Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

RALIYA 13

RALIYA-13
.
Abu na karshe dayaji kafin ya suma shine sautin kiran sallar magariba da mahaifin Raliya ya kwada daga can nesa a cikin lasifika"
Ga mamakinshi sai yaji duk da ya kusa mutuwa yana so ya sake ganin Raliya 'yar makaranta masoyiyar sa
.
"Ka fito mun da akwatin kudina kaji ko" sauri nake yi kwamishina" bana so kana bata min lokaci Alhaji Elbashir ya sake dakawa kwamishinan 'yan sanda tsawa" akaro na biyu"
kwamishina danmasani ya dafe kirjinshi domin kuwa bayan tabaren dake yi mashi lugude a ciki" har wani abu kuma mai tsini kamar mashi yaji yana sukar hakarkarinshi
Ya zauna akan katafaren teburinshi domin ya samu sauki" ya dubi shu'umin mutumin cikin damuwa"
Ba banza ta saka kwamishinan 'yan sanda ya tsorata da Alhaji Elbashir ba" akwai kwakkwaran dalili
Alhaji Elbashir yana daya daga cikin manyan 'yan siyasar kasar Nigeria wadanda suke nada gwamnoni da 'yan majalisu kamar sarakuna" suna sayen kowacce irin kujera a ciki kuwa har da ta kwamishinan 'yan sanda" idan bukatar hakan ta taso"
yasan cewar idan yabi Elbashir da tsiya to dole ne asirinshi ya tonu" bazai yayata maganar duniya taji ba" domin kuwa shima bazai so asirinshi ta tonu ba" to amma yana da karfin ikon da zai sauke kwamishina ayi mashi ritaya da tsiya ko yana so ko baya so"
Don haka ya zamewa kwamishinan 'yan sanda wajibi ya san hanyar da zaibi ya kawar da Alhaji Elbashir cikin hikima" ba tare da wani yasan abinda yake faruwa ba" kwamishina yayi kasa-kasa da muryarshi yace dashi
"An sami matsala Alhaji" kudi basu zo hannu ba
Elbashir ya gyara zama yana kallon kwamishinan 'yan sanda a tsanake kamar mai bitar darasi" zuwa can ya ce dashi
"ban faminci abinda kake nufi ba" da an sami matsala kwamishina?
Dan masani yayi ajiyar zuciya sannan yace
"Hakika mun kamo Jarmai to amma kuma akwatin da muka samu a wurinshi babu kudi a ciki" muna tsammanin ya canza akwatin ne domin yaudararmu
Elbashir yayi shiru babu wani alamar tsorata ko damuwa akan fuskarshi" idan wani ya ganshi sai ya rantse da Allah an sanar dashi labarin bacewar kwandala hamsin ne ba miliyan hamsin ba" wannan yanayi na rashin damuwa dake tattare da Elbashir ya sake rikita kwamishina domin kuwa yasa cewar akwai matakan da yake so ne ya dauka da gaggawa"
Yanzu ina Jarmai din da kuka kamo" ina son ganinshi akwai maganar da nakeso muyi ni da shi Elbashir ya sanarwa kwamishina" wanda ya ciro kyalle yana goge fuskarshi dake kama da kaskon tuyar awara" bayan ya gama goge fuskar sai yace dashi cikin damuwa"
Yaranmu sunyi sakaci sun barshi ya gudu bayan sun kamoshi" amma na bazasu nace su tabbatar sun sake kamo mana shi
Alhaji Elbashir ya sake yin shiru yana nazarin daddumar dake malale a ofishin zuwa can kamar zaice wani abu sai ya dakata" ya mike domin ficewa daga ofishin" har ya fara tafiya " saiya waigo ya dubi kwamishinan 'yan sanda yace dashi cikin kunar rai
Sau da yawa mutane masu hadama irinka sun sha niyyar cutata dan masani" amma kuma har yanzun babu wanda ya taba kai labari" duk wanda ya zalunceni dole ne saina rama" don haka na baka nan da awa biyu ka kawo min kudina" nasan cewar wannan rubabbiyar kwankwalwar taka bata tunanin komai sai shirya maka yadda zaka kwace min miliyoyin kudina
kayi kuskure danmasani" kuma baza kayi nasara ba" mun dade muna wannan bakar huldar dakai shekara da shekaru" wannan kawai ya isheka sanin koni wanene a kasar nan"
Idan awoyi biyu tayi baka kawo min kudin ba" zan fara gudanar da nawa motsin"
Alhaji Elbashir yayi makararren murmushi sannan yace dashi"
"Bana fatan kaga irin motsina" dan masani ka kawo mani kudina
Ya fice daga ofishin a fusace" sannan ya mako kofar ta biyo bayanshi" kwamishinan 'yan sanda yaji numfashinshi yana kokarin tsayawa" yayi saurin bude wata karamar dirowa dake gabanshi ya dauko robar ruwan sanyi yabude ya kafa kai yana kwankwada
.
Lokacin da Alhaji Elbashir ya shiga cikin motar shine dake can waje wacce ke da duhun gilasai" sai ya zage gilasan motar" sannan ya waiga kujerun baya ya dubi ifiritan samarin dake zaune suna wasa da kananan wukake a hannunsu" yace a fusace
"Bai bani kudina ba" bayan awoyi biyu kuci gaba da aikinku" ku tabbatar kunci nasara"
Gambo da abokinshi dumfama suka hada muryoyinsu dake kama da fashewar nakiya sukace "an gama Alhaji
.
=====>******^********<======
.
An kai kusan rabin awa kafin suri ta dawo hayyacinta kanta yayi nauyi gingiringin ko ina a jikinta sai faman zugi yake mata"
ta muskuta daga inda take a kwance a cikin duhu" taji kyankyasai suna bin kafafuwanta" nan da nan tayi sauri ta haura kafafunta ta goge kwarin dake bin jikinta"
A daidai lokacin ne taji numfashin mutum a cikin dakin sannan taji an motsa jiki
Suri taji tsoro ya kamata tayi sauri ta matsa baya ta hadu da bangon dakin ta riga ta gama sakankancewa da rayuwa" a halin yanzu mutuwarta ta fiye mata sauki da wannan azabar da take fuskanta"
Ta fashe da kukan bakin cikin wannan muguwar rayuwa da tasa kanta a ciki"
"na cuci kaina"
tace a sanyaye tana kuka"
Sai yanzu nasihohin da kawarta Raliya keyi mata a makaranta suka fara dawo mata cikin kwakwalwar kanta
Hakika Raliya gaskiya take fada mata" to amma kuma ita tsammaninta Raliya 'yar kauye ce bata waye ba" yanzu kam ta tabbatar rayuwar kawarta tafi tata inganci nesa ba kusa ba"
Domin kuwa tana can a halin yanzu a cikin kwanciyar hankali" a garinsu tare da masoyinta Rufa'i
Me yafi zama lafiya dadi a duniya?
Suri ta tambayi kanta" Hakika zama lafiya yafi zama da kudi ko nawa ne a duniya" komai yawansu" wannan itace shawarar da Raliya tasha fada mata" domin kuwa ba wanda ya isa ya yiwa kansa arziki a duniya komai wayonsa"
Suri tayi tsammanin idan mutum yana da wayo a duniya" dole ne ma ya tara isassun kudi yadda yake so"
sai yanzu data sami kanta a cikin wannan halin sannan ta fahimci samun kudi a duniya ko wata baiwa ba ruwansu da wayon mutum ko kyan jikinshi" Allah shine mai azurta bayinsa aduk inda ya so" kuma ga wanda ya so"
Suri ta sake fashewa da kuka" Hakika Raliya itace wayayyiya" domin kuwa tasan yadda zata zauna lafiya a duniya da mutuncin ta ba tare da wani ya biyota yaci mata mutunci ya wulakantata ba"
Suri tana cikin shishshikar kuka sai taji numfashin dake tasowa a cikin dakin ya sake gawurta wanene?
suri ta tambayi kanta" tace a bayyane"
"wanene a cikin dakin nan?"
sannan ta sake mannewa da bango a tsorace kamar wacce take jin sanyi" tayi matukar kaduwa da amsar da aka bata"
Nine...... Baki ganeni ba ne suri?"
nine masoyinki jarmai?"
"jarmai?" suri ta tambayi mai maganar a tsorace" kai nake ta nema jarmai meya kawoka nan...... Kaima sun kamaka ne?"
Jarmai dake nannade da ankwa a makure a lungu yace da ita
"Rana ta baci suri" mafarkinmu yazo karshe" wannan shine karshen zaren sa'armu"
Suri ta sake daburcewa a tsorace kamar wacce tayi gamo da fatalwa" bata gaskata abubuwan da take saurare ba a cikin duhun" Jarmai ya sake cewa da ita
"kawarki Raliya ta sami sa'a kudin suna can a wajenta ta tafi da kudin kauyensu sai wata rana kuma.."
Suri tayi saurin dakatar da Jarmai"
"A ina kasan Raliya jarmai?" me kake nufi da kudinmu suna wajenta" meya hadaka da Raliya?"
Jarmai ya sanar da suri yadda akayi suka hadu da Raliya a mota zata koma garinsu" da kuma yadda akayi sukayi musanyar akwati a karshe yace da ita
"Ba rabonmu bane suri" rabonta ne" ina so ki cire wannan kudin a ranki domin kuwa nidai tawa ta riga tazo karshe" bana so su kashe mun ke suri" domin kuwa duk ni na jawo miki wannan masifar na gwammace ni su kasheni" amma bazan barsu su kasheki ba" wannan shine kawai abinda zanyi miki na karshe a matsayina na masoyinki
Suri ta fashe da kuka ta dauki lokaci batayi shiru ba" domin kuwa taga ishara da idonta a zahiri" jiya jiyan nan take ba Raliya labarin zata zama miloniya"
Ashe duk fafutukar da takeyi Raliya ce zata amfana da miliyoyin kudin" wacce bata damu da kudin ba gashi ita kudin suke bi tana gudunsu" ita kuma suri data nace tana bin kudin gashi suna gudunta" Shin dama haka rayuwar duniya take?"
Hakika arziki nufi ne na Allah" Raliya 'yar kauye ta zama miloniya tabar suri a cikin daki mai duhi wasu azzaluman mutane suna gana mata azaba ita da masoyinta jarmai"
Suna nan cikin duhu suna maganganu sama-sama sai suka ji sautin harbin bindiga a cikin gidan har sau biyu suri ta fashe da kuka ta cewa jarma
"Gasu nan sunzo zasu kashemu jarmai" ina kake in rikeka sai dai su kashemu tare"
suri ta tashi cikin tsananin firgici ta lalubi jarmai a cikin duhun taji shi makure a jikin bango" ta lalubi hannayenshi dake manne da ankwa ta rikesu" jarmai yace da ita
"bana so su taba ki suri" ina son ki gudu ki koma ciki gaba da rayuwarki" kici gaba da karatu ni tawa tazo karshe suri"
kafin ya rufe baki ne" yaji ansa wani abu mai kama da rodi an sare kofar dakin ta katako" ta yanke jiki ta fadi kasa kamar tsawace ta fado a cikin dakin" wasu ifiritan mutane su biyu suka shigo cikin dakin rike da bindigogi da kuma cociloli a hannayensu"
Ifiritan mutanen suka haske wa masoyan idanuwansu
Daya ya kai hannu ya fizgo suri daga cikin masoyinta nata" dayan kuma ya kama kwalar rigar jarmai suka iza keyarsu zuwa waje"
Babu wanda ya zaci faruwar wani abu a cikin wadannan ifiritai biyu da suka fito da jarmai da kuma suri"
to amma kuma fitowarsu keda wuya daga cikin dakin ko taku daya basu kara ba" sai kato daya a cikin ifiritan ya kwantsama ihu" wanda ke rike da kwalar rigar jarmai ne" ya yanke jiki ya fadi" sannan ya saki bindigarshi ta fadi kasa"
Ragowar daya katon dake rike da suri" ganin abinda ya faru da abokinshi" sai ya ture ta gefe daya ta fadi
sannan ya auna goshin jarmai da bindigarshi" to amma kuma ya makara" kafin yaja kunamar bindigar" tuni jarmai yayi tsalle ya cimmashi yayi mishi irin naushin da yayi wa dan uwanshi da hannayenshi biyu dake dauke da ankwa a gefen kuncinshi"
Daya ifiritun shima ya hadu da bangon gidan ya fadi kasa ricaaa......