Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

TSEGUMI 14

TSEGUMI-14
.
A gida ne dana dawo na gwada finger prints d'in kwalbar turaren da na bata ta ri'ke. Ganin sunyi matching da sauran,yasa raina yayi fari saboda na tabbata kwanannan zan binciko sirrin da idan har nayi nasara zan zamo 'daya daga cikin manya wa'danda ake ji dasu a duniyar bincike da jarida sai dai ina ji a jikina akwai abu guda daya kamata na gano kafin ha'ka ta ta cimma ruwa. Ban'daki na wuce kai tsaye na watsa ruwa bayan na fito ne na kimtsa kaina cikin wasu 'kananan kaya sannan na 'dauko 'yar 'karamar bindigar da na aro na cusata a tsakanin bel da wandon da na 'daura. Duk da kasancewar dare ne ko kad'an ban ji tsoron fita ba a daidai wannan lokacin saboda ina tunanin wannan shine mafi cancantar lokacin da ya kamata na isa wurin
Hanyar Zaria na nufa cikin matsanancin gudu,sai dai na kasa kwantar da hankalina sakamakon hangen bayana ta mirror da nake ko zan hangi mutumin da ke bibiyata na biye dani wannan karon ma,amma banga alamarsa ba. Tunanin zan iya wuce wajen ne sakamakon masifaffen gudun da nake ya sani rage tafiyar da nake har na isa wuri. A gefe na ajiye motar sannan na kutsa kaina gidan gonar cikin matsanancin duhun daren,tsoro ne ya ziyarci zuciyata. Tsintar kaina nayi ina waige-waigen bayana kar aljani ya fito min amma shiru,sai a sannan kuma na tuna da bindigar da ke ma'kale a 'kuguna. Wani 'karin kuzari naji yazomin cikin ta'kama da kwanciyar hanakali na durfafi ginin da ke tsakiyar gonar ta hanyar bin wata 'yar siririyar hanya. Da farko nayi niyyar kunna 'yar 'karamar tocilar da ke jikin wayata amma sakamakon bana so mutane su hangi hasken daga titi ya sani kauda wannan tunani har sai na isa ginin.
A kulle na iske 'kofar shiga ciki sai dai ban sha wahala ba wajen bud'e 'kofar domin tuni na 'kware wajen bud'e irin 'kofofin. Sai a sannan na kunna fitilar wayar ina haskaka kowanne sashe na d'akin, a gefen haguna na hangi wata makekiyar akwati ta katako ajiye a 'kasa. Idan ka 'dauke akwatin babu komai a d'akin sai taga dake 'daya sashen na 'dakin suna fuskantar juna da kofa. Akwatin na nufa da niyyar bud'eta amma sai na isketa a kulle da wani 'katon 'kwad'o,na jima kana nasha wahala kafin na samu damar bud'e kwad'on. Wani wari ne ya ziyarci hancina lokacinda na bud'e ,'kwarangal 'din mutum ne shimfid'e a ciki babu ta yadda za'ai ka gane ko wanene. Tun daga 'kafa na fara haska 'kwarangal d'in har zuwa kansa,a daidai goshinsa tsakanin kwarmin idanunsa biyu wani d'an rami ne wanda na tabbatar da cewa na harsashine da aka harbeshi dashi. Tunanin irin rama wula'kanci da cin mutuncin da ubangidana (Ibrahim Atiku) yamin ne ya sani mursmushi ganin yadda na binciko abinda yake tunanin ba mai yiwuwa bane. Tabbas yanzu kam na gama warware komai da 'kwararan hujjoji.
Kamar yadda na saba ji a jikina yawancin lokuta idan wani na kallona,haka yanzunma nake ji kamar da mutum a bayana. Waigowar da zanyi yayi dadidai da lokacinda aka kunna 'kwan lantarkin da ke 'dakin hakan ta sani sakin murfin akwatin da 'karfi ta koma ta rufe. Mutumin da ke bibiyata ne tsaye a bakin 'kofar hannunsa ri'ke da bindiga yayi shiga cikin ba'ka'ken kaya kamar dai yadda na ganshi lokacin da na fito a 'dakin Laila sai dai wannan karon babu ba'kin gilas a idanunsa.
.
Sosai na tsorata da yananyinsa musamman ganin yadda ya saita bindigar tasa 'kirjina saitin zuciya,ko kad'an babu alamar annuri ko fara'a a tattare dashi hakanne tasa na 'kara tabbatarwa da kaina ba lalle na sha ba. Bayan na mi'ke tsaye ne had'e da d'aga hannuwana sama alamar surrender sai naji tsoron da ke zuciyata ya kau,tsintar kaina nayi ina mai cewa "Hajiya Fatima Jaheed,babu shakka dama ina tsammaninki nasani kina biye dani da fitilar motarki a kashe,kin kusa makara domin tuni har na gama abinda ya kawoni ina shirin fita kika risken"
"Da ni kai ne,to tabbas da tuni na fara bankwana da duniya domin babu makawa yau d'innan sai na kashe ka"tace dani
"Na sani"nace da ita. 'Kwa'kwalwata ce ta fara aikin neman mafita kafin daga bisani na 'dora da cewa
"Kafin ki kashe ni zan so ki bani damar fadar wasu abubuwa"
Tsawon wasu da'ki'kai bata ce dani 'kala ba sai ma zubamin na mujiya da tayi idanunta basa ko 'kiftawa daga kaina daga bisani ta numfasa had'e da cewa "ina jinka,amma ka tabbatar ka ta'kaita domin tuni na fara 'kaguwa na kasheka"
"Kar ki damu,zaki cika burinki a kaina kafin gari ya waye"
"Ya isheka haka,ka fad'I abinda kake son fad'a ko kuma yanzunnan na aika ka lahira"
"To!"Nace da ita a lokacinda na jingina da jikin bango idanuna a 'kasa suna kallon wajenda na ajiye bindiga ta,sai dai na tabbata bani damar 'daukota sakamakon attacking d'ina da tayi. Babu shakka ya kamata na siyowa kaina lokaci don haka nema yasa na fara daga farko a lokacinda na d'ago kaina ina kallonta.
"Labarin na da tsayi,zanso kiyi min uzurin sauraro"
"Babu ruwana da tsayinsa,kasan yadda zakayi ka maidashi gajere"
"To! Shekaru uku da suka shud'e akwai wani abokina dake garin kaduna daya ta'ba gayyatata 'daurin auren kawunsa Alhaji Jaheed Auwal na tabbata kinsan abokinnawa. A wajen 'daurin auren naku ne na ganki anan naji sunanki Fatima. Bayan watanni uku kuma da aurennaku sai na samu labari a kafafen yad'a labaru cewa an sace ki sannan aka bu'kaci makuden kud'ad'e a wajen mijinnaki kimanin miliyan goma saboda tsabar yana sonki shi kuma ya biya kud'in amma duk da haka suka kasheki sai gawarki ya tsinta. Satinnai biyu da suka gabata kuma na kai ziyara Khairat Night Club to ananne kuma na ganki. Da farko kasa gano wajenda na sanki nayi sai daga baya bayan na 'karasa gida. Naso na gamsar da zuciyata cewa ba ke d'in bace saboda na san ba'a mutuwa a dawo amma na kasa"
Duk wad'annan surutan banzan da nake cikata dasu ina yinsu ne domin siyawa kaina lokaci,a zuciyata ina Allah-Allah na samu hanyar da zan kubuta. Shi yasa ma na raba hankalina gida biyu 'daya ina amfani dashi wajen surutan a yayinda 'dayan kuma ya shiga searching (binciken) mafita
"sai ku...."Shiru nayi a lokacin da naga ta baro jikin 'kofar sannan ta 'kara taku biyu zuwa sashena sannan ta tsaya
"Muje"
Babu shakka na lura da cewa tana son taji labarin ko dan ta san ta yadda akai na ganota ko dan tabi ta toshe duk wasu hanyoyi da nabi wajen ganota saboda gaba bayan ta kasheni
"Yauwa kamar yadda na fad'amiki zuciyata ce ke ingizani take rayamin cewa kece Fatima Jaheed wannan dalilin yasa na kira ubangidana nake fad'amar amma sai yake fad'amin cewa ba ke bace domin Fatima Jaheed an kasheta kuma har yanzu gawarki na gidansa a ajiye. Ko kad'an ban gamsu da abinda ya fad'amin ba,hakan tasa na yanke shawarar zuwa gidan Jaheed 'din ganin gawar. Yau kwana sha uku kenan da zuwana gidan ganin gawar sai dai nayi rashin sa'a Jaheed ya kamani a gidan. Na tsorata sosai lokacin hakan tasa na fad'amasa dalilin zuwana gidannasa. Maimakon ya dam'kani ga 'yan sanda ko kotu sai yace dani ya bani sati biyu (kwanaki goma sha hudu) na tabbatarwa duniya cewa kece matarsa ta asali. A lokacin ni kaina nasan hakan ba mai yiwuwa bane amma duk da haka ban karaya ba na fara bincike a kanki,ko zaki so kiji yadda na gudanar da binciken?"
"Ina jinka"
'Dakin nake 'karewa kallo,babu komai a cikinsa da zai taimakmin wajen kare kaina. Takaici ne ya ziyarci zuciyata ko kad'an ba mutuwar nake tsoro ba amma ace wai macece ta kasheni abin da ciwo gaskiya kuma na tabbata irin kisan wula'kancinnan zatamin mafi muni.
"Ci gaba mana"tace dani
"Da farko zan warware basajar da kikayi kece Hadiza Abdullahi Adamri wannan shine asalin sunanki ba Jamila ko Fatima ba sannan ke 'yan biyu ce. Sunan 'yar uwarki Zainab Abdullahi Adamri. Kuna matu'kar kama da juna sannan ku kad'ai iyayenku suka mallaka wad'anda suka mutu sanadiyyar hatsarin mota. Kun taso baku san kowa ba a danginku hakan tasa wata ma'kociyarku Hajiya Jummai taci gaba da ri'ke ku amma saboda rashin godiya irin taki kika gudu da 'yaruwaki kuka barta. Bayan kun gudu ne daga baya kowaccenku ta kama gabanta,inda ke kika had'u da Abubakar Garba kuka fara soyayya duk da kasancewarsa 'dan iska zauna gari banza. Daga baya kuma kika had'u da Jaheed Auwal a 'daya daga cikin restaurant 'dinda kikai aiki ya nuna yana sonki kika amince ba wai don ke kina sonsa ba sai don wani dalili naki da ke kad'ai kika barwa kanki sani. Daga baya kuma kika shirya wani plan 'dinki da Abubakar inda kika aiko masa daya je gidan karuwai ya duba Zainab ko tana nan,bayan ya dubo ya fad'amiki shine kika taho daga kaduna kika tafi da'ita wajensa (Abubakar) kuka 'boyeta sannan kika sace kanki a matsayin 'barayi ne suka saceki da had'in bakin Abubakar kuka aikawa Jaheed akan idan yana son a dawo masa dake sai ya biya miliyan goma shi kuma saboda tsantsar begenki da yake ya biya kud'in ku kuma sai kuka kashe Zainab 'yar uwarki kuka ajiye masa gawarta yazo ya dauka a tunaninsa ke ce sakamakon matsananciyar kamannin da kukayi. Ya kika ce gameda bincike na?"
"Kai Karshe ne a duniyar Jarida da bincike"tace dani
Murmushi ne ya su'buce min jin wannan sunan da ta kirani dashi
"Au wai murna kake don na kira ka da haka? To ka daina,wai ma tsaya kanajin akwai wani mutum mai hankali da zai gamsu da duk wad'annan 'kir'kirarrun labarin da ka tsara?"
"Alkali zai yarda da batuna domin kuwa ina da hujjoji"
"Wanne Alkalin?"
"Na kotu man"
"Yimin shiru ! Ai yanzu haka kana kotunda daga nan sai lahira"!!!!www