RALIYA-05
.
RALIYA ta shiga cikin motar ta xauna
tare da sauran fasinjojin" yaron ya shigo ya
rufe kofar direban yaja suka tafi" Ga al'adar
xaman mota ba wanda ya damu da wani" fasinjoji ne duk da raliya baya a gaba biyu na a
kujerar tsakiya"
mutum hudu sun warwatsu" a sauran
kujerun
baya" kowa yana ta tunanin da ya
dameshi"
kamar yadda raliya ta dukufa yin
nata tunanin"
bayan ta ciro kudin mota ta bayar"
Ba a fi minti biyar ba da fara
tafiyar su ba sai wani
fasinja ya sake tare su cikin sauri"
yana sanye da
gajerar riga da wando mai ruwan
kasa" yana
dauke da nashi murgujejen akwatin a
hannunshi"
yaron motar ya bude kofar bayan
motar ya tsaya"
Sannan ya bude but din motar yakai
hannu ya
amshi akwatin fasinjan" da farko
mutumin bai so
ya bashi akwatin ba" domin kuwa yafi
so ko ina
xai xauna ya kasancee tare da
akwatinshi domin
kuwa ba abin wasa bane a ciki"
to amma don kada mutane su
xargeshi saiya
mikawa yaron motar ya saka a cikin
but din
motar" tare da akwatin Raliya wacce
xata koma
kauyensu" shi kanshi yaron motar
saida abin ya
bashi sha'awa daya ga an jera
Akwatina biyu irin
su daya a bayan motar" kowanne
yana ta sheki ajikinshi an rubuta
(Japan Express )
.
Yaron motar ya dawo cikin motar ya
xauna"
direban yaja suka tafi" wannan
fasinja daya shigo
motar yanxu" mai akwati irin na
raliya 'yar
makaranta" akwai alamar damuwa
mai yawa a
tare dashi" domin kuwa shima tun
sanda ya shigo
yayi tagumi" motar tana tafiya yana ta
faman
waige-waige sai kace yana
tsammanin wasu
suna biye dashi"
TO amma kuma idan ma har yayi
wannan xato ba
laifi bane domin kuwa shi kanshi
yasan cewar ya
kinkimowa kanshi uwar rigima"
wacce idan ba
wata kwakkwarar sa'a ya taka ba" to
xai yi wahala idan bai bar baya da kura ba"
mutumin yayi ajiyar xuciya sannan ya dubi
budurwar dake
xaune kusa dashi mai yiwuwa irinshi
ce" duk abin
duniya ya isheta" to amma kuma
matsalarta
tasha banban da irin nashi" gashi dai
sun shigo
mota daya" sannan kuma akwatinan
da suka
shigo dasu cikin motar duk irinsu
daya" amma
kuma basu damu da suyiwa juna
magana ba"
Lokacin da mutumin ya dubi yatsun
Raliya ne sai
yaga wani xobe a dan yatsanta
wanda yayi kama
da xoben da ya taba ba masoyiyarshi
dake jami'a baiyi kawaici ba saiya
tambayeta cikin tausasa murya"
"Yan mata ina kika samu wannan
xuben don Allah?"
Raliya ta dube shi a karo na farko
tun
shigowarshi cikin motar" sannan tace
dashi cikin
mamaki"
"Kamar yaya ina na samu wannan
xoben" malam
wannan wacce irin tambaya ce
haka?"
RALIYA tayi tsaki sannan ta kawar da
kanta xuwa
wani bangare tana kallon bishiyoyin
dake wucewa
a gepen titi" domin kuwa tasan cewar
dama
akwai irin wadannan mutanen masu
karambanin
yiwa 'yan mata magana a mota"
Gashi kuma ita ba a irin wannan
surutun da ita in
har tahau mota to da xarar ta biya
har a sauka
ba wanda xaiji muryarta" Ralita tayi
tsammanin
mutumin ya rabu da ita" to amma
kuma xuwa
can sai taji ya sake yafitota a
hankali" lokacin da
ta juyo ne a fusace ta dubeshi sai ya
dukar da
kanshi kusa da kunnenta yace da ita"
"Kiyi hankuri 'yan mata dama ba wani
dalili yasa
nayi maki wannan tambayar ba" ina
da wata
masoyiyata ce dake jami'a wacce na
taba bata
irin wannan xoben" sunanta SURI ni
kuma sunana JARMAI"
.
======>*****()******<=======
ALHAJI ELBASHIR ya dauki tsawon
lokaci akwance bai san inda kanshi yake ba"
jinin dake
xubowa kadan" kadan" daga cikin
raunin dake a
kanshi ya gangaro yana malala a
fuskarshi"
bayan ya kwashe kwararan awoyi
biyu a haka"
xuwa can sai numfashinshi ya dawo"
sannan ya
fara motsa yatsun kafarshi da kuma
hannayenshi"
ya dauki lokaci mai tsawo yana haka
kafin ya fara
yunkuron tashi ya xauna"
Duk wannan abu dake faruwa
hankalin Elbashir
yana kan akwatin kudinshi da ya
bari a bude a
tsakar falon" har xuwa lokacin da ya
tuno cewar
an sami akasi wata matsala ta faru"
bai amince
da xargin da yake rayawa a ranshi ba
na tunanin
wani ya shigo ya tafi da akwatin"
Yasan cewar hakika an shigo bai
sani ba" kuma
ya tuno cewar an kwada mashi wani
abu mai
kamar karfe akai" to amma kuma duk
da wannan
yana saran idan ya farfado xai laluba
yaji ba su"
to tabbas dole ne ya amince da
xargin da baya
so" wanine ya shigo yayi awon gaba
dasu" wanda
kuma idan har haka din ta kasance to
dole ya
dauki mataki kwakkwara"
Elbashir ya samu da kyar ya tattara
karfinshi wuri
guda" ya fara kokarin tashi ya xauna"
to amma
kuma juya tana dibarshi" da xarar ya
kusa
xaunawa sai kuma ya koma ya sake
faduwa yaraf! Sai kace yasha barasa"
Bayan yaga wahala yana kokartawa"
xuwa can
saiya samu sa'a ya xauna" tun baya
iya ganin
komai sai duhu" har ya share
fuskarshi da
hannun rigarshi" sannan ya fara
ganin abubuwa
dake a cikin dakin"
to amma kuma cikin rashin sa'a sai
yaga wayam"
babu katon akwati" nan da nan sai
yaji gabanshi
ya fadi" ya sake waigawa ko ina a
cikin falon" babu akwatin kudi ba dalilinshi"
"DALA MILIYAN HAMSHIN" shinkenan sunbi ruwa" Amma kuma dole ne
ma ya nemo su ko ina suka shiga a duniya"
Elbashir yace a fusace" ko xan rasa raina saina
dawo da abina!" ya karashe maganar cikin daga
murya"
Yana nan cikin falon yana ta surutai shi kadai
saiya kai ganinshi xuwa tsakar dakin inda yayi
male-male a lokacin da hadarin ya faru" Elbashir yaga wani dan mabudin mota a kasa akan
darduma" nan da nan yayi hanxari yakai
hannunshi ya dauki mabudin" dubawarshi keda
wuya sai yaga hoton Jarmai a cikin gilashi a
baya kuma hoton wata budurwa ne" to amma
kuma bata hoton budurwar yake yi ba" Ganin
hoton Jarmai da yayi shiyafi komai tayar mishi
da hankali" domin kuwa a halin yanxu ya
tabbatar da abin da ya faru ko shakka babu
Jarmai ne ya shigo yayi mishi wannan muguwar ta'asa"
"JARMAI..!!!" Elbashir ya tambayi kanshi cikin
mamaki" bai taba tsammanin Jarmai yasan da
wannan sirri ba" na wadannan makudan kudi da suka sata daga gwamnatin tarayya" Gashi yanxun
ya biyo sawunsu kuma yayi nasara" tabbas
Jarmai ne ya shigo ya doke shi" ya dauke
akwatin kudin ya gudu abinshi"
Tun Jarmai yana karami Elbashir ke rike dashi"
wannan ya samo asali ne a lokacin da yayar
Elbashir mai suna LANTANA taxo ta sameshi da
maganar hatsabibancin da danta Jarmai yake yi mata" baban Jarmai ya dade da mutuwa yabarta
da rigima" mahaifiyar Jarmai ta kaishi karatun
allo can wani gari mai nisa" domin ta huta da
axabarshi" acan makarantar ko sati ba'a yi ba
jarmai ya rotsa kan almajirai uku da allo suna
fada" da malamin yasa a kamo shi ne ya gudu" akasa ya dawo gida bayan ya kwana biyu yana
tafiya"
A ranar da ya dawo ya kwashe tiramen xannuwan
mahaifiyar shi Lantana ya sayar yaje aka cinye
kudin a wajen caca" Da Lantana ta kwashe duk
wannan labari ta shaidawa dan uwanta Elbashir sai yace ta kwantar da hankalinta xai yi mata maganin Jarmai zai daukoshi su xauna tare" tun
daga wannan lokaci shekaru ashirin kenan xuwa yanxu" Jarmai yana hannun Elbashir " ya sashi a makaranta tun yana karami amma yaki karatu"
ganin haka saiya mayar dashi boyi-boyin gidanshi
yana aikenshi wurare daban-daban" yana taka
tsan-tsan da halinshi" Daga lokacin da Alhaji
Elbashir ya fara xama da wannan hatsabibin da
nashi Jarmai ya kamashi da laifuka da dama"
kadan daga ciki sun hada da dauko matan banxa
yana kawosu gidanshi" da kuma shaye-shayen
kayan maye"
To amma kuma duk wadannan laifuka basa
damun Elbashir " abban abinda ya tsana a
rayuwarshi ta duniya shine ayi mishi sata" daka
daukar mashi kwandala daya ya gwammace kayi
tatul da giya kaxo ka xaxxageshi kayi ta kwara
mishi amai a jikinshi"
shiyasa suka dade tare da Jarmai basu bata ba
shekara da shekaru" domin kuwa Jarmai baya
daukar mashi ko anini" idan yana son kudi yakan xo ya tambayeshi"
To amma gashi yanxu ba xato ba tsammani
Jarmai ya sake hali" ya fara sata gawurtacciya"
babu mamaki dama can kwanton bauna yayi"
hakika ya shammaci kawunshi Elbashir to amma kuma baiyi nasara ba" Elbashir yace a xuciyarshi"
xan nemoshi duk inda ya shiga" ya daga mabudin
motar a saitin fuskarshi ya dubi hoton Jarmai
cikin tsananin fushi kamar ya jawoshi a cikin
hoton ya kashehi" yace dashi cikin kunan rai a
bayyane"
"Asirinka ya tonu munafuki" saina kamaka duk
inda ka shiga" kuma saika dawo min da kudina"
DALA MILIYAN HAMSIN" baxa su taba kubce
mani ba"! Saina ganoka yaro"
.
Elbashir ya mayar da numfashi sannan ya shiga
cikin wani daki dake jone da falon" da shigarshi
yakai hannu inda wayarshi ta sadarwa take akan
wani teburi karami" ya danna lambobin wayar"
sannan ya saurara yana rike da hannun wayar a
kunnenshi" xuwa can ya fara magana a fusace"
"Hello! Nine Alhaji Elbashir
"Yi maxa ka kira min kwamishinan 'yan sanda
kace nine ke magana" akwai muhimmiyar
maganar da xamu tattauna dashi"
"Zuwa can Elbashir ya dakawa wanda suke
magana tare tsawa sai da dakin ta masa kuwwa"
"Yayi barci?" kace a tasheshi babu lafiya ne" bana
so kana bata min lokaci"
A daidai lokacin ne akayi walkiya mai haske a
sararin samaniya" sannan akayi tsawa" yayyafi
mai sanyi ya biyo bayan haka"
.
=======>******^*****<======

.
Kwamishinan 'yan sanda C.P RAIYANU
DANMASANI yana xaune yana fuskantar
mataimakan aikinshi su biyu sun yi mishi tsuru"
suna sauraron abinda xaice dasu" domin kuwa
tun lokacin da ya buga masu waya a gidajensu
yasa matansu suka tattashesu a cikin wannan
talatainin dare yace su hanxarta xuwa su
sameshi yana a gida yana jiransu"
Sun san cewar babu lafiya inma kuma da lafiyar
to akwai wani babban al'amari daya faru mai
Zafi-zafi wanda yake bukatar jan damarar yaki"
Kwamishina 'Danmasani dogo ne dan kimanin
shekaru hamsin a duniya" fuskarshi ta fara
tattarewa kadan" sannan kuma furfura ta fito jefi-jefi a cikin sajenshi da kuma tumbujejen gashin bakinshi" kullum kanshi a aske yake kamar tulu"
tun lokacin da yana karamin ma'aikaci yana
matukar alfahari da..............
