Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

RALIYA 11

RALIYA-11
.
Raliya Tana kan tafiya ne ta hango wasu dattawan mutane biyu sanye da bakaken kaya a jikin wata
bakar mota fijo" sun kura mata idanu" suna ta
kallonta tun daga nesa" akwai wani yanayi dake
tattare da mutanen wanda bai kwantawa suri Arai ba" tazo daidai inda suke zata sabasu ta wuce" sai taji wani mutum ya daga murya yace da ita" "ke muke zaman jira anan suri"
.
Suri taja birki ta tsaya a tsorace ta sake duban
mutanen sai a lokacin ne ta fahimci kayan
jami'an tsaro ke jikinsu" suri taji gabanta ya fadi
tayi sauri taja baya
Me zanyi muku malamai...... Me kuke nema a
wurina?" Wanda yayi magana da farko ya sake cewa da ita a tsanake"
"wasu bayanai muke nema a wurinki acan
ofishinmu" shigo cikin mota mu tafi" ba abinda
Zai sameki 'yan mata"
Suri ta sake ja da baya zata yi tirjiya ta ruga da
gudu" sai ta dubi hannun daya tsohon jami'in
tsaron taga yana rike da guntuwar bindiga
saitinta" ta dubi fuskokinsu taga babu alamar
wasa ko yaudara" mai rike da bindigar yace da
ita "kina iya guduwa idan kina bukatar yin hakan" to
amma kada ki zargeni idan kikaji harsashin
bindiga ya karairaya kafafuwanki 'yan mata"
Nan da nan mara bindiga ya bude kofar motar yashiga ya zauna akan kujerar direban" wanda ke rike da bindigar ya bude kofar baya na motar" ya
yiwa suri murmushi sannan yace da ita"
"zaki iya shigowa yanzu 'yan mata sunana Aminu Jangwarzo" wannan abokin aikina ne bilya" mu dukanmu jami'an tsaro ne" idan kika bamu hadin
kai ba abinda zai sameki" amma idan kika bamu wahala wajen binciken da zamu yi maki" ina
faragabar sanar dake koke kanki bazaki gane
kanki ba nan da wani dan lokaci mai zuwa"
Suri ta fashe da kuka" tayi saurin rufe bakinta
ganin har yanzu mutumin bai dauke bindigarshi
daga saitin inda take a tsaye ba" suri ta taho a
tsorace kamar kwai ya fashe mata a ciki" ta shiga
cikin motar" jami'in tsaron yabi bayanta cikin
sauri sannan ya rufe kofar" direban yaci taya
suka fice daga harabar makarantar" suka doshi
hanyar ficewa daga babbar kofar da suke
fuskanta"
Wadansu yara dake gara taya a kusa da wajen
suka dagawa motar hannu" lokacin da ta wuce
kamar kibiya" a karo na farko direban motar yayi murmushi tun zuwansu makarantar neman suri" sannan ya dagawa yaran hannu"
Lokacin da su bilya da Aminu jangwarzo suka kai suri gidan tuhuma na sirri" C-P Dan masani yana ciki yana jiransu" a cikin gidan ne suka kulle Jarmai a wani faffadan daki mai duhu wanda ke cike da kyankyasai da kuma zarnin fitsari da masu laifi da ake kawowa a kulle su a ciki suyi sati ba'a waiwayesu ba"
Sau da yawa idan ba irin wannan bincike na sirri ya taso ba" ba kasafai ake kawo mai laifi wannan kebentaccen gida ba da kwamishina ya ware domin wasu bukatunshi na musamman" tun dazun yana nan a cikin gidan" tun lokacin da su bilya suka tafi jami'a domin nemo Raliya ko kawarta Suri bayan sun tafi ne ya shiga cikin dakin da aka kulle Jarmai ya sameshi a nannade da ankwa hannu da kafa" yayi iyakar kokarinshi wajen ganawa Jarmai azaba iri iri domi ya fada masa inda ya boye jakar kudin da suke nema"
Amma kuma Jarmai ba abinda yake iya fadi sai dai bai sani ba"
Danmasani bai rabu dashi ba saida yaga ya suma" sannan ya fito daga cikin dakin yana huci idanunshi sunyi jawur kamar gauta"
Lokacin da su ACP bilya suke fito daga cikin mota suka iza kyeyar suri zuwa cikin gidan" Dan masani yana tsaye a bakin dogayen dakunan tuhumar inda Jarmai yake" suri taji gabanta ya fadi" ta sake tsurewa a lokacin da taci karo da kwamishina " yanayin fuskarshi kawai ya isheta fahimtar azabar dake yi mata lale marhabin a cikin gidan"
Tun kafin su gabatar da ita" kwamishina ya daka mata tsawa a fusace" "Ke.... Ina kawarki Raliya? Suri ta firgice ta fara in-ina cikin tsananin kaduwa"
"Raliya?" ban san....... Ta koma garinsu" Wallahi bata nan ta koma gida"


kwamishina Danmasani ya harareta" yakai hannu ya cakumo kwalar rigarta da hannu daya" ya dagata sama kamar 'yar tsana sannan ya wanke ta da mari tas!! Sai da kuncinta ya tsage kamar an yanka ta da reza"
Suri ta fasa kururuwa iyakar karfinta" kwamishinan 'yan sanda ya jefar da ita kamar totuwar masara ta hadu da bangon dakunan tuhumar nan take ta watse a kasa"
ya matsa kusa da inda take a kwance tana juye-juyen mutuwa" jini ya wanke 'yar matsakaiciyar fuskarta" ya duka yace da ita a sanyaye
Ba kasheki zamuyi ba" ballantana ki huta" zamuci gaba da karairayaki ne har sai kin koma tsumma" ki fada mana gaskiyar abinda muka tambayeki" ina kawarki Raliya ta tafi?"
Suri ta bude baki dakyar jini yana zuba tace dashi "ta koma gida dazu da sassafe" ta koma garinsu
kwamishina ya zare idanu yace
ina ne garinsu" a ina yake?"
Suri ta yunkura ta matsa baya kadan a tsorace tace" "Dan marke ne garinsu" wani kauye ne Dan marke acan take"
Kwamishina ya daka mata tsawa"
Me taje yi ana tsakiyar karatu" kuma yaushe zata dawo! suri tace "ta koma ne domin ayi mata aure" tace bazata iya ci gaba da karatu ba" tana da wani masoyi da take so sunanshi" RUFA'I tace donshi zata bar karatu" domin yace bazaici gaba da jiranta ba" zai auri wata budurwa.
Kwamishina ya daka mata tsawa saida hanjin cikinta ya motsa"
"Dame ta tafi lokacin da zata bar makarantar" baki ganta da wani akwatin kudi ba?
Suri ta girgiza kanta a tsorace"
"wallahi ban ganta da akwatin kudi ba" da akwatin kayanta ta tafi wanda take zuwa dashi ko yaushe" Raliya bata da kudi ni na bata kudin motar komawa gida"


kwamishina ya mike tsaye yana mayar da numfashi ya dubi mukarrabanshi biyu dake tsaye suna kallon yadda yake tuhumar 'yar budurwar" fuskokinsu sunyi sharkaf da zufa sun koma kamar dodanni" yace dasu a fusace
"ku hada ta da waccan ku kulle mana su" zasuyi mana amfani nan gaba kadan"
tun kafin su rufe baki Aminu jangwarzo yayi sauri ya taho yasa hannu daya ya cafi gashin kan suri dake a hargiste a waje kamar shekar ungulu" ya mikar da ita tsaye" sannan ya jata zuwa dakin da Jarmai yake tana binshi da digirgire tana kukan azaba"
Da zuwanshi yasa kafa ya haure kofar dakin ta bude" bai shiga ciki ba" kafin kofar ta sake dawowa ta kulle ne ya jefa suri cikin dakin kanta ya hadu da siminti kofar ta rufe lokaci guda" duk da haka sai da ya jiyo sautin kuwwar suri daga can ciki" sannan sai yaji tsit"
Yayi murmushin mugunta" sannan ya dawo ya sami kwamishinan 'yan sanda ya sara mashi cikin girmamawa" kwamishinan yace dasu
"Ba zama zakuyi ba" kuyi hanzari ku dauki mota ku nufi kauyen dan marke" tu tabbatar kun kamo min Raliya" da ita da masoyinta duk muna bukatarsu" idan kuma kunga akwai matsala to kuna iya kamo min masoyin nata shi kadai" idan tana kaunarshi dole ne ta fito mana da kudinmu" inda kuma tafi son kudin dashi" sai ku amso likkafani a warinta ku bar mata kudin
Kwamishinan 'yan sanda ya sake murtuke fuska sannan yace a fusace
"zamu amshi likkafanin ne a matsayin gudumawarta na jana'izar masoyinta rufa'i