Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

RALIYA 02

RALIYA-02
.
RALIYA wanne irin tunani ke kuwa kikeyi haka?"
Ina ta faman yi maki magana amma koki dago
kai ki dubeni"
raliya tayi ajiyar xuciya" sannan ta rufe littafin
da ta rike a hannunta" kwata kwata ta mance a
gindin bishiya take xaune"
"ke ma kin san tunanin da nakeyi suri"
Raliya tace da ita a sanyaye sannan ta sake
kurawa wata shadda idanu wacce ta sauko daga
saman bishiyar ta sauka akan wani tsohon famfo
dake kusa da inda suke"
Suri ta xauna a kusa da kawarta Raliya" sannan
tace da ita cikin damuwa"
"Raliya waeke da gaske kike yi barin makarantar
nan xakiyi saboda kawai ki koma gida ki ga
masoyinki"? Ki tuna fa yanxu lokacin jarrabawa
ne" kowa ya mayar da hankali wajen karatu"
gaskiya nidai ban baki goyon bayan ace kin bar
makaranta a irin wannan lokaci ba
RALIYA" ta dubi kawarta suri cikin nutsuwa"
dogowar budurwa mai yawan kiriniya da kuma
rashin nutsuwa a wajen magana" wankan
tarwada mai yawan barin gashin kanta a waje"
Raliya tace da ita"
"Ba wai naki in bi shawararki bace suri" nasan
cewar abinda kika fadi mani gaskiya ne" to amma
kuwa ya xame mani dole in hankura da karatun
nan tunda dai ko da ace na tsaya makaranta
yawan tunanin Rufa"i baxae taba barina inyi
karatu ba" ballantana har inci jarrabawa"
Dalili na biyu kuwa shine" ke kinfi kowa sanin
halin da nake ciki a makarantar nan suri" ba wani abu nake xuwa dashi ba" da xan iya rike kaina a
makarantaar nan" dole ke nake dorawa"
dawainiya dani" kina tsammanin xan
iya jurewa inta xama a haka kullum a wahalce
suri?" gaskiya baxan iya ba"
Suri tayi farat tace da ita"
"To ai kece Raliya wallahi wani abin ma laifinki
ne" na sha nuna maki hanyar da nake bi ina
samun kudi" amma ke sai kice wai ba halinki
bane" to muda mukeyi halin mu ne Raliya?" ba
dole ke sa mutum yayi wani abin ba?" ni inda ace nice nake da wannan kyan naki to da na gama
hayewa tsanin arxiki a duniya"
wannan kyan da Allah ya baki Raliya na samun
hutu ne amma ke baki san darajar shi ba" kin
tsaya kina wahalar da kanki a banxa" ni bansan
lokacin da xaki goge ki xama cikakkiyar 'yar birni ba Raliya"
Raliya ta dubi suri cikin damuwa tace"
"Na sha baki amsar wannan maganar suri" ni ban
dauki duniya a bakin komae ba" nasan cewar
maganr kyau" hakika ni kyakkyawa ce kuma na
godewa Allah daya yi mani wannan baiwa" Amma
a gaskiya ni baxan taba ampani da wannan dama
in bata rayuwata ina biyewa maxa 'yan iska dake
bata 'yan mata ba" don in tara kudi a duniya" ni
nasan cewar komae nufin Allah ne" da arxiki da
talauci duk nufi ne na Allah"
Idan Allah ya nufa xan sami wani abu a duniya"
to ba saina bata rayuwata zan kae irin wannan
matsayi ba" domin ban isa in ba kaina wani abu
da ubangiji bai nufeni da samu ba" Na gwammace
dai in hakura in koma kauyenmu in auri
masoyina Rufa"i dake can yana xaman jirana"
Suri tayi tsaki ta kawar da kanta tace"
"Ai ke dama haka kike Raliya. Sai kije kiyi tayi" in
banda lalacewa tayaya xa.a ce kinyi karatunki"
kin xauna kin goge a birni kowa yana sha.awarki"
amma ace kin koma kauye kin auri wani wanda
bai yi karatu ba?" haba Raliya gaskiya ki rabu da
wannan Rufa"in in dai ba sammu yayi maki ba" ki
tsaya ana birni ki more rayuwarki" ga samari
masu kudi da motoci wayayyu suna binki kina
sharesu kullum"
ke ba matar kauyawa bace malama" xaki fi macin da miloniya dan birni" ba wani dan kauye ba wai shi Rufa"i. Rufa"in me dan Allah?"
.
Raliya tace"
"Nidai ina son abina hakan nan! Gaskiya suri ki
daina kushe min saurayi meye haka?" wannan ma
ai rainin arxiki ne" ki daina kushe mani shi
gaskiya bana so"
suri tayi murmushi sannan ta dafa kafadar Raliya
tace"
"Lallai Raliya kinyi nisa" ai an har fushi kikayi har
kina wani kakkareshi" sannu malamar soyayya"
sai ki gafarceni ban san cewar ba.a kushe maki
rabin rai ba"
Raliya ta saki ranta da taga suri tayi fushi tace
da ita"
"Ba haka bane suri" kiyi hankuri" abin da yasa
kikaga na nace akan kaunarsa" alkawari ne mai
karfi tsakanina dashi" tun muna yara" kuma kinga
dai bai kamata ace na karya alkawari ba suri"
shiyasa kikaga na mace akan kaunarsa" wannan
ita ce hujjata"
Suri tace.
"To ae shinke nan" tunda kina ganin haka yafi
dacewa da rayuwarki baxan hanaki ba Raliya" mu
dai muna nan cikin birni xamu xauna a cikin
ni"ima da daula" Babu komai kawata" watarana
idan na xama miloniya xanxo kauyenku in da kike
domin in ganki"
Raliya ta harareta" sannan tace"
"A gidan wa xaki ga miliyan din kina fama da
wahalar makaranta"? Kedai suri baki rabuwa da
daukar aradu ta ka"
Suri tayi dariya sannan ta kurawa shuke shuken"
dake a wajen idanu"
koraye shar dasu a cikin fararen duwatsu kamar
tutar nigeria" tace da Raliya cikin sanyin murya"
"Nasan cewar dama xakiyi mamaki Raliya" to
amma kuma bari in rantse miki kiji da kunnenki"
Wallahi gobe i yanxu na gama hayewa" domin
kuwa na mallaki kudi nawa na kaena dala na
gugar dala" dalar amurka har miliyan hamsin"
.
WANNAN wani sirrine a tsakanina dake wanda
bana so kowa ya sani daga ni sai ke Raliya"
"Raliya ta dubi kawarta shekeke har cikin
idanunta" tasan suri da son wasa" to amma
kuma a wannan karon babu alamar wasa ko
karya a fuskar saru" duk a ina xaki sami
wadannan kudade ke da kike a makaranta?
Suri ta sake yi wani makararren murmushi
sannan ta hade fuskarta tace da Raliya"
"Gaskiya wannan wani sirri ne mai girma" to
amma kuma baxan boye miki ba Raliya. Akwai
wani mutum da yake sona kuma yana matukar
kashe mani kudi" kome nace ina so shi yake saya min sunanshi JARMAI amma a gaskiya baxan boye miki ba JARMAI rikakken ƁARAWO ne"
Bashi ya fada mani ba" to amma kuma yasan
cewar na sani" jiya ne da yaxo nan makaranta ya dauke ni a mota muka fita shine yake sanar dani cewar yaji kawunshi tare da wasu mutane suna hirar sirri da daddare cewar akwai wasu makudan kudi da xasu fitar a boye daga matatar man fetur kawun Jarmai masoyina shine babban mai lura
da kudi na cibiyar tace man fetur na kasa"
Kuma a gidanshi Jarmai yake xaune" shine yake so idan sun xo da kudin ya sacesu basu sani ba"
ya kawo mana mu gudu dasu mubar kasar" to
amma kuma ni tuni na yanke shawarar cewar
idan har yaxo da kudin na gansu to sun xama
nawa"
.
RALIYA dake sauraronta kamar wacce ke kallon
mahaukaciya tace da suri"
"to amma ke suri" idan ma ace duk wannan
labari da kika fada mani gaskiya ne" alal misali"
me xakiyi da irin wadannan kaxaman kudi a
duniya?" ina xaki kai miliyan hamsin.....?
SURI ta kalli Raliya cikin rainin hankali tace"
"lallai ke cikakkiyar bakauyiya ce Raliya" ke in
banda abinki a ina kika taba jin kudi sunyi wa
mutum yawa a duniya" tab!
Bari kiji in fada maki" idan kina da kudi a duniya
dole ne ki xauna tare da mutanen da ake ganin
kimarsu a duniya" sannan kuma xaki je wurare
da mutane kejin labari a duniya"
Xaki ci abinci da wasu kejin labarinshi har su
mutu ba xasu taba ganin irinshi ba" koda a hotone" ko aure kikayi dole ne mijinki ya kalleki da
mutunci fiye da kowacce mace" saboda ya san
cewar kema kin dogara da kanki"i dan baki da
kudi a duniya" kina cikin rububi Raliya" babu
wanda yasan kinxo ko baki xo ba"
RALIYA tayi dariya domin kuwa ita har kullum
tana daukar suri ne a matsayin wata birkitacciya
mara kamun kai" tace da ita"
"to bayan kin gama xuwa wuraren da kike so"
sannan kuma kin gama ganin irin mutanen da
kikeso a duniya" sannan kuma kin gama cin
abinci da kike jin labari...." to maganar mutuwa
kuma fa suri" ita kuma nawa xaki kashe ki boye
mata a duniya?
SURI taji gabanta ya fadi ras!! Ta bata rai ta kalli
kawarta Raliya a fusace" bata san lokacin da
takai mata duka a baya ba"
RALIYA ta tashi tana dariya ta nufi dakin
kwanansu" suri tabi ta a guje" 'yan mata biyu
suka haye saman bene da gudu sannan suka
shige cikin wani daki"
.
SHIMFIDA TA BIYU"
.
Ba abinda yafi batawa mutane rai irin ace an
dauke wuta da daddare" musamman kuma a irin
wannan lokaci da aka sheka ruwan sama da
yamma" duk inda mutum ya jepa kafa" ruwa ne
ke cin gudu akan hanyoyi" don haka mutane da
dama suka hankura da fitowa cikin daren domin
shakatawa" tun kafin karfe goma tayi kafa ta
dauke" kamar an sawa mutane dokar ta baci"
Wasu halittu kuma sunji dadi da irin wannan
yanayi" kamar su mujiya uwar 'yan bakin jini"
wacce zata fito a cikin daren tayi shawaginta ako
ina a sararin samaniya" ba tare da sauran
tsuntsaye axxalumai irin su shaho sun ganta sun
takura mata ba" sannan kuma dangin kwaro anan
ma an samu shinge" domin kuwa duk da yake
cewar halittune ma.abota son haske" a wannan
karon sun firfito ako ina a cikin daren" suna marin bangon gidajen mutane babu wanda ya kula tasu"
Idan kuma aka dawo bangaren mutane suma
baxa a rasa wadanda wannan dare ya burgesu ba suke a cikin nishadi" musamman ALHAJI ELBASHIR
wanda yake takai komo a cikin falonshi na sirri da
ya kebe don ganawa da manyan bakinshi" tun
kafin ayi sallar isha'i yake ta inda-inda yana jiran
xuwan abokan shi guda uku" ko kuma ace
abokan satarshi beraye masu malum-malum"
Wadanda suka mara mishi baya" suka wawure
makudan kudi daga asusun man fetur na kasar
nigeria har dala milyan hamsin" A halin yanxu
wadannan kudi an fitar dasu" suna nan a cikin
falon a boye" duk duniya ba wanda yasan wannan sirri" daga wadannan axxaluman mutane barayin
dukiyar talakawa da kasa ke dauka tana yi masu
aiki" sai kuma JARMAI wanda ya rabe a
kwanakin baya yaji mutanen suna kus kus" da
daddare akan wannan mahaukaciyar dukiya da
xasuyi awon gaba da ita kowa ya dibi nashi
kason yaje ya xuba a bankin da yake ajiya"
Elbashir yana nan a tsaye yana duba agogo" har karfe sha daya ta cika har da minti hudu" saiya ji motsin mota.....