Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

RALIYA 12

RALIYA-12
.
Ba karamin kokari kwamishinan yan sanda yayi wajen tuko motar shi ya dawo ofishinsa ba daga gidan tuhumar" yayi wannan tafiyar shi kadai babu 'yan rakiya ne da direbanshi" domin baya so kowa yasan abinda yake faruwa" wannan wani sirri ne da ya shafeshi dashi da mataimakanshi" sudin ma da zarar kudin sun zo hannu zai aika dasu barzahu daga nan babu sauran matsala miliyan hamsin dalolin amurka sun zama nashi
A karo na farko kwamishina ya dan saki ranshi" sannan kuma yayi ajiyar zuciya a lokaci guda ya fara lissafin yawan kudin idan aka canza su suka koma kudinmu na gida nigeriya" hakika miliyoyin nairori suna da yawa" kwamishina yasan cewar sun isheshi yayi duk abinda yake so a duniya har iyakar rayuwarshi" ya huta da wadannan bakaken kaya dake manne a jikinshi dare da rana kamar cingam shekara da shekaru"
Jami'an tsaro manya da kanana sukayi ta bushewa a tsaye cikin girmamawa a lokacin" ya shigo cikin katafaren cibiyar jami'an tsaron inda ofishinsa yake" bayan ya ajiye motarshi ne saiya fito ya nufi ofishinsa" a lokacin ne sakatariyarshi ta sanar dashi cewar yayi wani muhimmin bako" yana ciki a zaune yana jiranshi"
Bako?" kwamishina ya tambayi kanshi cikin damuwa" wanne bako ne kuma yazo yana son ganinshi a daidai wannan lokaci?" yayi tsaki sannan ya shiga cikin ofishin domin kuwa yana bukatar hutawa a halin yanzun bazai yi farin cikin zuwan wani bako ba
A lokacin da ya shigane ya sameshi a zaune" yasha sabuwar shadda fara da riga malum-malum da kuma farar hula" yana rike da jarida yana karantawa to amma kuma duk da wannan shiga da bakon yayi ta limamai" kwamishina yasan cewar ko shakka babu wannan bako bashi da bambanci da ganin bakin maciji
"Meya kawoka ofishina....?"
kwamishina ya tambayeshi a fusace" domin kuwa ya mance da wannan shu'umin mutum a cikin mutanen da zai kashe domin ya samu damar mallakar wadannan miliyoyin kudi" tabbas shima wannan dole ne yabi sahun su Bilya zuwa barzahu
Tunanin kwamishinan 'yan sanda ya katse a lokacin da mutumin yayi murmushi sannan ya tattare jaridar ya ajiyeta a gefe guda" ya dawo da hankalinshi kan kwamishina yace dashi
"Nazo ne domin ka bani kudina dala milyan hamsin" daka amsa a wurin jarmai"
"Na sami labarin ka tura yaranka sun kamoshi da akwatin kudin" nayi tsammanin zaka biyoni har gida ka kawomin kudina" domin kuwa ladan da nayi alkawarin zan baka yana da yawa" nan take nazo da kaina yanzu yi sauri ka dauko min kudina in baka ladanka kwamishina"
Alhaji Elbashir ya daka mashi tsawa cikin fushi
kwamishinan 'yan sanda yaji wasu tabare irin na daka sakwara suna rubdugu a cikin zuciyarshi" ciwonshi ne ya tashi na hawan jini"
.
=====>*******^******<======
:
Babu abinda yafi burge kananan yaran kauyen dan marke irin ace yamma tayi" babu hadari a sararin samaniya" wannan yanayi yana matukar basu kwarin gwiwar fitowa da dokunansu na kara suna hawan salla" suna zagaye gidanjen kauyen da gudu suna wake wake"
Haka abin ya faru a wannan yammaci" tun lokacin da yamma tayi sakaliya" suka ga sararin samaniya ya kori kananan giza-gizan da suka fara neman wurin zama" sai suka firfito daga gidajensu" da zarar sun daga kansu sama zasu ga farin watan dake zaune a gabar ya fito tarwai" yana jiran rana ta gama nata zamanin" in dare yayi shi kuma yazo ya dare kan gadon mulkin kwararar da Haske da iznin Ubangijin Al'arshi mai buwaya da hikima"
Bayan kananan yaran dake ta gudu a cikin kauyen" tsuntsaye suma ba'a barsu a baya ba" suna ta shawagi suna gasar tsere da zilliya" kurciyoyi suna ta kuka a saman bishiyoyin dake cikin gidajen mutane" yawancinsu suna kwancin sabuwar kyankyansar da sukayi ne" basu da damar fitowa saboda sun san karambanin dan adam da rashin tausayi" da zarar sun tashi sun bar jariransu yara zasu sa kara su zunguro shekarsu ta fado kasa"
Don haka kurciyoyin sun gwammace su zauna a cikin duhun reshikan bishiyoyi suna rera wakokin yabo da gamsuwa ga wannan yanayi mai tsananin dadi da jefawa zuciya Annashuwa"
Kamshin damina da kuma kamshin tukwanen miya ya gauraye ko ina a cikin kauyen dan marke" sannan kuma sautin bugun makerar dake tasowa da wani makeri yake yi a kowacce rana ta duniya" ya taimakawa mazauna kauyen wajen debe kewa"
samari sunyi sansani a wani dandali da ake yanka rake da kuma rumfar sayar da shayi"
wadansu kuma sun fito da rikoda a hannu" sun sa wakar fina finan hausa" suna sauraro" sannan kuma suna ta faman gardama da jayayya a tsakanin kamfanonin shirya fina-finain Hausa da suka fi yin kyawawan wasanni da kuma jaruman da sukafi iyawa" da kuma taurarin 'yan mata da suka fi kyau da burge 'yan kallo"
Wadannan abubuwan nishadi suna faruwa ne akan idon Raliya da masoyinta Rufa'i suna tsaye jikin wata akuri-kura wacce mahaifin Raliya wato malam muntari ya taba tukawa tun kafin a haifi yayanta Naziru duk tsawon wadannan shekaru motar tana nan wurin ta zama mushe amma kuma kwarangwal dinta da yayi saura yana matukar taimakawa wadannan masoya biyu Raliya da Rufa'i suna samun abin jingina
Sun dauki lokaci mai tsawo a jikin akori kurar suna ta hirarsu ta soyayya Raliya ta fuskanci masoyinta Rufa'i yana nan kamar yadda yake a zuciyarta" farin saurayin mai yawan fara'a wanda baya iya rabuwa da hula a kowanne lokaci koda barci yake yi tun lokacin da suka fara hirar Rufa'i baya wata magana saita aurensu" ya dubi Raliya ya sake tambayarta a karo na uku"
Wai da gaske ki keyi bazaki sake komawa makaranta ba Raliya?
Raliya tayi murmushi zata bashi amsa kenan saita hangi babanta malam muntari ya fito daga cikin gida" yana rike da karamar fartanya da wani irin kubewa a leda zaije bayan gida ya shuka" bayan ya wuce sai tace da Rufa'i
"Kasan cewar bazan yi maka wasa da irin wannan maganar ba Rufa'i gaskiya nake fada maka" dama can mahaifina ya bani zabi da dadewa yace duk lokacin da na gaji da karatu naji ina son aure in fada mishi domin baya son ya takurawa rayuwata har inzo in shiga wani hali
Rufa'i ya lumshe idanunshi cikin jin dadi yace"
Allah mun gode maka daka nuna mana wannan lokaci"
Na dade ina jiran zuwan wannan lokaci raliya"
sukayi dariya abin gwanin ban sha'awa suna nan suna hira har rana ta fadi mutane suka fara dawowa gida suna daukar butocin alwala
Rufa'i yace da Raliya
"lokacin sallah yayi zan tafi gida Raliya" sai anjima bayan anyi sallah zan sake dawowa"
Raliya ta dan bata rai tace dashi"
"saura kuma ka bata lokaci kabar ni ina ta zaman jiranka
Rufa'i yace da ita cikin farin ciki"
"Haba Raliya ai kema kinsan bazan dade ba" yau ma anan saikin gaji da ganina"
sukayi bankwana Rufa'i ya nufi gidansu dake can bayan gari Raliya ta rabe a kofar zaurensu tana hangenshi har ya bace" sannan tayi murmushi ta shige cikin gida
Rufa'i ya karasa kofar gidansu yana tunanin wannan masoyiya tashi wacce ya dauki shekaru fiye da goma yana kaunarta" baya fatan wani abu da zai rabashi da Raliya rabin ranshi
to amma kuma aski yazo karshe komai me zuwane da wucewa yayi hakurin jiranta tsawon lokaci" gashi yanzu lokacin da yake jira yazo tunda rufa'i yake a duniya bai taba jin tsananin farin ciki irin na wannan ranar ba
.
A lokacin da yake kokarin sa kai da ya shiga cikin gidansu kenan sai yaji an kwala mishi kira daga baya
Rufa'i ya waigo cikin sauri" ya hango wasu mutane biyu suna ta sauri sun nufo zuwa inda yake" daga can bayansu wata mota ce baka irin ta ma'aikatan gwamnati Rufa'i yaji gabanshi ya fadi domin kuwa ya fahimci mutanen dake kiranshi" sannan ya tsaya jiransu har zuwa lokacin da suka cimmishi
suna sanye da bakaken kaya iri daya" da hulunan 'yan sanda" akwai wani yanayi dake tattare dasu wanda Rufa'i bai amince dashi ba" wani mai katuwar murya a cikinsu yace dashi
"Baka ganemu ba ko rufa'i ?
Rufa'i ya girgiza kai cikin kokwanto"
Dayan yace dashi"
"Dole ne ka mance damu amma a shekarun baya munsha zuwa nan wurin mahaifinka" yana nan a cikin gida ne?
Rufa'i yace dasu cikin ladabi
"Baku ga fitowarshi ba?" yanzun nan na hadu dashi a hanya zai tafi masallaci
"mai katuwar muryar yace"
"yanzun nan muka zo" Dan Allah zoka taimaka mana mu turo motarmu mu karaso da ita" sai da tazo daidai can ta tsaya muna tsammanin mai ne ya kare
Rufa'i yace dasu cikin tausayawa"
"sharrin karfe kenan" muje in taimaka muku"
Rufa'i yabi bakin mutanen a baya masu kama da yan sanda suka bar cikin gari suka je can inda motar take a baya daidai wata gonar waken suya da dawa" da zuwansu daya daga cikin mutanen ya shiga cikin motar wurin zaman direba
Rufa'i ya zagaya bayan motar tare da daya mutumin wanda ya biyo ta bayanshi" Rufa'i zai dafa motar kenan" sai yaji wani abu mai kama da busasshen karfe ya mareshi a fuska" nan da nan fararen taurari suka rufe mishi idanu" kafin yayi kuwwa ne domin a kawo mashi agaji sai ya sake jin irin abinda ya mareshi" ya sake sauka akan kwakwalwar kanshi
tun daga nan bai sake jin komai ba" sai daga baya ne yaji an ciccibeshi an sakashi a cikin motar sannan an tayar da motar an bata wuta an fara tukawa" ba'a jima ba yaji mai katuwar muryar yana cewa
"ka tabbatar ya suma Bilya?" bana son mu sami matsala a hanya
Daya mutumin yace a fusace
"wannan yazo hannu ba matsala tuka kawai mu tafi jangwarzo"
Har motar ta yi nisa Rufa'i bai san inda kanshi yake ba"
Abu na karshe dayaji kafin ya suma shine sautin kiran sallar magariba da mahaifin Raliya ya kwada daga can nesa a cikin lasifika"
Ga mamakinshi sai yaji duk da ya kusa mutuwa yana so ya sake ganin Raliya 'yar makaranta masoyiyar sa