Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

TSEGUMI 15

TSEGUMI-15
.
"Kamar yadda na fad'amiki ina da hujjoji 'kwarara wanda zasu gamsar da kowaye wanda zan kawo miki su 'daya bayan 'daya. Amma kafinnan zanso na gama baki labarin"shiru nayi ina kallonata ko zatace wani abu kafin naci gaba amma batace 'kala ba
"Yauwa bayan kun samu wadannan kudaden keda Abubakar da shekara guda shine kuka gina wannan gidan sha'katawar. Da farko tsarin zamantakewarki da Abubakar tana tafiya daidai kafin daga baya ya fara kawo tsoffin abokansa Club d'in wanda ke kuma tsoron kada su ganki su shaidaki shine kika yanke shawarar garga'darsa akan ya daina amma ya'ki har ma yake miki barazanar zai fasa 'kwan kowa yaji. Kin tsorata sosai da barazanar da ya miki,bayan kunyi aure shine kika shammaceshi kika taho dashi nan gidan gonar kika kasheshi. Na tabbata 'kwarangwal 'din da ke cikin akwatinnan nasa ne,ko ba haka bane?"
"Wannan shine kawai hujjar taka?"
"A'a,ai na fad'amiki labarin nada tsayi zan fad'amiki komai,a bincikena akan Abubakar an fad'amin cewa ma'aikatanki kin fadamusu mijinki ya mutu sanadiyyar nutsewa da jirginsu yayi kamar dai yadda kika fadamin a tattaunawarmu amma ban yarda ba,sai kuma na tuna lokacinda nake tambayarki abinda kike sha'awa kikace noma shima ban yarda ba amma da na had'u da Hajiya Jummai (mari'kiyarsu)sai take fadamin kina sha'awar noma da shuke-shuke. Lokacinda yaronki ya fadamin cewa kina da gidan gona kuma harda daki a ciki a wajenn gari na tabbatarwa da kaina cewa anan kika kashe Abubakar. Kinyi 'ko'kari wajen 'badda hankalin duk wani mutum da zaiyi 'ko'karin tona asirinki,babu shakka nima na yaba kaifin basirarki"
"Kana 'batamin lokaci fa,duk abubuwannan da ka fada babu wanda zai gamsar da wani cewa nice Hadiza Abdullahi Adamri ko Fatima Jaheed ko kasancewata 'yan biyu da har za'a gamsu cewa masauyen 'yar uwata nayi a madadina"
"Kar ki damu zan gamsar dake yanzu,ki saurareni kiji. A tattaunawarmu dake kin fadamin cewa asalin garin mahaifinki Busuku ne,naje har garin domin tabbatar da haka daga nan kuma sai na dawo kano au kafin na dawo kano sai da na biya ta kakori garinsu Abubakar inda na hadu da mahaifinsa yake fadamin irin munanan halayyansa sai naga sun sa'ba da yadda kika fadamin gameda shi. Da na dawo kano sai naje gidan yayansa wanda shima ya tabbatar min munanan 'dabi'unsa da yadda ya sama masa aiki a kamfanin takalma amma aka koreshi saboda halinsa. A can ma'aikatar ne na samu sunayen mutanen da ke kawo masa ziyara ciki harda ke (Hadiza Abdullahi Adamri)tun daga wannan lokacin na fara bincike a kanki har restaurant 'dinda kika had'u da Jaheed. A wata farar mota 'kirar BMW yazo ya daukeki,nasan zakiyi mamakin yadda akai nasan haka. Akwai wani mai shago da take da dabi'ar rubuta lambobin duk wata mota data birgeshi,agunsana samu lambar motar inda aka tabbatar min da cewa ta Jaheed ce
"Dakyau! Sai dai har yanzu banji wata hujja mai 'kwari ba"
"Daga nan kuma sai na binciki makarantar da kikayi,anan na fara gano cewa ku 'yan biyu ne sannan na samu adreshin Hajiya Jummai itace ta tabbatar da kamannin da kukayi da juna"
"Sai kwana kake har yanzu ka kasa fadin wani abu mai 'kwari"
"Nayi 'kokarin samun hoton Zainab,jiya kuma na sami naki a gidan Jaheed. Bayan na dawo don gano wani bambanci tsakaninku da juna ne na gano cewa akwai 'dison baki a kunnenki dan karami sabanin Zainab"
Dariya ta kamayi ba 'kak'kautawa sai dai bata kauda idonta a kaina ba
"Menene abin dariya kuma anan"
"Wallahi kai gara ne,yanzu wannan shine hujjar da ka rike?"
"Tsaya kiji"
"Ya isheka haka"
"Ina da wata hujjar"
"Wacce hujja kuma kake da ita?"
"Jiya lokacinda nake gidan Jaheed kafin na fita sai da na gwada tamabarin hoton hannun gawar (finger prints)sannan na dauki wasu kwalaben turare da kikayi amfani dasu suma na gwada amma basuyi daidai dana gawar ba. Da yammannan yau nazo Club dinki na dauki hoton naki yatsun ta hanyar yaudararki ki rikemin kwalba sanda nake nuna miki kamar 'kwaro ya fada a ido na. Nayi sa'a lokacin kanki a kulle yake baki gano plan 'dina ba har na samu kika rike kwalbar. A gida dana gwada sai naga sunyi matching dana sauran kwalaben da kuma agogon da na tsinta a motar da kike bibiyata. "
"Wannan tsinannen,mummunan mutuminnan sai naga bayansa wallahi sannan na kone gidan idan yaso naga ta inda har wani zai samu wasu kayaki da nayi amfani dasu"a fusace cike da 'karaji take fadin hakan,da alama ta fusata da yadda Jaheed din ya adana kayakinnata.
"Kinga dakata,duk wannan bazai kaiki ko ina ba. Me yasa don Allah zaki kashe 'yar uwarki jini 'daya.Saboda wata bukata taki anan duniya?"
"To menene amfaninta,yarinyar da bata da wani bambanci da karuwa,idan ka dauke iskanci da batawa mutane suna mai ta sani. Ko kadan bana takaicin abin da na mata"
"To ke fa? Kina ganin a hakan gara ke?"
"Kwarai kuwa"
"Naji amma waya baki damar daukan doka a hannunki alhalin ke ba hukuma ba?"
"Kaga kar kamin wa'azi"
"Naji amma me yasa zaki kasheta saboda kudi?Ina kike tunanin kudin zasu kaiki? Kin aikata 'barna da dama,ko kinsan adadin mutanen da kika hallaka sanadiyyar haka? Bari na 'kirga miki su. Da farko kin kashe mijinki Abubakar wannan ne ma ya tunamin da wani abu,babu shakka duk fadin 'kasarnan ke ce mace ta farko da ta taba aikata Polyandry"
"Menene Polyandry?"
"Ma'ana mace ta auri sama da miji daya a lokaci guda. Kin auri Jaheed kika sace kanki sannan kika zo kika auri Abubakar"
"Baka da hankali"
"Nagode"nace da ita sannan naci gaba "na biyu kin kashe Auwal sai kuma Laila da saurayinta sannan sai masu gadin ministry inda kika kashe daya sannan kika raunata daya sai kuma Hajiya Jummai. Hadiza wallahi ko kadan baki da imani yanzu duk tsufa da kyautatawa irin na wannan matar amma baki 'kyaleta ba,wacce irin zuciya ce dake. Sai kuma na bakwai ma'aikacinki da kika kad'e a mota"
"Ka gama 'kirgen?
"Eh"
"Ina fa ka gama,ai baka lissafa da kanka ba"
.
Sosai na tsorata ban san lokacin da fitsari ya d'isomin ba,bawai mutuwar nake tsoro ba sai dai yanayin yadda ta furta hakan ya nuna zan sha wahala.
"Hadiza"nace da ita
"Fad'I"
"Wai kuwa kin yarda da Allah?"
"Kar ka dameni da shirmen banza,duniyar nan da kake gani wayonka da 'karfinka ne zasu kwaceka"
'Kura mata ido nayi na 'yan wasu da'ki'kai sannan na dora da cewa "me yasa tun fari baki kashe ni ba kika zo kina kashe wa'dannan bayin Allah,ko kinsan cewa da farko kin kashe ni shikenan karshen tashin hankali kenan."
"Ji nayi a jikina cewa kasan ina biye da kai shi yasa ban yi yun'kurin afka maka ba saboda nasan zaka iya zama cikin shirin haka,kaga idan na gwada afka ma ban samu nasara ba shikenan asiri na ya tonu suma sauran da kaga na kashesu shammatarsu nayi saboda basu ta'ba kawowa a kansu zan kashe su ba. Lokaci d'aya ne nayi yun'kurin take ka da mota amma sakamakon gosulo da cinkoso na mutane tasa na gudu na bar motar"
"A'a ba wannan kad'ai bane,kin manta da tarkon da kika had'amin da dutsin guga (iron) lokacinda kika gayyaceni gidanki?"
"Kwarai kuwa sai dai wannan nima nasan ba lallai plan d'innawa yayi aiki ba"
"Yauwa wannan ne ma ya tunamin da wani abu da masu pidgin english ke cewa man miss road. Babu shakka mutane kamarki wad'anda suka kasa gano baiwar da Allah ya musu suke kasancewa cikin 'dayan biyu ko dai kiga sun dauwama cikin talauci ko kuma su azurta kansu ta mummunar hanya"
"Kana nufin ni yanzu ban gano baiwar da Allah yamin ba kenan?"
"Kwarai kuwa,irin yadda kika nuna rashin saninki a lokacinda na nuna miki 'bud'add'iyar wayar dutsin babu wanda zai gano da gangan kikayi. Da ace zaki shiga shirin film tabbas sai kin zamo best actress"
"Hmmm na sani amma dai bana dana sanin kasancewata haka"
Da alama duk wasu abubuwa da nake son fad'amata don siyan lokaci sun fara 'karemin,hakan tasa na zura mata ido ina kallonta a yayinda 'kwa'kwalwata tayi nisa a duniyar tunani
"Yauwa wai kuwa ya akayi kika san ina bincike a kanki?"
"Hmm baka san cewa ni 'yan biyu bace?"
"Fadamin yadda akai kika gano"
"Tun a tattaunawarmu na sha jinin jikina cewa akwai dalilin da ya kawoka wajena na sani jaridar da ka buga ko kuma ka bawa wani ya buga akan tattaunawarmu kayi hakane bawai don makaranta ba sai dan ka kawar da tunanina. Sai kuma mafarki da nayi kwana daya kafin a koreka a aiki,a mafarkin na ganka ka biyoni da gudu hannunka rike da wuka tsirara. Nayi 'kokarin guje maka amma na kasa duk inda nayi sai ka bini a haka har nazo kan wani tudu wanda 'kasansa ruwa ne da duwatsu na rasa yadda zanyi kai kuma gashi kayiyo kaina gadan-gadan ganin haka yasa na zabi fadawa kasan tudun. 'Karar da na saki ce ta farkar dani daga baccin da nake,sosai na tsorata da mafarkin kuma na tabbatarwa kaina cewa kana bincika ta hakan tasa washe gari na tafi ma'aikatarku anan na sami wani nake tambayarsa game da kai shine yake fad'amin ai an kore ka. Na tamabayi dalilin da yasa aka koreka sai ya cemin wai yaji cewa kana son bincikar wata mata a Khairat Night Club maigidanku ya hanaka amma ka 'ki har kaje gidan mutumin da gawar matar take. Shine ma ya bani adreshin gidanka"
Tunani wanda ya san adreshina a ma'aikatarmu ne ya fad'omin sai kuma na tuna da cewa ashe fa bamu da yawanda zamu kasa sanin juna
"Daga nan sai na wuce gidanka kai tsaye cikin sa'a sai na iske kana fitowa daga ciki d'auke da jaka a hannunka alamar zaka bar garin. Sai da na bika har tashar motar inda naga kahau motar Jigawa-hadejia ganin haka tasa na juyo sannan na watsar da lamarin domin ban kawo kaina saboda ni zaka can ba sai kuma daga baya mafarkin yayi ta zuwamin daga nan kuma na fara bibiyarka"
"Dakyau! Ina ma nima ina da irin wannan baiwar. Kafin ki kashe ni ina son zan roki wata alfarma a wajenki"
"Ina jinka"
"Don Allah ki dawo min da rediyota da dubu na d'aya da kika dauka a gidana saboda 'yan uwana su gada