RALIYA-14
.
'Daya Ifiritun shima ya hadu da bangon gidan ya fadi kasa ricaaaa!! Kamar giwa ta fadi" jarmai ya dakawa suri tsawa!!
"yi sauri ki gudu suri"
Suri ta fasa kururuwa
"bazan tafi in barka anan ba jarmai"
"A daidai lokacin ne ifiritun farko da jarmai ya
Zubar yayi saurin lalubo bindigarshi dake kasa"
suri taga lokacin da ifiritun ya auna fankacecen
bayan masoyinta da bindiga kafin ta sake
kururuwa tuni har karar bindigar ya cika ko ina acikin gidan"
Jarmai yayi taga'taga kamar zai fadi sai ya dafe
hannunshi a jikin bango" ankwar dake kafarshi ta tadiyeshi ya zube kasa"
A lokacin ne ifiritu na biyu shima ya taso da
bindigarshi" duk da jarmai ya baje a kasa bai
hakura ba sai da ya sakar mashi bindigar a
goshinshi"
Kwanya ta fallatso mishi a jikinshi" suri ta sake
fasa kuwwa ta daka masu tsawa a fusace"
"Bakwa bukatar ci gaba da harbinshi ya mutu"
Ifiritu na biyu ya dawo da hankalinshi kanta yana mai murmushin mugunta yace da ita a fusace "mutuwarshi ta fiye mashi sauki fiye da
rayuwarshi"
Ifiritu na farko ya matso daf da ita ya daka mata
tsawa"
"Ina akwatin kudin dake hannunku su muka zo
amsa?"
Suri ta kankame kirjinta a tsorace tace dasu
"suna wurin kawata Raliya" da ita jarmai yayi
misanya a mota" kwamishinan 'yan sanda
akwatinta ya amsa na bogi" amma akwatin kudin suna can a wurinta" don Allah ku rabu damu haka nan kubi ta kauyensu can danmarke ku amso kudinku"
Ifiritan mutanen biyu suka dubi juna cikin
tsananin damuwa"
Na farko yace da ita
"Bamu cika son muna kashe mata ba a wannan
sana'a tamu da mukeyi na kashe mutane" Amma kuma bazamu barki haka nan mu tafi ki tona mana asiri ba" fada mana inda bakya so a jikin ki mu harba sauri muke yi 'yan mata"
Suri ta dubi fuskokin mutanen cikin hasken farin watan da ya cika ko ina a gidan" ta fara yi masu magiya tana kuka"
Don Allah kuyi hankuri" ku kyaleni ni daliba ce"
ina da kaka a gida gurguwa ce nike taimaka
mata
Ifiritan biyu suka fashe da dariyar mugunta"
dayan yace
"to ai shinkenan ma kin bamu amsa" bari mu
karya maki kafarki daya mu rabu dake" sai ki
koma gida kici gaba da yawon bara tare da
kakarki 'yan mata"
Zamanki gurguwa yafi ace mun kasheki kina
karama" bai kamata ki mutu yanzu ba"
Da gama sanar da ita yaja kunamar bingigar
saitin cinyarta kafin suri ta motsa sai taji wani
abu mai kamar kibiya ya soketa a cinyarta ta
dama" ta jefar da ita akan gawar masoyinta
jarmai" suri ta fasa kururuwa sannan ta lumshe
idanunta tana jiran mutuwa tazo ta dauketa"
ifiritun da ya harbeta yace da ita
Kada ki mance damu 'yan mata
FARAUTAR KUDI
ya jawo mukayi miki haka sunana Gambo
wannan kuma shine dumfama
"A can sama-sama suri taji muryoyinsu suna
dariya" sannan suka fice daga gidan tuhumar
suna murnar kashe-kashen da sukayi na 'yan
sandan dake gadin gidan da kuma jarmai" suri
taji jini yana malala a jikinta ta dada sake lumshe
idanu tana jiran mutuwa tayi hanzari tazo ta
dauketa" domin ta huta da azaba"
.
DON JIN YADDA RAYUWAR SURI KAWAR RALIYA YA KASANCE SAI A NEMI LITTAFIN
(BOYAYYEN MAKIRCI)
.
=====>+++++^+++++++<======
.
Raliya tana tsaye a cikin dakin mahaifiyarta ita
kadai" tun tashinta da safe" take a cikin dakin ta tsaya a jikin taga tana kallon sararin dake duniya acan bayan gidansu" da kuma sauran wasu wurare"
Hasken rana ya kutso ta cikin giza-gizan da suka toshe sararin samaniya" ya warwatsu ako ina a kauyen dan marke"
Ya haske gonaki da kuma sorayen gidaje" sannan kuma hasken ya warwatsu a cikin katafaren kogin dake bayan garin"
Daga inda Raliya take tsaye a cikin dakin tana iya hango kyallin ruwan yana toroko yana daukar idanu" masunta dake fita kamun kifi da safe sun haye kwale-kwale yana ta yawo dasu akan makeken kogin"
Raliya tayi ajiyar zuciya" sannan ta mayar da
hankalinta kan tunanin dake damun zuciyarta"
wanda ya hanata barci a daren da ya gabata"
Me yasa ta nemi rufa'i sama da kasa ta rasa
inda ya shiga tun rabuwarsu a yammacin jiya?"
ta aika gidansu ba sau daya ba ba kuma sau biyu ba" amma ance ba'a san inda ya shiga ba" saida dare yayi ne sannan wata yarinya dake tuyar kalallaba a kusa da gidan su Rufa'i tace ta
ganshi tare da wasu mutane masu bakaken kaya da yamma" amma bata san inda suka nufa ba
Wannan labari da Raliya ta samu yayi matukar
tayar mata da hankali domin kuwa indai Lafiya-
lafiya to tasan cewar Rufa'i bazai bar gida yaje
wani wuri kwana ba" bayan kuma yana dokin
dowawarta
Ta tashi da sassafe ta aika yaro gidansu Rufa'i
aka sake cewa da ita bai kwana a gida ba"
Na shiga uku!! Raliya tace a zuciyarta Ina Rufa'i yaje tun jiya anya kuwa ba sace shi akayi ba?"
Babu mamaki don hakan ta kasance domin kuwa Raliya tasan cewar wannan zamani da muke ciki yana da wahala" satar mutane ya zama ruwan dare a birane da kauyuka
Raliya taji hawaye ya zubo mata akan kyakkyawar fuskarta" ba ta share hawayen ba domin kuwa tasan cewar koma ta share wasu zasu sake zubowa" don haka saita bar tagwayen hawaye guda biyu suna gasar tsere a harabar fuskarta" tace a zuciyarta"
Allah ka karemin masoyina Rufa'i
Allah kasa kada su kashe min shi" sannan sai tasa hannu ta share hawayen a karo na farko sannan tayi ajiyar zuciya ta baro bakin tagar dakin ta dawo cikin daki ta zauna a bakin gado tayi tagumi
A daidai lokacin ne wani yaro ya shigo cikin dakin yace da ita cikin ladabi"
"Raliya wasu mutane a waje sunce wai kizo"
"su wanene?" Raliya ta tambaya yaron yace da ita" "Nima ban sansu ba"
"je ka kace ina zuwa" watakila ko masoyinta ne Rufa'i da abokinshi"
Raliya taji zuciyarta ta danyi sanyi" wa zaizo yace yana son ganina" in ba masoyina Rufa"i ba?"
Nan da nan tayi sauri ta mike zumbur ta nufi kofar gidansu tana fatan Allah yasa rufa'i ta ne ya dawo" fitarta keda wuya tayi karo da wasu mutane irin tsofaffin barikin nan wadanda suka kwana biyu amma kuma saboda rashin wahalhalu na yau da kullum jikinsu yana nan garas"
Kamar kananan yara banda jefi-jefin furfura data bayar dasu" suna sanye da bakaken kaya da huluna" da gani babu tambaya ansan jami'an tsaro ne" jajayen idanuwansu da gashin bakinsu dake kama da fuka-fukan jirgin sama ya isa ya tabbatar da hakan kai tsaye
Raliya ta tabbatar sune mutanen da ke son ganinta" to amma kuma a wanne dalili 'yan sanda zasu zo nemanta me tayi?"
Raliya taji gabanta ya fadi" ta tsaya daga baya-baya tana kallon mutanen cikin shakka da mamaki da kuma tsana" domin kuwa jikinta yana bata cewar akwai wata matsala babba dake shirin faruwa"
Rufa' imasoyinta ya bace bai kwana a gida ba" sannan kuma yanzu gashi wasu jami'an tsaro sunzo suna nemanta"
Raliya ta sake tambayar kanta" a daidai lokacin ne wani a cikin jami'an tsaron biyu yayi mata murmushi"
A nashi tsammanin wannan shine murmushin da namiji zai yiwa 'yan mata domin ya karfafa musu gwiwa su amince da abinda zai fadi masu" saidai kuma a bangaren Raliya murmushin yazo mata ne a yanayin da mutum zai gani a fuskar aljanin da malalacin yaro ya zana dan firamare ya zana a littafinshi na zane-zane
"ya kika tsaya daga baya-baya Raliya ki matso kusa damu" mu bakinki ne" wurinki muka zo"
mai yin murmushin ne ya sanar da ita"
Raliya ta kara taku daya ta tsaya inda jami'an tsaron suke" wani mai katuwar murya a cikinsu wanda tun zuwansu fuskarshi a murtuke take yace da ita
Mu jami'an tsaro ne" munzo wurinki ne ki bamu akwatinmu ki amshi naki" domin kuwa kin yi misaya a motar da kika hawo"
Raliya taji gabanta ya fadi" ta dafe kirjinta a tsorace Akwati?"
wanne akwatin ni banyi misaya da kowa ba"
mai murmushin ya dawo ya murtuke fuskarshi yace da ita"
"Bamu son ki bata mana lokaci Raliya" kinsan abinda muke nufi ki dauko mana kudinmu dala miliyan hamsin dake wurinki ki amshi akwatin tsummokaranki sauri mukeyi kinji ko?
Raliya ta sake daburcewa tana rawar jiki"
"wallahi ban san wannan maganar ba" akwatin da na dawo dashi yana wurin yayana Naziru kuma yaje zai budemun abokanshi sun sace akwatin jiya" babu wani akwati a hannuna"
Mai fara'ar yace da ita
"kije ku tattauna ke da yayanki ya fito miki da akwatinmu ki kawo mana" domin ki amshi masoyinki Rufa'i dake wurinmu?"
Raliya ta sake rikicewa"
"Rufa'i ? ta tambayesu" don Allah a ina kukaga Rufa'i masoyina ne" ku dawo min dashi"
Dayan yace da ita a fusace"
"yana hannunmu tun jiya da daddare" idan kina sonshi toki yi hanzarihanzarin fito mana da akwatinmu zamu sake dawowa anjima"
Idan kuma bakya sonshi toki shiga cikin gida ki dauko mana likkafani domin idan mun kasheshi mu sami abin jana'iza
Raliya tace dasu a rude"
"Na shiga uku!! Don Allah kuyi hakuri kada ku taba mun Rufa'i shi ne masoyina da zan aura" zan baku akwatin kudinku
"ta fashe da kuka to sai dai kuma daga Raliya har jami'an tsaron da suke tare da ita" babu wanda ya daga kanshi sama akan wata itaciyar kadanya dake a kusa da kofar gidan saitin tsohuwar a kori-kura"
Da ace wani a cikinsu zae daga kanshi sama da yayi nasarar hango ifiritan samari biyun dake a boye saman bishiyar tunda asuba" Gambo ne da abokin tafiyarshi Dumfama
.
======>++++++^+++++<======
.
Lokacin da Bilya da Aminu jangwarzo suka baro wurin Raliya sai suka koma bayan gari inda motarsu take" suka shiga suka zauna domin su sami nutsuwa su kammala hirarsu da suka fara a lokacin da suke tafiya akan hanyar
Tun daren jiya suke ta nanata wannan magana" a halin yanzu dinma zamansu keda wuya sai bilya ya dubi aminu yace dashi
Na fada maka tun jiya muddin......
.
MUDDIN ME ?
.
KO SUMA YAUDARAR OGA KWAMISHINA ZASUYI ?