Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

RALIYA 03



RALIYA - 03
.
ELBASHIR yana nan a tsaye yana duba agogo"
da karfe sha daya ta cika dai dai harda minti hudu" sai yaji motsin mota a waje" yayi sauri ya leka ta
gilashin tagar falon" yaga mutane uku sun fito
daga cikin mota daya da suka shigo tare" ko
wanne a cikinsu yana fama da katon ciki" kamar
an kifa musu kwarya" sai nishi suke cikin
manyan
riguna" sun kwashi haramun duniya na barci ba.a
gane ba" gashi yanxu da kowa ya farka ma basu daina ba""
Lokacin da barayin xaunen suka halarta shiga
cikin gidan Elbashir" basu ankara da wasu
mutane guda biyu dake boye a cikin filawoyin da
suka xagaye gidan ba" koda yake dai zaifi kyau
idan aka ce dasu ifiritai" domin kuwa ba don
suna
da hannaye da kafafuwa kamar sauran mutane
ba" to ba abinda zai sa a sakasu a cikin sahun
'yan adam" wannan halittu guda biyu sun kure
akan wata sana.a wacce suke ci suke sha da ita shekara da shekaru" kuma basu taba yin wata nadama ko jin tausayin wannan muguwar sana'a ba"
Shiyasa koda Elbashir ya tuntubesu da xancen
wasu bakinshi guda uku da xasu kashe mishi yau da daddare" basuyi wani faragaba ba" tuntuni suke nan a rakube suna xaman jiran xuwa mutanen" suna duba agogo lokaci-lokaci suna yin tsaki a fusace" domin kuwa sun fi so in xasuyi kisa" nan da nan suke so su gama" basa son xaman bata lokaci"
Lokacin da abokan Elbashir suka gama shigewa
cikin gidan" sai ifiritan mutanen buyu suka dubi
juna a cikin duhu" daya yace"
"daya xaka kashe ka bar min biyu" ko kuwa in
kashe daya ka gama da biyun?"
Ragowar dayan ya shafi kan guntuwar bindigar
dake hannunshi sannan yace"
"Bar min biyun kawai ka dauki wannan mai jar
rigar da hula" ni xanyi maleji da biyun dukansu"
yakamata ace su goma ne kaga da xa.a samu
aiki da yawa" amma dai yafi babu"
Ifiritan suka tunshire da dariya cikin shake
murya"
don kada a jiyo su" sannan sai suka fito daga
cikin filawoyin rike da bindigoginsu 'yan kanana"
tsawonsu da girmansu duk iri daya ne" haka
kuma xuciyoyinsu da sana'ar su kayan dake
jikinsu ne kawai suka bambanta"
Daya yana sanye da bakin wando da shudiyar
singileti mai hannu"
Daya kuma yana sanye da koren wando da kuma bakar riga mai hoton damisa a bayanta" basu tsaya jiran komai ba" sai suka shige cikin gidan ransu a bace"
.
************* ********** ******** **********
.
Suri tana tsaye ita kadai a saman benen" ta dafa
karfen matari tana kallon jepi jepin masu gadin
dake gilmawa rike da cociloli a hannayensu" da
kuma sauran daliban dake dawowa daga cikin
gari suna shigowa makarantar" wadanda ruwan
da akeyi da kuma sahun daminar bai hanasu fita
kallon sinima ba" da kuma xuwa hira wajen 'yan
matansu da basu kwana a cikin makaranta"
Iskar daren ya busa da karfi" reshikan
bishiyoyin dake makarantar suka rausaya a lokaci
guda" sannan ganyaye suka farfado kasa"
Suri ta lumshe idanunta cikin jin dadi" a lokacin
da iskar ta doki fuskarta tare da watso mata
kwayoyin ruwan dake makale a sararin samaniya
wadanda tun lokacin da ana ruwan Allah bai basu
ikon fadiwa tare da 'yan uwansu ba"
Suri tayi murmushi data tuno abinda ta tabbatar
yana can yana faruwa a wani wuri" a daidai
wannan lokaci" tun lokacin da Jarmai ya
gwangwadawa Suri labarin wannan dukiya da
xai sato daga wurin kawunshi ta fara
tunanin abinda xatayi da dukiyar" domin kuwa
tasan cewar indai sunxo to sun xama nata har
abada"
ta riga ta gama shirya duk yadda xatayi ta
yaudari masoyinta Jarmai ta kwace dukiyar ta
gudu da ita cikin uwa duniya"
Daga nan ba wanda zai sake jin duriyar inda
take" sai dai in ana labarinta idan ta fara gina
kampanoni" tasan cewar mutane da dama xasu
tsananta binciken yadda akayi ta xama biloniya
tun tana budurwa ko karatu bata gama ba" tace
a xuciyarta" Idan na sami kudin dole ne ayi
shakkar tabani" suri ta sake murmushi"
Dole ne suri ta riga girmama kudi da dala a
duniya
Domin kuwa taci bakar wahala a rayuwarta
kamar 'yar mahauniya" tun lokacin da aka yaye
ta a hannun wata azababbiyar kakarta ta girma"
wacce kullum idan xa.ayi lissafin gaskiya bana
dokin rano ba" to sai ta lakada mata shegen
duka sau bakwai ko sau tara a rana"
kuma ba wani laifi ma take yi ba" laifin dai kenan
idan ta dora mata talla bata sayar ba" kuma a
kullum kakar suri takan dora tukwanen shinkafa
gudu uku manya-manya kamar mai saida kan
awaki" Haka suri ta rika daukar su a bangaji daya bayan daya" duk sai sun kare"
Idan dare yayi aka xo kan lissafin ribar da aka ci"
kullum kafin suri ta kwanta barci sai kakarta ta
nemi lafiyayyen itace tayi mata dukan ala-tashemu lafiya" domin kuwa a ka"ida indai akayi lissafi ba.a ci ribar jaka uku ba" to suri ta banu ta lalace"
.
SAI lokacin da ta samu ta gama sakandire ta
shiga jami.a sannan ne Allah ya raba suri da
masifar wannan kaka tata" domin kuwa tun
lokacin da ta kawo karpi suka fara sa"insa da
tsohuwar"
Watarana suri ta koma gida hutu daga jami"a tayi
xanxaro da jaket mai ruwan kasa" wadanda
samarinta na jami.a 'yan duniya suke saya mata"
xaman ta keda wuya" ko ruwa bata sha ba" sai
kakarta ta nufi murhu ta fara neman itatuwa tana cewa"
"Ai naji dadi da wannan hutu da kuka samu suri"
dama duk na kosa ki dawo wallahi" haka nan
nake xaune ba cas ba as" tun da kin dawo da
wuri yanxu bari in dora maki shinkipa ko tiya
hudu ne" tunda rana tayi" ala bashi gobe sai mu
tashii da shiri" mu girka shinkafa tiya takwas
wake tiya uku"
SURI tayi banxa da tsohuwar tana ta kicin kicin
ragar shinkafa" bayan taci aikinta ta gama
shinkapa ta nuna cike da tukunya" sai kakar suri
ta leka daki" ta sameta tana duba alban din
hotunan da suka yi ita da kawayenta da kuma
samarinta a jami.a" kakarta ta daka mata tsawa
tace"
"ke nake jira ga shinkapar can xan kwashe" so
nake kiyi hanxari shinkafar tayi rana in kinje can saiki ci taki"
SURI tayi murmushi sannan tacewa tsohuwar"
"kaka ai wannan xamanin kuma ya wuce" yanxu
ni 'yar jami.a ce ba 'yar sakandire ba ce!"
Tsohuwar ta matso kusa da ita ta rike kugu tace"
"suri ubanki nace" ko bakya jina" nace ubanki!!"
wato har kin fara koyo fitsara daga xuwanki
jami.ar?" to bara in fada maki" wallahi tallahi ko
ferfesa kika xama a gidan nan sai kin daukar min
tallata" xaki tashi kije ki nada gammo ko saina ci ubanki?"
Suri ta sake yin murmushi sannan taci gaba da
bude alban din hotunanta" bata ko daga kai ta
kalli tsohuwar ba" kakar tace"
"Au! To nasan abinda kike so" kin rabi da samu
ne shiyasa" tayi sauri ta fita waje ta nufi inda
take ajiye itacen konawa" ta xabo wani mukeken
faskare tana ta sumbatu tana ce"
"Ina amfanin abaka rikon maraya" tun kina
jaririya da iyayenki suka yanke jiki suka fadi"
shegiya nina daukoki ina ta wahala dake" wato
yanxu kin girma kin shiga jami.a" shine xaki yi
min ixkanci" to baki isa ba yarinya"
Tsohuwar ta fada cikin dakin rike da faskarenta"
suri ta mike a fusace ta rike itacen a lokacin da
tsohuwar take shirin kawo mata duka tace"
"Gaskiya fa kaka wallahi baxan yarda kullum kice
xaki rika dukana kamar kin sami jaka ba" yaya
kawai na girma zaki rika takura wa rayuwata"
yakamata ki rika wayewa" ki gane cewar da fa"
ba yanxu bane"
Tsohuwar ta xaro idanu cikin mamaki tace"
"Ni ai banyi ilmi ba" bansan komai ba sai talla da
duka" kuma tunda kince min kin girma kin wuce
duka da talla" to mu xuba ni dake shege ka fasa"
dan halak sai yanka"
Tsohuwar ta kama jikarta da kokawa kici-kici" da
yake irin mutanen da ne" tasha sauyoyi da jike-
jike tana nan garas da karfinta" ta dauki suri ta
buga da kasa" ta shake mata wuya da kumbunan
hannunta"
Da suri taga tshohuwar xatayi mata lahani" saita
xame jikinta" sannan ta tashi ta ruga a guje ta
nufi kofar gida"
tsohuwar tabi ta a guje cikin tsautsayi sai taci
tuntube da tukunyar miya a kafafuwa ta fadi ta
sake wuntsilawa" kakar suri ta fara kururuwa
mutane suka shigo suka kawo mata dauki" bayan
an duba tane aka ga ta karye guri biyu a kafarta" ta dama sannan ta goce a hannunta na hagu"
Tun daga wannan rana ta xama gurguwa" kuma
tun daga nan suri ta sami sauki" dole sai dai ita
ke dawainiya da ita" shiyasa suri take bin samari
'yan duniya suna kashe mata makudan kudi" rabi
tayi hidimar karatunta" rabi kuma ta aikawa
kakarta gurguwa wacce ke xuwa yawon bara da sanda"
.
A halin yanxu da suri take tsaye a saman benen
cikin duhu" tana shakar daddadar iska mai cike
da kamshin damina" kuma mai sanyaya xuciya"
saida ta tuno da axababbiyar kakarta dake acan
gida tana yawon bara" daga gobe kakarta ta
daina xuwa bara" suri tace a xuciyarta tana
murmushi a bayyane" domin kuwa gobe ne xan
xama miloniya" daga ni har dangina mun gama
shan wahala a rayuwarmu ta duniya" Allah yasa
Jarmai yayi nasara yaxo mana da kudin"
.
Suri ta bar jikin karpen benen cikin fara.a ta
nufi
dakinsu ita da Raliya" da kuma wata iyamura mai suna MARY
Da xuwa ta sami Raliya xaune gaban kyandir din
dake a jikin teburin karatun su" ta bude
wargajejen akwatinta mai taya baki" tana ta
kimtsa kayanta a ciki wasu ma basu bushe ba"
haka nan take ta faman cusasu" suri ta matsa
kusa da ita" ta dafa kafadar Raliya tace-;
"Allah sarki kawata" shike nan xaki tafi ki barni"
Raliya tayi murmushi" sannan ta dubeta"
"Kada kidamu suri" tace da ita" sannan ta dauko
wata rigar mama ta jepa a cikin akwatin kayanta"
wata rana ai xamu sake haduwa" in dai bake ce
kika jepar dani ba"
Suri tace
"Baxan taba jepar dake ba Raliya" duk da yake
xan xama miloniya baxan mance dake ba" da
karpe nawa xaki tafi goben?"
Sammako xanyi tun da sassafe" Raliya tace da
suri" sannan ta koma kan littatafanta dake xube
akan katifarta" suri ta dafa kawarta sannan tace da ita cikin murmushi...