TSEGUMI-16
.
KARSHE
.
Dariya ta kamayi amma duk da haka idanunta 'kyar a kaina bata ko 'kiftasu
"Ya akai kasan ni na daukesu?"
"Taya bazan sani ba"
"Lallai dagaske kai 'din KARSHE ne"
"Wato da farko ban kawo a kaina ke din bace sai daga baya na ankare. Na sani lokacin kinzo d'aukar hotonki ne shine kika had'a dasu don 'badda tunanina."
"Kasan lokacin da na fara ankarewa da binciken da kakeyi game dani,zuciyata ta rayamin cewa kana da hotona a wajenka wanda ka d'aukeni a tattaunawarmu shine nazo na dauke"
"Bakyaso na buga hotonki a jaridar don kar Jaheed ko wani daga cikin mutanensa su gani ko?"
Girgiza kanta kawai tayi alamar eh
"Wai kuwa na tambayeki man"
"Fad'I tambayarka"
"Amma dai kina karanta littatafan hausa musamman irin na Nazir Adam Salih ko?"
"A'a me ka gani?"
"Kawai naga wasu abubuwa shigen rubutunsa tattare dake"
Hannuna na le'ka agogona 'karfe biyu daidai na dare (02:00a.m) waiyo Allah nace a raina har yanzu dai ban samu wata mafita ba. 'Dago kaina na sake yi ina kallonta har yanzu babu alamar sassauchi a tattare da ita. Ganin zata iya harbina kowanne lokaci idan taji shirun yayi yawa ne yasa na sake 'daukan wani layin.
"Farkon wajen da na fara gano kece ainashin matar Jaheed shine lokacinda na tsinci wasikar da kika aikowa Abubakar a gidansa. Wato sai yanzu na yarda da abinda wasu mutanen ke fada"
"Me mutanen ke cewa"
"Sunce kaji tsoron macen da ta had'a abubuwa biyu"
"Me da me?"
"Kyau da kuma hikima"
"Hmm taya akai ka tsinci wasikar?"
"A dakinsa daya rushe,a cikin wata tsohuwar dirowa"
"Yanzu ina wasikar take?"
"Tana gida"
Yanzu kam na tabbata duk abinda zan fada na fadesu,sai dai har yanzu ban shiryawa mutuwar ba hakanne tasa na 'dora da cewa
"Na 'kara tambayarki?"
"Ina jinka"
"Kin yarda yanzu cewa kece Hadiza Abdullahi Adamri,Fatim matar Jaheed Auwal ba Jamila ba?"
"A'a"
"Me yasa"
"Saboda har yanzu ban gamsu ba kawai dai ka ja dogon labarin mai rikitarwa wanda ba kowane zai gamsu dashi ba"
"Idan kina musu me zai hana muje kotu muji ko Alkalin zai 'ki gamsuwa"
"Na fadama babu wani kotu da zaka daya wuce nan,kuma yanzunnan wannan kotun zata yanke ma hukunci"
"Kamar yadda ta yankewa Abubakar?"
"Yauwa eh"
Akwai kuma wani abu da nake son na sani"
"Menene?"
"Saboda tsabar wayonki kika yaudari Jaheed Auwal ya aureki sannan kika samawa kanki kyakkyawan mazauni a zuciyarsa saboda tsabar kissa,amma me yasa kika kasa fahimatar cewa idan kina tare dashi zaki mallaki makudan kudade fiye da miliyan goman da kika cuceshi?"
"Kasan kuwa yadda mutum yake ji idan yana tare da mutumin da bayaso a matsayin abokin rayuwa?
Shiru kawai nayi na zuba mata ido,lokaci guda naji wani tunani yazo min wanda na tabbata zai kubutar dani!!
Shiru kawai nayi na zuba mata ido,lokaci guda naji wani tunani yazo min wanda na tabbata zai kubutar dani,ban jira ba kuwa na fara gabatar da shi kamar haka
"Kin san cewa a bincikena da nakeyi a kanki sai da na gano cewa ke........."Shiru nayi lokaci guda na kauda idona daga nata na 'kurama 'kofar dake bayanta ido. Idanuna na zazzaro cike da firgici kai kace wani dodo na gani wanda ke 'ko'karin kunno kai cikin 'dakin. Dagangan nayi hakan saboda burina ta kauda idonta daga gareni koda kuwa na 'yan sakanni ne,cikin sa'a kuwa ta fad'a tarkona. Juyawa tayi da niyyar duba abinda na gani a bayanta,cikin 'kiftawa kafin ta dawo da dubanta gareni na daka tsalle na fad'a ta tagar da ke kusa dani jikake timmm na fad'a waje. Ai kuwa ban jima da kaiwa 'kasa ta biyoni aguje tana harbi ba 'kak'kautawa. Da gaggawa na mike sannan na fake a jikin lungu na bangon dakin daga waje,bindigata na zaro nima na harba cikin dakin ba tare da sanin wajen da na harba ba.
Gaba 'daya dakinne ya kaure da duhu,ashe dai harbinda nayi ne na samu 'kwan lantarkin da ke ci a dakin. Karar takun sawunta naji alamar tana fitowa hakan tasa na arce a na kare,kwane-kwan
e na ringa yi a yayinda nake gudun daga wannan sashe zuwa wannan. Ganain haka yasa itama ta ringa aikomin da sakon harsashi kowanne bangare ba 'ka'k'kautawa. Banyi nisa ba cikin gudun da nakeyi naji saukar harsashi a kafata,hakan tasa na saki wani uban gunji mai 'karfi na fad'I kasa shame-shame a yayinda ita kuma ta tunkaro ni gadan-gadan.
Tsakaninta dani bai wuce taku hamsin ba najiyo wani sauti daga can nesa ana fadin "waye anan"da alama sautin ta microphone yake fitowa. Ai kuwa bata jira ba ta aika da sakon harbi daidai wajenda muka jiyo sautin muryar,faruwar hakan ke da wuya daga can bangarenma naji sun sako tasu wutar na dan wani lokaci kafin daga bisani a tsagaita. "Su waye kuma wadannan?Ko dai 'yan sanda ne?"Na tambayi kaina. Ni dai ina daga 'kasa kwance cikin jini sai naji dayan na cewa kofur ku 'karaso nan mun harbeshi,jira nake naji sun yanyameni amma ga mamakina sai naga dukansu sun nufi wajen gidan,sai a sannan na hango ta kwance a 'kasa sakamakon haskata da sukayi da fitulunsu masu tsananin haske.
"To amma me wannan mutumin ke harbi tun farko?"Naji dan sandan yace da 'yan uwannasa
"Gaskiya duk yadda akai yana da abokin karan battar"inji dayan
"Mu bincika ko zamu ganshi 'kila shima an kashe shi ko kuma ya buya a wani wajen"
"Gani nan anan"nace dasu da 'karfi a lokacinda naji sun fadi haka sannan na dora "kar ku harbeni,so take ta kasheni"
Shiru ne ya biyo baya,can sai dayansu yayi magana "waye kai,kuma me ke faruwa anan?"
"Sunana Haidar Ali ni dan jarida ne"
"Haidar kaine?"Aka ce dani,naso na shaida mai muryar amma na kasa
"Eh nine"
"Kana ina?"
"Gani nan anan"
"Fito fili mu ganka"
Dakyar cikin jan 'kafa na taso daga inda nake kwance,amma kafinnan sai da na boye bindigata a 'kuguna.
"Haidar me kakeyi anan?"
Daga kaina nayi na kalli mai tambayar tawa sai a sannan na ganeshi,abokinn
annawa ne da ya aramin finger print gadget
"Ta mutu ne?"Nace dashi
"Wacece?"
"Matar dake kwance a 'kasa"
"Ai ba mace bace Haidar ko baka ga gemu ba a fuskarsa?"
"Ba namiji bane macece badda bami ne wannan gemun da kake gani"nace dasu
Sai da suka matsa har kusa da ita sannan suka fisge gemun da ta saka sannan suka tabbatar da abinda na fadamusu.
"Taya akai kuka san muna nan?"
"Mun dawo daga operation ne sai muka ga mota a gefen titi ganin haka yasa muka tsaya bincikawa sai kuma muka jiyo 'karar bindiga".
<<<<<<<<<<
Washe gari dana farka sai na tsinci kaina kwance a gadon asibiti gefena nurse ce a zaune.
"An ciremin harsashin?"
"A'a amma yanzu za'a cire ka huta tukun"
Bayan kamar awa guda da ciremin harsashin budurwata A'isha da abokin aikina Ibrahim suka shigo dakin da aka kwantar ni
"Ya jikin naka?"Tace dani
"Da sauki"
"Yanzu abokina sai da binciko wannan lamarin?"
Murmushi kawai namar bance 'kala ba sai a sannan na tuna wani abu yau ne daidai ya cika kwanaki goma sha hudun da Jaheed ya yanke min. Ina cikin wannan tunani kuma sai ga maigidanmu Ibrahim Atiku ya shigo shima yana ta washe baki
Cikin isa da gadara na dubeshi nace "Atiku so nake ka samomin lambar da zata sadani da Jaheed yanzu" "Ba damuwa"yace dani sannan ya fita.
.
KARSHEN TSEGUMIN KENAN.
.
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH