Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

RALIYA 15

RALIYA-15
.
Bilya ya dubi Aminu yace dashi
"Na fada maka tun jiya" muddin kwamishina ya
dora hannunshi akan wadannan miliyoyin kudin to ba abinda zamu samu na dade da sanin halin kwamishina wajen hadama
Aminu ya gyara zama yace dashi
"Na fahimci wannan matsalar ni kaina Bilya
Bilya yace "munyi dabara tun jiya bamu sanarwa
kwamishina cewar mun kamo Rufa'i ba yayi
kyau da muka ce dashi" bamu sami sa'ar ganin
shi ba" kuma bana tsammanin zai gano inda
muka boyeshi"
Aminu yace "Ina fa zai gano tunda baiyi tsammmanin mun sake tunani ba" kawai da zarar ta bamu kudin tun
anan mu raba kudin mu" kowa ya san inda zai
nufa" domin kuwa na san kwamishina zaiyi
kokarin baza yara su nemomu
Bilya yayi dariya yace "Ina zai ganmu tunda dai ba kusa zamu tsaya ba" in dai Raliya ta amso mana akwatin kudin ina sa ran gobe kamar yanzu nakai kasar Colombia
Acp Aminu yace "Ni kuma nakai kasar Japan ko kuma Indonesia
tsofaffin biyu suka fashe da dariya hade da tafa
busassun hannuwansu" wani ragon maza dake
tsattsagar kan gero a cikin wata gona kusa dasu yayi saurin tashi a tsorace yana shirin bazawa aguje
.
=====**************************=====
.
Raliya tana zaune a kofar dakin kakarta tayi
shiru tana tunani" tana faman hada biyu da biyu kuma babu shakka ta sami hudu a amsarta sai yanzu ta sake dawo da tunaninta na dalilin da yasa data sauka a mota jiya taji akwatinta ya kara nauyi" sai da badamasi mai amalanke ya taimaketa ya dauko mata daga bakin titi zuwa cikin kauyensu" bayan kuma tun daga cikin jami'ar Bayero har zuwa bakin titi inda ta tsaya ta shiga mota da hannunta ta dauko akwatiakwatin kacokan babu wani nauyi"
.
Sannan kuma bayan ta dawo gida a lokacin da
Naziru ya matsa mata saita dauko mishi tabarau da tace ta sayo mashi tsarabar kano"
Raliya tayi mamaki sosai da akwatin yaki
budewa" bayan kuma a duniya tsawon shekarun
da ta dauka da wannan akwati bai taba bata
mata lokaci ba wajen rufewa da budewa ba"
Raliya ta sake jin tsoro ya kamata" tabbas ba
akwatinta bane" tace a zuciyarta" hakika misaya akayi min a mota" ba akwati na bane" to amma kuma babban abin takaicin shine tun jiya data ba Naziru akwatin domin ya kaiwa abokinshi Shegen Sama ya bude" bata sake ganinshi ba sai da daddare" data tambayeshi akwatinta ne yace da ita abokanshi sun sace akwatin daga
yabar musu ajiya yaje zai dawo" da ace babu
wannan sabuwar magana data taso"
Raliya bazata taba damuwa ba don yayanta ya
bayar mata da akwatin kayanta"
A kalla tasan cewar tunda dai yanzu aure za'ayi
mata zata sami wasu akwatinan da kuma wasu
sababbin kaya na sawa iri-iri
to amma kuma maganar wadannan mutanen da suka zo suka yi mata na tsabar kudi har Dala miliyan hamsin tayi matukar girgiza ta
kuma dole ne ma ta sami Naziru suyi magana"
domin kuwa bazata taba rufa mashi asiri ba" ita
kuma su kashe mata masoyinta a banza Hakika sunyi dabara da suka kama Rufa'i domin kuwa akan Rufa'i zata iya zuwa ta nemo musu duk inda akwatinsu yake takai musu"
.
Raliya taso ace ta sanarwa mahaifinta wannan
danyar magana domin asan halin da ake ciki a
gidansu" to amma kuma sai daga baya ta gano
cewar baiyana maganar ba abinda zai jawo sai
tashin hankali Kuma bayan haka ma wannan wata magana ce ta sirri da ake yinta a boye" maganar Dala Miliyan Hamsin ba karamar magana bace" dole ne tayi
taka tsantsan domin kuwa ba rayuwar Rufa'i
kawai ke a cikin hadari ba ita kanta rayuwarta a
halin yanzu yana cikin hadari"
Domin kuwa idan har ta salwantar da akwatin
kudin" to bayan sun kashe masoyinta Rufa'i
itama bazasu barta haka nan ba" wannan wani
abu ne da Raliya ta tabbatar kuma dole ne ta
kiyaye
Raliya tana nan zaune tana kissime-kissime
mahaifiyarta tana dakin girki rufin jinka tana
Fama da hayaki zuwa can saita ji fiton yayanta
Naziru ya shigo gida yana wakar Bob Marley
da gwarancin turancin sa yana sanye da kodadden wandonshi na tamfal kalar fatar jaki" da kuma wata jar riga ta saka wacce bai cika sata ba" sai yana jin tsiya
Duk lokacin da Naziru yasa wannan jar riga ko
magana bai cika yi ba a gidansu" don haka ne
yasa da zarar Raliya taga yasa rigar itama take
dauke mishi kanta" domin kuwa ya taba sa rigar daga kawai tace dashi "ina kwana" yayi kwallo da ita cikin tabo
Mahaifinsu ya fito daga cikin daki a guje" ya
rarumo iccen turken awaki ya wawukeshi suka
Zuba a guje zuwa kofar gida
Naziru bai sake dawowa gidan ba saida aka yi
sati biyu
To amma kuma a wannan karon duk da yake
Raliya ta tuno wannan al'amari daya taba
faruwa" sai taji bata fargabar tunkararshi da
maganar akwatinta na jiya" zuciyarta tuni ta
gama bushewa" domin kuwa an tabo wani
bangare na ruhinta" an taba mata masoyinta
Rufa'i
.
Ina Son ganinka yaya Naziru" akwai maganar
da nakeso mu yi
Naziru ya tsaya da fiton da yake yi"
"wacce magana kikeso ki fada mun?
Raliya ta sake kallon mahaifiyarta dake fifita wuta a murhu tace da Naziru"
"Zanso mu shiga daki domin kuwa banaso kowa yaji abinda zamu tattauna Naziru"
"Naziru yayi tsaki sannan ya duba wani kafcecen
agogon dake hannunshi kamar ankwa" agogon
yafi shekaru biyar da daina aiki" amma haka nan yake barazana dashi Yace da ita
"lokaci yayi nisa" sauri nake yi zanje wani wuri ki bari mana saina dawo"
Raliya tace dashi "kayi hankuri ka saurareni ba dadewa zamuyi ba"
Naziru yabi Raliya suka shiga cikin dakin
mahaifiyarsu" ya sake duban mushen agogon
dake hannunsa" ya kosa ya tafi" domin kuwa tun jiya yakai tsohon babur dinshi gari ya sayar dashi naira dubu biyu" yana so ne ya samu isassun kudin mota ta yadda in ya bar gida zaiyi nisa ba tare da anji labarin inda yake ba
Yanzun nan shirin tafiya yayi zuwa fadama"
domin hako akwatin kudinshi ya gudu" yazo ne
yayi wa cikin gidansu kallon yaushe gamo" da
kuma wani guru da ya mance dashi a dakinshi
maganin bindiga Da kuma wukarshi da yake daura ta a kwankwaso duk lokacin da zaiyi wata tafiya ta musamman
gashi yanzun ya shigo kuma Raliya zata tsareshi da surutu" yace da ita a fusace bayan sun shiga dakin
"Raliya wai wacce irin magana ce na fada maki
sauri nake yi "Raliya ta tsaya a gabanshi suka hada idanu tace dashi babu alamar fargaba"
Ina so ne kaje ka dauko min akwatin dana baka
jiya" domin kuwa nima ba nawa bane" na wasu
mutane ne da muka yi misaya a mota" akwai
wani muhimmin abu dake ciki"
Naziru yaji numfashin shi ya tsaya cak!!
Yayi sororo a tsaye yana bitar maganar
kanwarshi" sai kace ta yafa masa wuta a
tsakiyar kanshi" wannan saurin canzawa da
Naziru yayi a cikin dan lokaci kankani shiya sake tabbatarwa Raliya cewar da gaske Naziru ya bude akwatin yaga abinda ke ciki" kuma har
Yanzu akwatin yana nan a wurinshi ya boyeshi"
Naziru yace da ita a fusace
"Na fahimci baki san halina ba Raliya" ban taba
nuna maki bacin raina ba shiyasa baki jin shakkar tunkarata da maganganun da kike so" to na cinye akwatin bazan baki ba" in kina da abinda zakiyi kije kiyi
"Raliya taji zuciyarta ta dauki radadi" ta tuno
halin da masoyinta rufa'i yake ciki ta cewa
Naziru
"Zan so kasan cewar wannan akwatin dake
hannunka daidai take da rayuwar masoyina
Rufa'i kuma daidai yake da rayuwar wadansu
mutane da dama bayan Rufa'i ciki har dani da
kai da iyayenmu
kasancewar ka bude akwatin tun jiya kaga abinda yake ciki" ina so ka canza niyyarka ta guduwa da wadannan kudade Naziru" domin kuwa koda ace ka tafi baza kayi nisa ba za'a cafkeka" domin kuma bakai kadai bane ke farautar wadannan kudin a duniya
Akwai mutane da dama" kuma wasu daga cikinsu a yanzu haka sun zo nan garin suna nan suna lura da duk wani motsi da akeyi kuma sune suka sace min masoyina jiya" don haka kaje ka dauko akwatinsu in kai musu domin in amso Rufa'i kada su kashesh
Naziru yayi makararriyar dariyar mugunta" yace
da ita "Baki da hankali Raliya" ke yarinya ce karama baki san muhimmancin kudi ba a rayuwar Bil-Adama" da ace kin san yanda kudi suke a rayuwar duniya" bazaki taba tsammanin zan tausaya maki inyi asarar miliyoyin kudi domin ki amso masoyinki ba
Don haka ina so ki san cewar akan wadannan
kudin ban damu ba suzo su tafi dake da duk
mutanen gidan nan" in suna bukata suzo su tafi
da mutanen garin nan baki daya suyi garkuwa
dasu bazan taba dawo da wannan akwatin ba" kiyi hakuri ki sake wani saurayin kanwata"
Raliya taji hawaye sun zubo mata tace da
Naziru kada kayi min haka Naziru" ka tausayawa rayuwata" ka duba halin da nake ciki" ka tuna cewar kudi komai yawansu zasu iya karewa" ni kuma 'yar uwarka ce bazaka taba samun kwatankwacina ba" bai kamata ace ka jefani acikin wannan masifar ba
Naziru yaci gaba da murmushin mugunta yace
"Baki san kudi ba Raliya" baki san zafin Farautar Kudi ba a duniya" yanzu a wannan
duniyar kudi sune komai duk wanda kika gani su yake nema" idan baka da kudi a duniya ba abinda zaka iya mallaka" amma idan kana da kudi zaka iya mallakar komai in dai yana wannan duniyar"
Raliya ta share hawayenta tace dashi
"kudi bazasu iya mallaka maka wata kanwar ba
idan bani a duniya" sannan kuma kudi bazasu
mallaka maka wasu iyayen ba idan kaja aka zo
aka karkashemu dasu baba da mama ko ka taba ganin wanda ya sayi "yan uwa da iyaye da
danginshi dole ne ka tausaya mana Naziru" ka
hakura da kudin nan idan kana da rabo saika
samu wasu anan gaba
Naziru ya murtuke fuskarshi yace da ita
"kudi suna sayen duk wadannan mutane da kika lissafo Raliya" samun kudin sune masu wahala agareni Da Zarar.....