RALIYA-06
.
TUN lokacin da yana karamin ma.aikaci yana
matukar alfahari da jajayen idanunshi dake boye a cikin loko kamar idanun maciji" da kuma
faskeken hancinshi da ya tsare rabin fuskarshi"
sau da yawa idan ya hade fuska ya kalli mai laifi" tun kafin yace wani abu wasu ke fara kuka" domin kuwa har gara mutum ya hada idanu da namijin zaki a daji da ya hada ido da DAN MASANI
.
Mataimakanshi biyu da yafi shakuwa da su A.C.P AMINU JAN ZAKI" da kuma ACP BILYA dukan su suma tsofaffin Ma'aikatane da suke dade suna shan damara tun a xamanin yakin basasa"
Har yanxu a ckinsu babu wanda ya mallaki
abinda ya wuce gida da kuma tsohuwar mota
banda motar ofishi da ake xuwa da ita a
daukesu" har gara kwamishina yana da 'yan
kadarori da ba'a rasa ba" to amma kuma idan
aka kwatantasu da hidimar da yake yi da
bila'adadin 'yan'yanshi sai dai ayi hamdala amma kuma baxa ace an samu yadda ake so ba"
Kwamishinan 'yan sanda ya dubi fuskokin
mataimakanshi dake xaman jiran yace dasu wani abu" ya gyara xama sannan yace"
Nasan cewar xakuyi matukar mamaki a dalilin
wannan kira da nayi maku" wata magana ce ta
taso mai girma a tsakanina da ku" Ina so ku
tattara hankalinku wuri guda" domin kuwa mun
sami dukiya mai yawa wacce xata amfanemu da 'ya'yanmu da jikokinmu har karshen rayuwarmu
Amma sai kun bani goyon baya" mun hada kai
sannan xamu cimma wannan dama data fado
hannunmu"
Tsofaffin 'yan sandan sukayi saurin gyara xama
da sukaji maganar da kwamishina ya fada" nan
da nan suka girgiza kawunan su domin su
karfafa mashi gwiwa yaci gaba
"Yanxun nan bada dadewa ba" kwamishina yaci
gaba" Alhaji Elbashir ya kirani a waya" har nayi
barci yasa aka tasheni" dana dauka ne yake
sanar dani gaskiyar abinda ya faru a tsakaninshi da wani dan uwanshi" wani yaro mai suna JARMAI
Elbashir ya sanar dani cewar Jarmai ya sace
mishi kudi har dala miliyan hamsin" ya gudu dasu a cikin daren nan" ya sanar dani ne domin mu taimaka mishi cikin gaggawa a samu a kamo barawon tun kafin yabar garin" yace zai bamu ladan dala miliyan daya" idan har muka taimaka mishi muka kamo Jarmai
Tsofaffin dake sauraron kwamishinan suka kalli juna cikin murmushi" domin kuwa ladan aikin yana da yawa" akalla zasu sami kudi mai tsoka
ACP Aminu jan Gwarzo yace cikin doki"
"Ya kamata mu gaggauta mu kamo barawon
domin kuwa dala miliyan daya kudi ne masu
yawa yallabai
ACP Bilya yace"
"Kwarai kuwa yallabai indai xai cika mana
wannan alkawarin lallai ya kamata mu kokarta
mu kamo barawon cikin hanxari"
Kwamishinan 'Dan masani yayi murmushii sannan ya dawo cikin kankanin lokaci ya murtuke fuskarshi" mataimakanshi biyu suka yi ajiyar zuciya" domin kuwa murmushinsa yafi xama abin tsoro fiye da abin sha'awa yawancin murmushin yafi kama da yanayin da xaka gani a fuskar busasshen tsohon da aka tsirawa allura
.
Har yanxun baku fahimci inda bayanina yasa
gaba ba" kwamishinan yace dasu" wadannan kudi
da yake so mu kwato mishi kada ku taba
tsammanin idan suka xo hannunmu xamu mayar
masa" domin kuwa shima ba nasa bane" kuyi
tunani xaku fahimci abinda nake nufi" a ina
Elbashir xai samu dala miliyan hamsin a kasar
nan"?"
Nasan cewar shima sato su yayi a asusun
matatar man fetur yana so ne mu rufa mashi asiri
da xarar kudin sunxo hannunmu sun xama namu
wannan rabo ne daga sama ya fado a hannunmu"
Tsofaffin 'yan sandan suka dubi junansu" cikin
tsananin rudewa da murna" domin kuwa indai har
abinda kwamishina ya fadi gaskiya ne" to hakika
sun gama hayewa" kwamishina yace dasu"
"Ina so kuyi hanxari kuje can ofis ku sami yara
hudu ko biyar na amana wadanda xasu yi mana
wannan aikin" ina so kafin nan gari ya waye su
nemo mana shi Jarmai din" suxo mana dashi
nan" kun ga da xarar sun kamo mana shi sai mu amshe kudin mu boyeshi a inda baxai kara
fitowa ba har abada" balantana ya tona mana
asiri" kun ga sai mu kasa wannan kudi kowanne a cikin mu ya adana abinshi domin akwai hadari idan muka ce xamu kai banki" yafi kyau musan inda xamu boyesu a gidajenmu" ko me kuka gani?"
.
Wannan haka yake yallabai" suka ce a lokaci
guda a cikin biyayya" a cikin dan lokaci kankani
har sunyi sharkaf da xufa duk da yake cewar
yayyafi akayi a waje" nan da nan suka tashi a
cikin daren suka baxama domin xuwa ofishinsu
su nemi 'yan sandan da xasu yi masu wannan
aikin cikin gaggawa"
Har xuwa lokacin da tsofaffin 'yan sandan suka
tura rundunar 'yan sanda domin a nemo musu
JARMAI babu wanda yayi ma wani mgana" domin
kuwa tunanin wadannan makudan kudi ta gama
rudasu" kowanne yana tunanin abinda xae fara yi
da xarar kudin sun xo" suna cikin tafiya ne a
mota xasu dawo gida" sai ACP aminu ya bugi
kafadar abokin aikinshi bilyaminu yace dahi"
mutumin naga kayi shiru ne! Tunanin me kake
yi?"
Bilya yayi ajiyar xuciya"
"tunanin wadannan kudin nake yi" Ina ta lissafa
abubuwan da xanyi dasu ne"
"Wata xuciyar tana raya min inje kasar rum in
gina kamfanin karafa acan"
"Amma kuma nafi so in koma kasar japan in hada
hannun jari da wani kamfanin kera bindigogi"
.
ACP Aminu yace dashi"
"Ni kuma tuni na yanke shawarar komawa kasar
swizilan in gina otal nawa na kaina" Daga nan
kuma ni da wannan kasar har abada Allah ya
rabani da talauci"
'yan sandan biyu suka fashe da dariya lokaci
guda" abinda basu sani ba shine tuni har
kwamishina ya gama shirya irin kisan da xaiyi
musu a boye" da xarar kudin sunxo hannunshi"
.
======>*****^*****<========
:
"SURI?" Raliya ta tambayi mutumin cikin
mamaki" ya akayi kasan kawata suri malam?"
jarmai yayi mata murmushi yace"
"masoyiyata ce" bata taba baki labarina ba?"
RALIYA ta girgixa kanta alamar bata taba ji ba"
Hakika wannan xobe dake a yatsanta suri ta
mallaka mata shi a daren jiya domin ta rika
tunawa da ita" gashi yanxu kuma ta hadu da
masoyin suri a mota kuma ya gane xoben shi" daya ba masoyiyarsa"
RALIYA ta tuno maganar da sukayi ita da suri a
yammacin jiya inda take shaida mata cewar"
AKWAI WANI SAURAYINTA RIKAKKEN BARAWO MAI SUNA JARMAI
raliya taji gabanta ya fadi ta dafe kirjinta" a
tsorace sannan ta sake kallon Jarmai wanda ke xaune a cikin fasinjojin motar yana yi mata
murmushi" taji tsoro ya kamata" to amma kuma
da yake taci sa'a ta kusa sauka daidai hanyar da xa'a bi a nufi kauyensu bata damu ba"
Jarmai ya mayar da hankalinshi a wajen nashi
tunanin da yaga raliya bata son hirar" domin
kuwa shima yana da nashi tunanin da ya dame shi a xuciyarshi" to akalla dai yanxu yana kyautata
xaton yayiwa kawunshi Elbashir nisa" domin
kuwa koda ace Elbashir ya sanarwa 'yan sanda"
bazasu taba kawowa a ransu cewar xai gudu ya boye a wani kauye ba" xasu bishi can wani waje
ne inda suke tsammanin ya nufa" kamar tashar
jirgin sama"
"to amma kuma gashi ya shammacesu ya dauko
murgugujen akwatinshi wanda ya cika FAL da
miliyoyin kudi na dalar amurka" ya shiga motar
haya xaije wani kauye ya labe sai kura ta lafa"
sannan sai ya biyo dare ya dawo ya dauki
masoyiyarshi suri su gudu da kudin su"
Jarmai yayi murmushin farin ciki da ya tuna irin
holewar da xaiyi a duniya da wadannan kudi bai
san cewar suri ta gama shirya hanyar da xata bi
tayi mashi wayo ba ta amshe akwatin ta gudu da kudin ba"
.
SURI tana can makaranta tana ta duba agogo
tana tsaki" domin kuwa ta kosa taga Jarmai" ta
kosa ta amshe kudin ta koma garinsu ta dauke
tsohuwar kakarta gurguwa su gudu xuwa wata
duniya inda xasu more kudinsu hankalinsu a
kwance ba tare da 'yan sanda sunbi sawunsu sun takura musu ba"
.
Motar taci gaba da sheka gudu akan titi" xuwa
can RALIYA ta hango lambar kauyensu dake a
bakin titi an rubuta DAN MARKE nan da nan tayi sauri ta taba yaron dake gyangyadi"
"Akwai wajen lambar can! Akwai......."
Yaron motar ya cewa direban cikin sauri"
"In kaje Dan marke akwai mai sauka"
Motar ta fara saranda nan da nan ta silale ta
tsaya a saitin hanyar kauyen su RALIYA" wasu
matan fulani su hudu sun dauko koren nonon
suna ta sauri sun kama hanyar kauyen" A kusa
dasu kuma wani saurayi ne ya tasa manyan
shanun huda a gaba sun dawo daga aiki duk ya
jike da raba a kafafuwan wandonshi da ya yage" raliya tayi ajiyar xuciya domin kuwa taga gida"
tayi sauri ta fita daga motar bayan yaron ya bude
kofar" ya nufi bayan motar cikin sauri domin ya
bude ya dauko mata akwatinta
Jarmai ya cewa raliya "sai anjima 'yan mata" idan kin ga suri kice ina
gaisheta"
RALIYA tayi banxa dashi domin kuwa ta tsaneshi
duk ta kosa dama ta sauka su rabu" yaron motar
ya ajiye mata akwatin a kasa" ya rufe bayan
motar ya dawo a guje ya shiga direban ya ja
motar suka tafi"
yaron motar ya daburce bai san akwatin da ya
ciro ba a cikin kwatinan biyu" domin kuwa irinsu
daya" wannan ba matsalarshi bace" yace a
xuciyarshi sannan yaci gaba da gyangyadin shi
motar tana ta sheka gudu
RALIYA ta gyara lullubinta da tsohon gyalenta"
sannan ta dauki akwatin domin ta kama hanya ta nufi kauyensu" to amma kuma ga mamakinta sai
taji akwatin yayi mata nauyi jigim!
Sai kace an xuba mata duwatsu a ciki" ta
yunkura dakyar ta raba akwatin da kasa" sannan
ta fara tafiya dashi batayi nisa ba ta tsaya domin
ta huta" me ya sami akwatinta kuma?"
RALITA ta tambayi kanta" to amma kuma
watakila laifinta ne domin kuwa yunwa take ji
bata karya ba ta fito daga makaranta" gashi
yanxu daukar akwati xai gagareta"
RALIYA tayi murmushi tace a xuciyarta"Dana sani
dana tsaya na karya domin kuwa suri ta gama
abinci" to amma kuma ta kosa ta dawo gida taga masoyinta rufa'i
RALIYA tana kan tafiya ne da kyar dauke da
akwati" sai ga wani mutum makwabcinsu mai
suna malam Dan kano" ya taho da amalanken
shanu yana turata da hannunshi" ya cewa
raliya "yan makaranta an dawo ne?" Raliya ta...
#sharfadi.com
Tags
# Raliya
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
Raliya
Category:
Raliya