Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

RALIYA 04

RALIYA-04
.
"SAMMAKO xanyi tunda sassafe" Raliya tace da suri. Sannan ta koma kan littatafanta dake xube
akan katifarta" suri ta dafa kawarta sannan tace
da ita cikin murmushi"
"zuwa lokacin kudina sunxo" in da rabonki kema
xan dan yaga maki ko dubu dari ne" kawata ko
kuwa me kika gani?"
Raliya tayi tsaki" sannan ta debo littatafan ta
xuba a akwatinta"
.
=======>*******<========
LOKACIN da abokan Elbashir suka shiga cikin
falon ne" suka same shi a tsaye!!
"ku nake ta xaman jira" tun daxun. Na dauka
cewar baxa ku sami xuwa bane"
Daya daga cikin bakin uku ya hade fuska yace"
"Haba Alhaji me xai hanamu xuwa kuwa?"
maganar kudi ba maganar wasa bace" yi sauri ka fito mana dasu kowa ya dauki kasonshi"
Elbashir ya dubi fuskokinsu yaga ko wanne a
murtuke yake basa fara'a yasan cewar tuntuni
tun lokacin da suka mara mishi baya ya wawuro wadannan kudade" dama suna xargin da wahala idan bai ha'incesu ba a wurin kasafin da xa'ayi to amma kuma da ace ma anan kadai abin xai tsaya to da da sauki"
"Ina fatan dai ba wanda yasan wannan magana"
domin kuwa wannan sirrine tsakaninmu mu hudu"
wani mai katon kai a cikin bakin yace a fusace"
"Haba Alhaji sau nawa xakayi mana wannan
tambayar?" kada ka daukemu kananan yara
mana" duk duniyar nan wa xamu fadawa irin
wannan sirri mai girma" yanxu maganar kasafi takawo mu" ka gaggauta don mu gama da wuri
kaga dare na kara yi"
Elbashir yayi murmushi" maimakon ya shiga cikin
dakin ya kinkimo akwatin kudin" sai suka ga ya
tafa hannayenshi fas!!
Bakin suka dubeshi a tsorace cikin rashin yarda
domin kuwa sun san cikakken ibilishiii ne" yanxu
haka wata makarkashiya yake so ya kulla musu"
kafin su san me yake faruwa ne" sai suka ji karar
harbin bindiga a bayansu" mutum biyu a cikinsu
suka yi koli-koli a cikin falon suka fado kasa
cikin
jini ko shurawa basu yi ba" dayan kuma yana
inda-inda a rude" sai wani harsashi ya sheko a
guje ya fada cikin malum-malum din da ya jibga" ba wanda yasan inda harsashin ya nufa da gana nan" sun dai ga mutumin yayi tsalle ya hadu da
bango" daga nan wurin yayi tsit kamar anyi ruwa an dauke" gaba daya mutanen sun tafi barxahu"
.
A gaisheku jarumai"
Elbashir yace da ifiritan samarin biyu wadanda ke
tsaye a bakin kofar falon" bindigogin su na fitar
da tiriri" suka matso xuwa cikin falon" suka dubi
gawarwakin mutanen da suka kashe"
Mai bakar rigar yace a fusace"
"Akwai wani aikin da xamu sake yi maka kuma
Alhaji?
Elbashir yace dasu"
"Ina so ku kwashe su ku sakasu a mota" nabar
muku su kyauta idan kuna so" Nidai ku kwashe
min su daga nan" Amma ku tabbatar kun batar
dasu ta yadda har abada baxa a gano su ba"
bayan kun gama sai ku dawo in sallameku
ragowar kudinku"
Nan da nan Ifiritan biyu suka fara kinkimar
gawarwakin bakin da suka kashe daya bayan
daya" suna kaisu cikin motar da suka xo da ita"
awaje"
.
Wadannan ifiritai biyu da basu dauko
rayukan mutane a bakin komai ba" suna da
tarihin rayuwarsu kamar yadda ko wanne dan
adam yake da nashi tarihin"
Matsalar kawai itace su nasu baiyi kama dana
sauran mutane dake a duniyar mutanen kirki ba"
Mai bakar rigar wacce ke da hoton damisa a
baya" sunanshi DUMFANA" mahaifiyarshi ce
kawai data rage masa a duniya" ita kadai tasan
sunanshi na gaskiya" ita ma kuma rabon da ta
sakashi a idanunta bana shekara goma sha biyu (12) cif-cif" tun wani ciwo da yayi a wajen
yawon
duniyar shi aka mayar dashi garin su" bayan ya
warke sai ya sake baxama ya fito" tun lokacin
bata kara jin duriyar shi ba" don haka babu
wanda xai ce yasan sunanshi"
.
Shi kuma dayan mai shudiyar singileti sunanshi GAMBO" amma kuma shi a iya cewa sam barka
ansan sunanshi na lakabin rana wato DANLITI saidai kuma idan mutum ya shekara yana neman shi
indai ba Gambo yace ba" to da wahala ya samu
wanda xaice ya sanshi"
Wannan shakiyan samari guda biyu abokan juna
ne na GANI KASHE NI" domin kuwa a wajen
yawon dambe suka hadu" daga sana'ar dambe
kuma sai suka koma satar kekuna"
Bayan nan sunyi sana'o'i da dama" daya bayan
daya dukansu na alatsine da tir!!
Daga bisani ne suka ci birki a guda daya wato
sana'ar kisa da gangan" Idan kuma sun dauki
lokaci mai tsawo basu sami wanda xa'a kawo su kashe ba" sukan tuna baya suje suyi fashi da makami"
.
GAMBO DA DUMFANA" suna kammala kwashe
mushikan barayin" suka xubasu a mota suka tuka
a cikin daren suka tafi" su kadai suka san inda
xasu kaisu su watsar" Elbashir yayi ajiyar xuciya daya ji sun tafi da motar"
ya shiga cikin daki ya jawo bakar akwati mai
tayoyi wacce ke cika FAL da makudan kudin" ya
xauna dirshan a falon kamar dan shayi" ya bude akwatin a tsanake ya dubi sababbin dalolin amurka suna ta sheki a ciki"
Yayi murmushin farin ciki" domin kuwa duk
duniya shi kadai yasan wannan lamarin a halin
yanxu babu wanda xai tona mashi asiri"
Elbashir yayi jugum a xaune yana kallon kudin" alokaci guda yana tunanin abubuwan da xaiyi
dasu a duniya"
.
Abu na farko daya fara xuwa mashi a rai
shine.....