RALIYA-08
.
Matan suka watsar da kullin kayayyakin su
daya kakkaura ce mai kiba" daya
kuma doguwa ce dakayar take iya tafiya" to amma kuma da
sukaji burarin yana kara matsowa
kusa dasu" nan
da nan suka xage dantse doguwar ta
wuce
kakkaurar tayi mata nisa" ita kuma
kakkaurar
tana biye da ita tana salati" domin
kuwa sun
gama tsinkewa mutuwa ce ta zo
.
Suna cikin gudu suna numfashi sai
suka ci karo
da wasu mata su uku dauke da
tuluna" sun debo
ruwa a wata rijiya" matan suka tsaya
tambayarsu
a tsorace" ganin tsofaffin sun wuce
su a guje
kamar iska suna haki sai matan suka
ajijjiye
tulunansu suka rufawa tsofaffin baya"
wadanda
aka tserewa sunata ihu suna cewa a
jira su"
A dai dai lokacin ne wani dan koli
dake bin
kauyuka da keken shi yana tallar 'yan
kunne da
sarka ya shawo kwana da tsohon
keken shi" ba zato da tsammani sai yaci karo da mata ridi-ridi
su biyar suna cin gudu" dan kolin
yayi iyakar
kokarin shi domin ya tsayar da keken
amma yaki
tsayawa" gashi kuma ya jiyo karar
wani abu
shima kamar jirgin kasa ya biyo
matan" nan da
nan yayi tsalle ya jefar da keken yabi
matan a
baya yana nannade malum-malum
dinshi data dabaibayeshi a kafa
.
Mata biyar da Dan koli suka keto
kauyen
danmarke a guje kamar sunga
mutuwa" wani
mutum da ake cewa tsalha mai jaki"
ya hawo
wani tsohon jakinshi mai shegen
gardama" ganin
mutane suna cin gudu" sai ya kada
kan jakin
domin su koma gida" amma kuma
jakin ya ruga
guje" ya tunkari inda burarin nan ke
tasowa"
wanda ba'a san ko menene ba" ganin
haka sai
yayi tsalle ya sauka daga kan jakin ya
dawo baya
ya rufawa matan baya suka yi cikin
gari raf! Raf!! A guje
Bayan sun kai bakin dandalin garin
ne sai suka ji shiru rugugin ya wuce" tsofaffin biyu suka fara
tsayawa suka dafa bangon wani gida"
suna share zufa" matan dake biye dasu da dan
koli da kuma tsalha mai jaki suka cimmasu"
kakkaurar tsohuwar ta dubi ragowar abokan
tseren tace dasu"
"Sannun mu jama'a barka da arziki
Dan koli yace"
"Lallai Allah ya auna mana arziki
sannunmu"
malam tsalha ashe haka wannan
al'amari yafaru"
Malam tsalha ya mikawa dan kolin
hannu suka gaisa"
ragowar matan uku masu tuluna suka
fara yiwa juna jaje
Matan makeri sannunmu da tsira"
wata a cikinsu tace
"Barka dai matar mai unguwa
sannunku"
"wannan bala'i dame yayi kama a
duniya?"
tsalha mai jaki ya cewa dan koli"
"wai me ya faru ne dan koli ni nayi
tsammanin
harin da akace jaji bush zai kawo
shine suka
jeho mana nakiya anan kauyen" jiya
matata taji
ana fadi a rediyo?
Dan koli ya share zufa yace da
malam tsalha"
"Eh, to nidai na taho naga wadannan
mata suna
gudu" ina jin maganar dai kenan koba
haka akayi ba?
Ya tambayi matan biyar" matan makeri
tace"
muma dai mun debo ruwa ne" muka
ci karo da
wadannan tsofaffi suna gudu" mun
tambayesu ko
lafiya basu ce mana komai ba" shine
muka biyo
bayansu
Dan koli ya bata rai yace"
Zancen banza kenan" kawai kuma
daga ganin
mutane suna gudu sai ku kama yi" to
ku baba me kuke yiwa gudu?"
Doguwar tsohuwar tace"
"mu baki ne muna tafiya ne zamuje
kauyen
kwananduke" daga magaji wando
muke" shine sai
muka ji karar wani abu kamar na
jirgin sama zai
fado" to munji labarin abinda ya faru a
birni kwanan nan shine mukayi ta kanmu"
.
Malam tsalha yayi tsaki yace da
tsofaffin"
"Amma wallahi kun cucemu tsohuwa"
haka kawai
daga kunji karar wani abu sai ku
kama gudu"
Yanzu haka ma babur din yaron can
NAZIRU dan gidan mai kiran sallah kuka ji"
Dan koli yace"
"shine mana!! Kawai kunja mana
tashin hankali
muna gudun banza ni banma san
inda na ajiye keken kayana ba"
Ya wuce gaba yana zage-zage" afusace ya koma
inda ya baro kekenshi" malam tsalha
yabi
bayanshi yana share zufa" yana ta
tsaki domin
kuwa matan sun gama bata mashi rai"
Matar mai unguwa ta shiga gaba suna
ta fada
domin su koma su dauki tulunansu"
"wannan sakarcin ma dame yayi kama
a duniya"
indai lalatar Naziru ne wanene bai
saba dashi ba
a wannan kauyen" haka yake tada
wannan babur
din ya tsorata mana yara" kuma kawai
ku da
girmanku sai ku kama cin gudu?"
Kakkaurar tsohuwar tace a fusace
"to mu ina xamu sani tunda mu baki
ne?" kawai
muna cikin tafiya malam" sai muka ji
abu ya taho
rugu-rugu ba arxiki" ina xamu tsaya
kawai-kawai ya cim mana?
matan suka yi ayari suka koma suna
ta musayar
maganganu" malam tsalha mai jaki
bai waiwayi
inda jakinshi yake ba" da xuwanshi
saiya shige
cikin gida" domin kuwa ranshi ya riga ya baci"
Duk lokacin da ranshi ya baci haka
kawai sai yaji
yana jin gudawa ya shiga cikin gidan
a fusace
yana ta xupa" matanshi suka fara
tambayarshi
abinda ya faru" ko daga kai baiyi ya
kallesu ba"
yayi sauri ya wawuri buta ya fada
bayi" da
shigarshi ya turo kofar ta rufe a
fusace"
.
=====>******^*******<======
.
NAZIRU ya shiga cikin gidansu" yana
gangara
babur dinsa" da shigarshi ya hango
kanwarshi
Raliya ta dawo tana xaune a kasa da
kakarsu tare
naziru ya jingine akwalar babur dinshi" sannan
ya nufi wajen kakarsu da kuma Raliya yana
fara'a "yan makaranta yaushe aka dawo ne?"
Raliya tace dashi
"tun daxun na dawo yaya Naziru" ina ka shiga
ne?"
Naziru yace da ita yana shafa tarin sumarshi"
"Na dan fita nan bayan gari ne" yaya karatun
naku Raliya?"
"kafin tabashi amsa ne kakarsu tace dashi"
"An fita yin sana'ar da aka sabo ko?" ai kai dai
wallahi Naziru har abada baxaka rika jin magana ba"
Naziru yayi saurin canxa hirar domin kuwa
yasan halin kakarsu idan ta fara yi mashi
bambami sai ta wuni bata gaji ba"
"Raliya ina fatan dai a wannan karon kin cika
min alkawarina" tuntuni nasha tuna miki idan xaki
dawo ki sayo mani tabarau irin mai dan fadin
nan" irin na SHEGEN SAMA abokina"
Raliya tayi murmushi"
"Ban mance ba yaya Naziru" tace dashi sannan
takai ganinta inda ta jepar da akwatinta tun
dawowarta anan ta sake shi a tsakar gida"
'ya'yan awakai suna ta hawa kai suna tsalle bata
damu ba" domin kuwa tasan cewar ba wata tsiya
ke a ciki ba" daya wuce tsummokara da littatafan
karatunta" yaunxun nan da xarar ta gama hutawa
dama take so ta amshi kudi a wajen mahaifiyasu
taje ta sawo omo tayi sukola
Raliya ta cewa yayanta Naziru
Yana cikin akwati ka bari sai anjima idan na bude
sai in baka yanxun nan xan tashi" dama in ciro
kayana wanki xanyi"
Naziru ya bata rai yace da ita"
"sauri nake yi tashi ki bani yanxu Raliya" wajen
abokina zan tafi Shegen Sama yana can gida
yana jirana"
kakarsu dake sauraronshi tace"
"kadai xama sangwamemen katon banxa Naziru"
ace kai ba xaka tsinanawa kanwarka komai a
duniya ba" sai dai ita ta samu ta baka kaji kunya kayi girman kwabo"
naziru yayi dariya ya cewa kakarsu"
"In banda abinki kaka menene to don taxo mini
da tsaraba" Daga birni fa take" tinda mu muna
nan a kauye" ai yakamata ace ta danyo mana
siyayyar birni" nima idan aurenta da rufa'i ya
tashi ai dole ne inyi mata
Raliya taji farin ciki ya lullubeta" data ji Naziru
ya ambaci sunan masoyinta Rufa"i da shigowar
ta ta aiki wani yaro domin gidan su domin a
sanar dashi cewar ta dawo" amma kuma taci
rashin sa'a Rufa"i ya tafi gona tunda safe sai ya
dawo " Anjima nan zaizo ya sameta su raba dare
suna hirar yaushe gamo"
Raliya ta tashi cikin tsananin farin ciki domin ta
dauko wa Naziru tabaronshi data sawo mishi a
kano" ta ciro dan makullin akwatin ta kori
awakan dake xaune akai ta daga akwatin tsaye
ta fara kicin kicin budewa" Raliya ta dage tana
dama da akwatin ya budu amma kuma yayi gam
yaki budewa"
wannan abu ya bata mamaki" daxun nan tahi
akwatin ya kara nauyi data sauko a mota" yanxu
kuma gashi ya kulle tayi-tayi ya bude yaki
budewa" anya kuwa wannan akwatin shine nata?
Raliya ta tambayi kanta cikin fushi" Naziru dake
a tsaye yana jiranta ta bude ta ciro mishi
tabaronshi yace da ita"
"kawo mabudin mu gani don Allah" sai kace wani aiki?"
Raliya ta mika mashi mabudin yayi nashi kokarin
amma akwatin yake buduwa" kakarsu dake xaune
tana yagar rama tace"
"to wai dole sai an bude" a hankura mana sai an
huta xuwa anjima" wannan naci har ina?" bana
son kana takurawa yarinyar nan Naziru" kai baka
san ka girma ba wallahi"
Naziru ya hauri akwatin cikin fushi da
gwandolarshi"
"Duk bukulunka saina sai tabarau yau akwati"
yace yana xaro idanuwa" sannan ya dauki
akwatin da hannu daya yace da Raliya"
"Kada ki dama Raliya bari inje dashi wurin
abokina Shegen Sama yana da karfen bude
kwatuna" idan ya bude kwadon sai in dawo miki
dashi ki ciro ki bani"
Raliya tace dashi"
"ba komai yaya Naziru kaje dashi ku bude"
Naziru yayi waje da akwatin kakarsu tace"
"wannan masifar naci naka Allah ya rabamu da
irinshi"
Naziru ya fito daga cikin gidansu" Abokinshi
Shegen Sama wanda suke takadarcinsu tare"
kamar Naziru dashi a gidansu" su biyu ne dama
suka gagari kowa a kauyen danmarke"
to amma kuma har dama-dama Shegen sama
shi ance yana xuwa gona idan ta raya mashi" to
sai dai kuma ko sati daya ba ayi ba daga kawai
mahaifinsh yace ya daina kawo mishi tuwo tunda
bayason xuwa aiki" kishiyar mahaifiyarshi ce keda
aiki" data gama abinci bata sa mishi ba" saida ya
bari babanshi ya fita masallaci ya fada cikin
dakinta" yayi mata dukan tsiya da bel" tsawon
lokacin mahaifinshi yayi yana tsine mashi
albarka"
Naziru ya sami shegen sama a xaune akan
gungume a kofar gidansu yana hamma" shegen
sama gajere mai fadin kirji kamar kofar gareji"
yana da murgujejen kai da kuma faskeken tafin
hannu kamar faranti" yana sanye da kodaddun
kaya irin dan madina" wanda ya zazzare ya koma kamar kyallen tatar koko
Naziru ya kunduma mashi zagi tun kafin ya
karasa wajen shegen sama.
.
ZANSO KUYI HANKURI SHAFIN DA NA SHIGO
YANA DA MATSALA" BANA GANE RUBUTUN"
AMMA SHAFI DAYA NE KAWAI"
.
Ayarin 'yan sandan da suka kamo jarmai suka ci birki a daidai ofishin ACP Aminu jangwarxo"
tsayawarsu keda wuya suka fito dashi nannade
da ankwa a hannayenshi tare da murgujejen
akwatin kudin...
Tags
# Raliya
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
Raliya
Category:
Raliya