Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

TSEGUMI 13

TSEGUMI-13
.
"Kayi hakuri zan turo wani yanzu ya tayaka canja wata tayar"
"Babu komai,nagode"
"Sai da safe"
"Allah ya tashemu lafiya"nace daita. Har tayi nisa ta dawo "Dan Allah idan bazaka damuba mu had'u a gidana mana gobe"
"Ba damuwa Allah ya kaimu goben"bayan ta ban adreshin gidan ta juya taci gaba da tafiya. Ranar ban isa gida ba sai misalin 'karfe daya da rabi na dare (01:30am).
Washe gari a zuciyata na yanke shawarar zuwa kaduna gidan Jaheed Auwal bayan na biya ta gidan Jamila kamar yadda ta nemi naje. A hanya nake ta nazarin dalilin da zai sa tace nazo gidanta. 'Kwan'kwasa 'kofar gidan da ta kwatantamin nayi ina jiran a bud'e amma sai naji ance shigo. A ciki na isketa da 'kananan kaya na training tana faman press up. Bata ko kalleni ba taci gaba da abinta,nima ban kulata ba sai ma 'karewa 'dakin kallo da nake a lokacin da na rufe kofar. 'Katoto ne 'dakin wanda girmansa zai linka girman normal daki sau biyu,a can wani lungu irin 'katon table "dinnan ne na snooker a 'daya sashen kuma makekiyar rediyo ce a jingine da bango. Idan ka 'dauke wa'dannan abubuwan to babu komai a ciki. Bayan na gama 'karewa 'dakin kallo ne na dawo da hankalina gareta na fara 'kirga press up 'din da take,sai da na 'kirga arba'in sannan ta tashi.
"Dakyau! Kina 'ko'kari fa,kinyi ya kai arba'in"
"Saba'in nayi"tace dani tana haki
"Ya kake?"
"Lafiya lau"
"Kullum kike wannan press up d'in?"
"A'a ina yi sau biyu a sati,ka iya snooker?"Tace dani lokacinda ta nufi wajen snooker
"A'a ban iya ba,sai dai in zaki koyamin"
Nan fa ta fara tarwatsa balabalannan tana jefasu a rami,babu shakka ta 'kware a wannan fannin ma. Bayan ta gama jefasu ne ta duba agogon hannunta "La'ila" kaga har na kusan makara ma akan abinda nake so zamuyi dakai. "Biyoni"tace dani
"Ina so ne kaban shawara akan fara kasuwancin Jarida"tace dani a lokacinda muka shigo wani 'daki mai kama da dressing room. "Ina so ne nima na bud'e ma'aikata tawa ta jarida"
"Me da me kike son sani gameda harkar?"
Dutsin guga ta 'dauka ta jona a jikin socket sannan ta fara goge kayanta a kan wani benci mai fad'I lullu'be da yadi. "Komai ma"
Nan na fara mata bayanin ta yadda zata fara da irin aubuwan da zata tanada har ta gama goge rigar sannan ta 'dauko skirt zata goge
"Don Allah taimaka ka gogemin skirt 'dinnan man zan shiga wanka,idan na dawo maci gaba"
Kafin na bud'e bakina har ta fice daga 'dakin. Wuta ce ta jani a lokacinda na kama iron (dutsin guga) 'din sai a sannan na lura da wayar jikin iron 'din ta sille kamar wacce 'bera yaci. Ajiye dutsin da kayan nayi na koma gefe na tsaya. Bayan wasu 'yan mintina sai gata ta dawo
"'Kin gogemin kayi ko?"
"Tarko ne wannan"nace da ita
"Tarko !Kamar ya tarko me kake nufi?"Tace dani a lokacinda take 'ko'karin kama iron 'din
"Dakata"
"Me ya faru?"
A hankali na dauki iron 'din na nuna mata wajenda wayar ya sille
"Tab! Allah ya taimakeni,kai amma nagode da ka ceci rayuwata Haidar"
"Babu komai,mu ci gaba da tattaunawarmu kawai"
"Mu bari sai wani lokacin maci gaba wallahi gaba daya na tsorata"
"Kar ki damu lokacinki baiyi ba tukun,zan wuce ni saboda ina so zanje kaduna yau"
"To shikenan nagode"
"Amma akwai 'bera a nan ne?"
"Akwai su"
"Ya kamata ki nemi maganinsu"
"Zanyi 'ko'karin hakan".
A hanya nake ta tunanin yadda akai ta goge rigar ba tare da iron 'din ya ja ta ba a karo na farko. Na tabbata yadda na kama dutsin gugar haka kowanne irin mutum zai yi idan ya tashi guga. Ya kamata ace itama dutsen ya ja ta a karo na farko.
Misalin sha 'daya na isa garin,kai tsaye wajen abokina daya gayyaceni auren Jaheed na wuce. Bayan mun gaisa na 'dan huta nake tambayarsa gameda Jaheed
"Wai ya labarin kawunnannaka yana nan?"
"Yana nan,gobe ma zamuje 'kauye ta'aziyya nida shi"
"Ok! A goben kuma zaku dawo?"
"A'a sai mun kwana biyu gaskiya"
Naji da'din haka domin ina son le'kawa gidannasa don 'karasa wasu bincike sai dai na yanke shawarar komawa kano yau don gudanar da wani aiki a Khairat Night Club kafin goben na dawo. Ban kama hanyar dawowa gida ba sai misalin shida na yamma,na isa kano da daddare misalin karfe tara. Kai tsaye Khairat na wuce sai dai wannan karon shiru na iske wajen sa'banin sauran lokuta da zakaji ki'de-'kide na tashi da tulin mutanen na 'dud'd'ukuwa ciki,a hanakali na'karasa wajen masu gadin zuciyata na bugawa.
"Barkanku da yamma"
"Yauw barka dai"
"Meke faruwa anan ne?"
"Yau bama aiki,mun rufe sakamakon bige wani abokin aikinmu da akayi yau a mota"
"Wanene?"
"Ba zaka sanshi ba"
"Kwatantamin yanayinsa"
A irin yadda ya siffantamin shi na tabbatarwa kaina cewa saurayinda nasa ya kula da shiga da ficen Jamila ne aka kad'e.
"Amma taya har aka buge shi?"
"Yau ne da safe zai koma gida a kan hanya"
"To yazo tsallaka titi ne ko ya?"
"Ko 'daya a gefen titi ma yake tafiya"
"Ina Jamila?"
"Kana nufin Hajiya?"
"Eh"
"Ta koma gida"
Haka nima na koma gida zuciyata cike da takaici da tunani!!!
.
Ban kama hanyar kaduna ba sai da la'asar sakaliyarta,wannan karon na yanke shawarar tunkarar maigadin kai tsaye yayin shiga gidan saboda zanfi samun nutsuwa da kwanciyar hankali wajen gudanar da abinda nake son aiwatarwa a gidan kasancewar maigidan baya nan kamar yadda abokina ya fad'amin,yau ne zasuyi tafiya,na tabbata yanzu kam sun bar garin. Bayan sallar magriba na isa kofar gidan kai tsaye wajen maigadin na nufa na masa sallama sannan na fara tambayarsa.
"Ka gane ni kuwa baba?"
'Kuramin ido kawai yayi yana nazarin fuskata a 'ko'karinsa na gano wajenda ya sanni na 'yan wasu dakikai kana ya numfasa hade da cewa
"Eh to kamar dai na shaida ka,amma ban wayeka ba sosai"
"Ka tuna kwanakinnan da suka shu'de da daddare maigidanka ya saka ka fita dani zuwa 'kofar gida?"
"Ok ! Na ganoka kuma"
"Yauwa !Ya fadama abinda ya kawoni kuwa waccan lokacin?"
"A'a bai fadamin ba,me ya faru?"
"Wato abinda ya kawoni waccan lokacin shine wata mata na gani da sukai matu'kar kama da matarsa da aka kashe,tsantsar kamannin da sukayi ne ya sani yanke shawarar zuwa naga gawar matar tasa ko itace ta rayo shine ya kamani. kaji dalilin zuwana waccan lokacin"
"Dama ana mutuwa a dawo?"
"Eh to ance dai wai wasu suna yin fatalwa su dawo"
"Amma yanzun dai ina fata ba wajen gawar ka sake dawowa ba?"
"Wajenta nazo"
"Ba zai yoyu ba gaskiya"
"Saboda me?"Nace dashi a lokacinda na zaro dubu 'daya na dam'ka masa a hannun
"Saboda babu mukullin gidan a wajena"
"Kar ka damu zan san yadda zanyi na shiga"
"Amma ina fata bazaka jima ba?"
"Minti goma sha biyar ma ya isheni zan gama abinda zanyi na fito"
"To yanzu yadda za'ayi ka koma wani wajen ni kuma zan je na kashe fitulun gidan sai ka dawo"
"To ba damuwa"
Bayan naga ya kashe gaba d'aya fitulun gidannane na shigo,kai tsaye 'dakin da gawar take na nufa. Bayan na bud'e gilashin da take ciki na 'dauko camerar da na aro agun abokin aikina na fara daukarta a hoto. A hankali na maida na rufe gilas 'din kamar yadda yake da sannan na shige 'daya daga cikin sauran 'dakuna ukun dake gidan,ina shiga na tabbatar ba shine 'dakin da nake nema ba don haka na fito daga ciki na fad'a 'daya 'dakin. Babu shakka wannan shine 'dakin Fatima sakamakon tulin kayan matan dana gani a cikin wani wardrobe dana bude,sai kuma jibgin turararruka da na gani da sauran kayan shafe-shafe na mata akan dressing mirror. Wata 'yar 'karamar leda na zaro daga aljihuna na 'dure wasu daga cikin kwalaben turaren ta hanyar amfani da hankici sannan na zurasu cikin aljihuna na wando. Ci gaba nayi da bincika 'dakin anan naga wani photo album na bikinnasu cikin wata loka dake jikin dressing mirror 'din. Sai da na zabi hotonta da nake ganin shine yafi miin sannan zai taimakamin wajen gudanar da bincikena shima na cusashi a aljihun wandona na 'daya 'bangaren sannan na fito daga cikin gida.
"Baba kaga ban jima ba ko?"Nace da maigadin a lokacin da na fito daga cikin gidan
"Eh baka jima ba kam"
"Yauwa nagode ni zan koma"
"To madallah, Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen"
A gida ne na 'dauko hotuna biyun ina nazarinsu. Na jima ina kallonsu irin kallonnan da ake kira na 'kurilla amma ban ga wani bambanci ba tsakaninsu. Tabbas da ace zasu saka kaya iri 'daya to bazaka iya bambancesu da juna ba. Sake dawo da dubana nayi jikin hoton daga sama zuwa 'kasa a karo na ashirin sai a sannanne naga wani abu daya ja hankalina,akwai'dison ba'ki 'dan 'karami jikin kunnen hoton da na sato a jikin photo album 'din kusa da wajenda take ma'kala 'dan kunne sa'banin na Zainab. Finger prints gadget na 'dauko sannan na fara gwada sauran kayayyakin anan nayi compairing 'dinsu dana agogon da na gani a motar da ke bibiyata. Nayi matu'kar mamaki ganin yadda sukayi matching.
Washe gari da safe na isa Khairat a ciki na iske matar da tamin iso kwanaki nake tambayarta Jamila
"Hajiya bata nan"
"Amma zata zo office yau?"
"Ban sani ba gaskiya,har yanzu tana jimamin mutuwar abokin aikinmu ne"
"Zan le'ko zuwa anjima da daddare ko zata zo"
"To"
A hanya ina dawowa gida na biya ta wani shago da ake sai da turare na sayi 'kwalba daya 'karami na sashi a aljihu na wuce gida huce gajiya kafin daren yayi.
Tun da misalin 'karfe tara na dare na isa can amma dana tamabayi masu gadin ko sun ga shigowarta suka ce bata zo ba. Ciki na wuce sannan na samu waje na zauna ina jiran 'karasowarta. Har sha 'daya da rabi ta gota amma bata 'karaso ba hakan tasa na tashi zuwa wajen matar naji ko Hajiyan zata zo yau
"Banajin zata zo gaskiya,amma dai ka jirata"
"Ba matsala na dawo gobe kawai dama jaje nazo yi mata"sannan na fito da niyyar fita sai kuma na hangota tana shigowa.
"Hajiya sannu da shigowa"
"Yauwa Haidar"
"Ya aka ji da hakuri kuma?"
"Alhmdulillah"
"Ai na jima ina jiranki na jajanta miki bakya nan"
"Eh wallahi,ina gida kasan na matu'kar ji takaicin abun"
"Sai ha'kuri"
"Naso ace masu gadin sun rike lambar motar wallahi da sai mun shiga kotu dashi"
"Ba mamaki direban 'danye ne ko kuma........Wai
yo Allah idona"na 'kwala da 'karfi ina murstika ido
"Me ya faru?"
"Ri'kemin"na mi'ka mata 'walbar turaren da na siyo sannan na fara goge idon nawa da hankici
"'Kwaro ne ya fadama?"
"Inajin 'kwaro ne"
"Ya fita"
"Eh ya fita"
"To Allah ya kiyaye bari na 'karasa office nagode"tace dani sannan ta mi'komin kwalbar turaren. Sai da na rufe hannuna da hankicin sannan na 'kar'bi kwalbar