar Garun Malam.
Daliban jami”ar sun sha rade-radi akan wannan
budurwa mai suna “RALIYA” domin kuwa wasu
samarin tuntuni sun tsinke da al”amarinta” sun
fara tunanin da wahala idan ba aljana ba ce ta
shigo cikin mutane tana karatu” domin kuwa
sanin kowa ne cewar ko da a jami”ar ‘yan matan aljanu “RALIYA” xata iya cinye gasar (miss campus) wato sarauniyar kyau ta jami.a”
Babu wani saurayi dake a jami”ar da zai ci karo
da Raliya koda a hanya baiji yana sonta ba”
ragowar “yan matan kuwa suna kinta ne kawai
saboda sun san cewar ta sami wani abu” wanda
koda miliyan dubu baza,a sayar masu ba a
duniya” shiyasa suke nuna mata kishi da kuma
kyashi” to amma kuma ya zasuyi tunda haka
Allah yaso ya ganta?
.
Ba dalibai kadai ke kaunar “Raliya ba” hatta
malaman makarantar su kansu labarinta sukeyi”
akwai lokuta da dama da “Raliya ke firgita
lakcarori da idanunta” domin kuwa idan malami
yana kan aikin bada darasi a cikin aji da xarar ya hada ido da ita a cikin dalibai duk sai yabi ya daburce”
wasu dalibai sun taba cewa” akwai wani malamin lissafi” wanda baya son shigowa darasi” idan babu “RALIYA” a cikin
ajinsu” wadansu kuma sun bada amanna da cewa
idan akwai “Raliya a aji” to malamai ba sa
yankewa kuma duk wanda ya shigo baya son fita”
.
TO amma kuma koda ace duk wannan zuki ta
malli ce” sanin kowane cewar “Raliya
tauraruwa ce a wannan makaranta” kuma duk
wani namiji dake kai da komo a makarantar tun
daga kan masu gadi har xuwa sama” su dukansu
suna mafarkin ace “RALIYA” ta xama masoyiyar
su idan so samu ne”
to sai dai kuma duk da wannan ni'ima da kuma
baiwa da Allah yayiwa wannan kyakkyawar
budurwa” sai kuma ya jarrabeta da kasancewa
cikin tsananin kuncin rayuwa da rashin galihu”
gashi kuma ita ba kula samari take yi ballantana ta dan rika yagar abin masarufi sau da yawa sai
wata kawarta da suka shaku mai suna SURI ta
taimaka mata sannan take samun sabulun da
xata wanke ‘yan tsummokaran ta shiyasa Raliya bata son shiga cikin mutane sosai domin kuwa
xamanta ita kadai musamman idan babu kawarta Suri ya fiye mata kwanciyar hankali” fiye da
komai a makaranta”
Sannan kuma wani karin abin al”ajabi ga lamarin
wannan budurwa shine” duk da samari da ‘yan
gayi masu xanxaro da motoci dake ta kawo mata
farmaki a kullum kwanan duniya domin ta xama masoyiyarsu” ita a nata bangaren tun tuni
zuciyarta tayi nisa da afkawa cikin xuxxurfan
kogin kaunar wani saurayi dake KAUYENSU mai suna RUFA'I
A xahiri tun RALIYA tana karama suke ta wannan
soyayya da Rufa'i dan kauye” gashi kuma yanxu
ta girma ta xama cikakkiyar ‘yar boko tana
karatun digiri” shi kuma Rufa'i tun tasowarsu ko
karatun firamare baiyi ba” to amma kuma ga
mamakin Raliya sai taji har yanxun tana kaunar
shi”
Da ace tuntuni ta sami karin masu goya mata
baya don tabar wannan karatu nata” da tuni
tabar makarantar ta koma kauyensu” domin ta
kosa taga ranar aurensu ita da Rufa'i to
amma kuma kakarta ce kadai ke goyon bayanta acire ta daga wannan jami.a ta koma gida haka
nan tayi aure” ita kuma kakartata ganin ta tsufa
ba.a cika daukar shawararta ba” kome ta fada
sai ace rudun tsufa ne shiyasa sai ta wuni tana
masifa” babu wanda zai saurareta”
Yawancin dalibai suna yiwa RALIYA mummunar
fahimta” domin kuwa wasu sun dauka cewar
tsabar fadin rai gareta” shiyasa bata cika son
yiwa mutane magana ba” sannan kuma bata da
wasu tarin kawaye sai SURI ita kadae” to amma
kuma RALIYA bata da fadin rai” yawanci idan aka
ga ta xauna ita kadai to tunanin rabin ranta
Rufa'i take yi” sau tari tunanin wannan saurayi
nata dan kauye yakan buwayi xuciyar Raliya
har ma ta kasa yin barci” ko a halin yanxu da
take a xaune a gindin wannan bishiya mai
tsuntsaye tunanin da takeyi kenan” tunanin
masoyinta Rufa'i
Duk lokacin da Raliya kyakkyawa xatayi irin
wannan xama ta tambayi kanya shin anya kuwa
Rufa'i xai yi xaman jiranta har xuwa lokacin da
xata gama wannan dogon karatu nata?” Hakika
wannan wani abu ne mai wahala wanda wanda
bashi da tabbas” domin tun shekaru shida da
suka wuce tun Raliya tana sakandire Rufa'i ya
matsa a gaggauta ayi aurensu domin kuwa ya
gaji da xaman jira” tasan halin samarin kauyensu
da son aure” yanxu haka watakila Rufa'i ya sami
wata budurwa wacce yake so ya aura ita kuma
ya hankura da ita” wannan tsammani da raliya
take yi a xuciyarta yana ci mata tuwo a kwarya”
.
Wannan tsammani da Raliya take yi xai iya
xama gaskiya” domin kuwa baxata taba mance
da maganganun da Rufa'i yasha fada mata ba
idan ta koma gida hutu
“wai ke Raliya wannan wane irin karatu ne haka
babu ranar gamawa?” ki duba fa ki gani yanxu
tsararrakinki su magajiya da talatu mai fura duk sun haifi ‘ya’ya biyar biyar” amma mu muna nan
har yanxu bama asan ranar da xa.ayi auren ba”
kuma shi wannan karatu da kikeyi” don baki sani ba ne” amma duk kauyen nan namu xagin
babanki ake yi” kowa yana tir da wannan karatu
da kikeyi na ‘yan birni………….
Duk lokacin da Rufa”i yayi mata irin wannan
maganar Raliya bata cewa komae” domin kuwa
tasan cewar shi baiyi karatu ba” bai san dadin
ilmi ba dole ne yaga kamar aikin banxa takeyi
tana batawa kanta lokaci”
to amma idan a yanxu data dawo jami'a ‘yan
kwanakin nan gab da xa.a fara jarrabawa” saita
fara wadansu irin munanan mafarki marasa dadin
gani” haka kawai da xarar Raliya ta kwanta barci
sai tayi mafarkin wai ga jama.a nan sun cika
kauyensu makil ana ta shagalin bikin auren
masoyinta Rufa'i da wata yarinyar daban”
hakika wadannan mafarkai” sun tayarwa da
Raliya hankali matuka. Sannan kuma duk
hankalinta ya koma kauyensu”
.
Don haka ne yasa ta yanke shawarar tattara
inata’inata ta koma gida” da xarar taje xata
tsaya kai da fata” baxata sake dawowa jami”a
ba” domin kuwa akwai sauran shekaru uku a
gabanta” kafin ta gama karatun” Raliya tana
fargabar xaiyi wahala a cikin shekaru ukun nan
idan har mafarkan da takeyi ba xasu xama
gaskiya ba” to ita kam” gara ace ta rasa karatun
digiri data rasa wannan masoyi nata Rufa”i ko
banxa dai xata karashe rayuwarta cikin farin ciki tare da masoyinta
.
Raliya taji an girgixa kafadarta da karfi” ta farka
daga dogon tunanin da take yi sannan ta daga
kanta taga kawarta suri” a tsaye a kanta ta dafe
kugu tana yi mata murmushi.