TSEGUMI-12
.
Tunanin bincika gidajen karuwai dake garin (kano) ne ya zomin ko zan dace na sameta. Ni kaina nasan ban isa na gama gewaye gidajen karuwan da ke fadin garin ba ko da tsawon shekara zan shafe inayi amma duk da haka ban karaya ba na fara bi daga nan zuwa can amma ban dace ba. Na zaga gidajen karuwai a 'kalla sama da 'dari biyu sai a wanine na samu wata nake tambayarta.
"Kinga tambayarki kawai zanyi sannan na biyaki ba wani abu ne ya kawo ni ba"
"Tambaya?"
"Eh"
"To ina jinka"
"Wata yarinya Zainab Abdullahi Adamri nake tambaya ko kin santa?"
"Zainab ta bar nan"
"Kika ce me?"
"Nace ta bar nan"
"Kin santa?"
"Eh sosai ma"
"Ya kuke da ita?"
"'Kawata ce"
"Kenan bazaki rasa hotonta ba ko?"
"A'a amma dai mun ta'ba dauka sai dai har yanzu bamu karbo ba agun mai hoton"
"Ina wajen hoton?"
"Anan unguwar ne"
"Ya sunan wajen"
"Al'ameen professional photos"
"Amma kinsan inda ta koma"
"A'a"
"Kika ce 'kawarki ce?"
"Eh,lokacinda ta tafi bana nan da na dawo ban ganta ba nake tambayar 'kawayena suka cemin ai wata tazo ta tafi da ita. Sun ce suna matu'kar kama da juna 'kila ko 'yar uwarta ce"
"Tun yaushe ne hakan ya faru?"
"Shekaru uku kenan yanzu"
Bayan na sallameta na koma mota. Na 'dan 'dauki lokaci ina zazzagawa kafin daga bisani naga shagon mai hoton amma a rufe. Washe gari da safe na koma shagon wannan karon a bud'e na samehi,kutsa kaina nayi ciki
"Malam barka da aiki"nace da saurayin da na iske a shagon
"Yauwa,sannu da zuwa"
"Akwai wata yarinya da ta'ba daukar hoto anan"
"Wacce yarinya fa?"
"Sunanta Zainab Abdullahi Adamri"
"Zainab ? Kai na mantata gaskiya"
"Karuwa ce anan kusa da ku take ta jima da 'daukan hoton"
"Ok ! Na tuna kuma"
"Hotunan da ka 'dauketa nake so zan siya"
"Hhhh ai ta had'u yarinyar bari na 'dubosu"yace dani yana dariya a lokacinda ya shiga wani daki. Bayan wasu 'yan dakikai ya dawo rike da hotunan a hannu
"Yauwa gasu ko,sai ka zaba"
Basu da wani bambanci da Fatima Jaheed haka Jamila ma. Yanzu kam na fara warware abubuwan amma matsalar wajenda zan had'u da Zainab 'din. Ko dai Jamilar ce ta canja sunanta daga Zainab zuwa jamila? Amma kuma banajin Jamilar itace Zainab saboda bambancin halinsu halayenta yafi kama dana Hadiza kamar yadda bincikena ya nuna min. Idan kuma Jamilar itace Zainab a ina ta samu ku'din da zata gina kanta haka sai sannan kuma na tuna ashe fa tace dukiyar mijinta ta gada. Shi kuma a ina ya tara wannan dukiyar? Shima ai bincikena sun nuna matsiyaci ne. Dole shima na zurafafa bincikena a kansa,wannan dalilin ne ya sani ci gaba da ziyartar sauran mutanen da ke jikin takardar da na samo a kamfanin takalma.
"Abubakar abokina ne sai dai mun daina ganin juna tun shekaru uku da suka wuce"wani abokinsa dana kaiwa ziyara yace dani wanda shima sunansa na jikin takardar
"To lokacin a ina yake da zama?"
"A gyadi-gyadi yake"
"Amma me yasa kuka daina ganin juna?"
"Haka kawai na daina ganinsa"
"Nagode"nace dashi sannan na nufi gyadi-gyadi har gidan da ya kwatantamin amma sai na iskeshi a rushe. Wajen wani mai shago na 'karasa kusa da gidan nake tambayarsa
"Malam yaushe ginin nan ya rushe?"
"Yau shekara uku kenan"
"Nagode"nace dashi sannan na koma mota. Har na tayar da ita ina shirin tafiya na tuno da wani abu. Rusasshen ginin na nufa,anan na sunkuya ina binciken abubuwa da ni kaina ban san me nake nema ba sai kace mahaukaci. Wata tsohuwar dirowa na gani bayan na jawo ta kusa dani ne na fara binciken abubuwan da ke ciki. A ciki ne naga wata 'yar 'karamar takarda da rubutu a jikinta kamar haka
Zuwa ga Abubakar
Na rubuto na sanar dakai cewa abubuwa sun daidaita kuma zan so na sani ko ka bincika wannan abun kamar yadda na fadama idan bakayi ba don Allah kayi 'kokari kayi kaga lokaci na 'kuratowa kuma abin nada muhimmanci. Ashirin ga wannan watan zan taho saboda zai fita kasuwanci na 'yan wasu kwanaki. Amma ba zanzo wajenka ba saboda bana so mutane su ganeni mu had'u a can wajen gari hanyar kazaure gaba da bandirawo city. Sai anjima
Daga masoyiyarka
Hadiza.
PLS!!! Kar ka kuskura kace zaka kirani ko kace zaka zo ko ka rubutomin wasika. Ka bari ni zan shirya komai.!!!!
.
Nannad'e takardar nayi na totsata a gaban aljihun rigata sannan naci gaba da bincika sauran takarcen dake rusashshen gidan amma ban samu wani abu mai muhimmanci ba. Hakan ta sani dawowa cikin mota sannan na nufi gida da niyyar hutawa kafin dare yayi na le'ka Khairat Night Club.
Misalin takwas daidai na dare (08:00pm) na kama hanyar Khairat,nesa dani daga baya na hango wasu motoci guda biyu na taxi na biye dani a raina ina tunanin yaran Jaheed ne dake biye dani,wannan karon ban damu da duba lambar motocin ba domin nasan su 'dinma na haya ne. Fakin 'din motar nayi a wajen da aka tanada saboda ajiye motoci a club 'din sannan na shige ciki. Wannan saurayin ne ya sake tarbata wannan karonma.
"Sannu da dawowa yallabai"yace dani
"Yauwa"
"Wannan karon me kake da bukata ko giyar?"
"A'a Maltina nake so"bayan ya kawomin ya juya da niyyar komawa na sake kiransa
"Don Allah inaso zan maka wasu tambayoyi idan bazaka damu ba"
"Ba matsala amma sai dai zuwa anjima misalin sha biyu (12:00pm) kafinnan aiki yayi sau'ki"
"Ba damuwa ina nan har zuwa lokacin"nace dashi. Tashi nayi ina 'dan zazzagawa har wajen matar da min iso wajen Jamila kwanaki.
"Sannunki da aiki"
"Waye kai?"Tace dani a fusace
"Nine 'dan jaridannan na kwanaki da yazo wajen Hajiya!baki ganeni ba?"
"Me kuma kake so yanzu agunta?"Wannan karonma babu annuri a fuskarta
"Dama tambayarta nake so nayi ko taga Jaridar tattaunawar da mukayi"
"Bata nan"
Ganin ban samu fuska ba a wajenta ya sa ni fita daga sashennata,a hanya ne na kusa kici'bis da ita
"Kaine Haidar Ali dan jaridar nan ko?"Tace dani
"Eh nine Hajiya ya aiki?"
"Da godiya,naga jaridar da ka buga"tace dani tana murmusawa cikin wani salo mai kashe zuciya.
"Yauwa dafatan kinji dadinsa?"
"Sosai ma kuwa"
"Yauwa haka nake so naji dama"nace da ita a lokacinda nake 'kare mata kallo daga sama zuwa 'kasa.
"Bari na wuce office"tace dani sannan ta shige.
Sha 'daya da hamsin (11:50pm) matashin ya dawo ya sameni
"Wato akwai abubuwanda nake so na tambayeka"
"Me dame kake son ka sani?"
"Da farko ina so na san wanene Abubakar Garba?"
"Abubakar shine mijin Hajiya amma ya rasu"
"Tun yaushe ya rasu?"
"Ya 'dan jima gaskiya,tun farko-farkon bud'e wannan gidan"
"Amma kasan ta yadda akai ya mutu?"
"Eh to Hajiya tace mana dai wai jirginsu ne ya nutse a ruwa a hanyarsa ta dawowa daga garinsu"
"Amma ya kake ganin sha'kuwarsu da Hajiya kafin ya rasu,sun ta'ba samun sa'bani?"
"Eh to ba sosai ba,amma dai suna zaune lafiya"
"A irin sa'banin da suke samu ko ka ta'bajin wata kalma da suke furtawa?"
"A'a"
"Ka tuna dai"
shiru yayi na 'yan wasu da'ki'kai da alama tunanin yake sannan ya 'dago kansa
"Eh to akwai lokacin da naji Hajiya tana cemasa wai yana kawo tsoffin abokansa. Shi kuma sai yake ce mata shine fa silar samun komai nasu idan ta matsa mar zai fasa 'kwai kowa yaji"
"Ka tabbata kaji haka da kunnenka?"
"Eh na tabbata"
"To amma wanne 'kwai zai fasa?"
"Ban sani ba"
"To me Hajiyan tace daya fad'I hakan?"
"Shiru kawai tayi batace 'kala ba"
"Tun daga wannan ranar daya fadamata haka sun sake samun sa'bani?"
"Basu sake ba,sai dai ko a gida ban sani ba"
"Bayan wannan gidan sha'katawar akwai wani kasuwanci da Hajiyar ke yi?"
"A'a sai dai tana da gidan gona a hanyar Zaria"
"Wajen ina ne?"
"Da ka kama hanyar a bangaren hannunka na hagu zaka ganshi a ciki da wani gida anan Hajiya take hutawa"
Sai a sannan na tuna tattaunawarmu da ita tace tana sha'awar noma. "Yanzu kasan me zakamin?"Nace dashi
"A'a"
"So nake ka sa mata ido ka lura da duk wasu shiga da ficenta,sai kana fadamin ni kuma zan biya ka kullum idan ka samo min wani bayani kaji"
"Ba matsala"
<<<<<
Tayar motata na tarar a sace,sai da na matsa daf da ita na hangi wata zungureriyar 'kusa cake a gefen tayar rabinta ya nutse a ciki. A fusace na juyo na sami masu gadin ina fad'a akan sakacinsu da har zasu bari wani ya shigo ya huda min taya suna gani amma ga mamakina ko ci kanka basu ce ba sai ma zubamin ido da sukayi hakan kuwa ba 'karamin fusatani yayi ba. Ci gaba nayi da yi musu fad'a a fusace sai kace ni na 'daukesu aiki.
"Haidar"naji an kirani a bayana. Juyawar da zanyi muka had'a ido Hajiya ce
"Me ke faruwa ne?"
"Hava ! Wadannan sokayen masu gadin naki ne man,suna gani wani yazo ya fasa min taya zo fa ki ga yadda aka mata"
"Kayi hakuri don Allah,amma nasan ba laifinsu bane sai dai ko a hanya ka taka 'kusar baka sani ba. Amma na tabbata babu wanda zai shigo nan suna gani"
Ko kad'an ban saurari abinda take fad'a ba gaba d'aya hankalina yana kan kamshin turaren da ke fitowa daga jikinta!!!!