Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

RALIYA 16

RALIYA-16
.
Naziru ya murtuke fuska yace da
ita kudi suna sayen duk wadannan
mutane da kika lissafo Raliya" samun kudin sune masu wahala a gareni" da zarar na mallakesu" ahannuna nasan
inda zanje in sayi wasu 'yan uwan da
duk wani mutum dana ke bukata a duniya" da
Zarar na nema zan samu" ki dana batawa
kanki lokaci Raliya" domin kuwa har abada bazan taba fitowa da wannan akwatin ba
Naziru ya daga mata hannu wacce ke
faman share hawaye
"sai watarana kanwata ni zan tafi kada ki
Zargeni kadan kenan daga cikin
Laifin Kudi sune ke jawo mana rikice-rikice a
duniya muke karkashe 'yan uwanmu ba laifina
bane Naziru ya sakai ya fita daga dakin
yana dariyar mugunta" cikin minti daya ya shiga dakinshi ya daura gurunshi da wukarshi a kwankwaso sannan ya fito cikin hanzari ya nufi bayan gari domin yaje fadamarsu ya hako
miliyoyin kudin shi ya shiga uwa duniya
Naziru yayi ajiyar zuciya sannan yayi
murmushi KUDI Wadannan halittun da dan
adam ya kirkiro a duniya sun dade suna bashi
wahala" ya neme su sunki zama" to amma yanzu kam tabbas sun zo kuma bazai taba bari su sake kulle mashi ba Naziru baiyi nisa da fara tafiya ba ifiritan mutane biyu dake boye a saman bishiya kadanya dake akofar gidansu suka sauko cikin hanzari kamar kadangaru" suka bishi a baya" suna tafiya suna wasa da karfinsu a matsayinsu na tsofaffin 'yan dambe"
.
======>+++++()+++++<=======
.
Har zuwa lokacin da Naziru Yakai fadama
Zuciyarshi bata daina wasi-wasi ba domin kuwa shi kanshi abin ya bashi mamaki
saikace amafarki Naziru ya tuno abokinshi marigayi Shegen Sama yana can karkashin kogi" yana rabawa kifaye da kwaduna abin kalaci" Naziru yayi murmushin samun nasara sannan ya tuno kanwarshi Raliya" bazai taba
mancewa da Raliya ba aduk inda yake aduniya" domin ba ba don ita ba da bai sami wannan miliyoyin kudi ba Naziru ya isa gindin dorawarsu ta jiya" inda suka binne akwatin kudin shida abokinshi Shegen Sama nan da nan ya durkusa yasa gwiwoyinshi akasa ya fara kwakulo kasar sannu ahankali yana tureta gefe daya" sai kace wanda ke gino dankali" tsawon lokaci yana ta kwakulo ramin sai ya cimma jikin akwatin yana nan akafe a cikin ramin yadda suka barshi jiya Naziru ya karashe ture kasar yasa yannu biyu ya zaro akwatin daga cikin ramin duk kasa ta dambare a jikin akwatin"
Naziru ya share ko ina sannan ya kurawa akwatin idanu yana murmushi
Daga nan ina ya kamata ya nufa? ya tambayi
kanshi kamata yayi ya fara kokarin
barin wannan kauyen idan yaso ko ina yaje zai
sami damar yin duk wasu shirye shiryen barin Kasar nan cikin kwanciyar hankali Naziru ya dauki akwatin ya rungume a kirjin shi zai motsa kenan ya tafi sai yaji wani bakon hancin bindiga yana asuwaki a gefen kunnenshi a lokacin ne yaji wata murya mai kama da fasasshiyar lasifikar rikoda tace dashi
"Idan ka motsa daga inda kake ka lissafa kanka
cikin wadanda kwanansu ya kare awannan
safiyar Naziru yaji wani bakon hannu mai kama da bayan itace ya fado kan kumatunshi"
sannan muryar dake gargadinshi taci gaba
"yi sauri ka ajiye mana akwatin kudinmu bamu
makara ba tun asuba muke tare dakai shashasha"
.
======>++++()++++++<=======
.
"Mun dawo ne domin mu amshi akwatin kudinmu Raliya" dama mun sanar dake cewar
Zamu dawo bada jimawa ba" shiga ciki ki fito
mana da kudinmu ko kuma likkafanin jana'izar
masoyin ki Rufa'i
A.c.p Bilya ya dakawa Raliya tsawa dake tsaye
tana kyarma tun lokacin da suka aika a kira
musu ita" Raliya ta dubeshi a tsorace tana niyyar fashewa da kuka
"Zan fada maku wurin da zakuje ku amso kudinku" suna wurin yayana yanzun nan ya fito
daga cikin gida ya tafi fadama zaije ya tonosu yagudu Raliya ta saurara kadan sannan taci
gaba "Don Allah kada ku taba mun yayana
Naziru" ku amshi kudinku kawai" bani da wani
dan uwa aduniya sai yaya na Aminu jangwarzo ya daka mata tsawa cikin sauri "Ina ne fadamar da ya tafi" yi sauri ki nuna mana" bama son bata lokaci Raliya ta nuna musu hanyar fadamar tana sheshshekar kuka" jami'an tsaron
biyu suka garzaya a guje kamar ransu zai fita
domin su cimma Naziru
.
=====>++++++*****+++++<=======
.
"Ka ajiye akwatin kuma bama son ka motsa" ko bakajin hausa ne? Dumfama ya sake dakawa Naziru tsawa" kamar harbin bindiga" bai san lokacin da ya saki akwatin ya fadi kasa Rambo dake rike da tashi bindigar yayi saurin dukawa domin ya dauke akwatin kudin.
A daidai lokacin ne Naziru ya shammace shi ya
matso da hannunshi daidai kwankwason shi ya
Zaro sullubebiyar wukarshi" kafin Rambo ya
dauke akwatin ya sake dawowa" sai yaji Dumfama" ya fasa kururuwa iyakar karfinshi"
Bindigarshi ta fadi kasa" Rambo ya fasa daukar
akwatin zai juyo da bindigarshi kenan ya harbi
Naziru sai yaji wani abu ya toshe
masa fuska kamar mota tabi ta kanshi ta wuce
nan take shima ya fasa ihu ya zube a kasa tare da babban abokinshi
.
Abubuwa uku ne suka faru a lokaci daya Da farko Naziru ne ya juya kan wukarshi ya
sokawa dumfama a tumbinshi sai da ta kusa
nutsewa dukanta" sannan kuma yasa gindin
takalmin shi ya naushi fuskar Rambo daga nan
baya yayi hanzarin mika hannu ya sure akwatin
kudin Naziru ya tsallake ifiritan samarin
biyu dake kwance suna juye-juye" ya runtse
akwatin akirjinshi da hannu daya" sannan ya
gangara ta wata siririyar hanya dake cikin
fadamar yaci gaba da gudu ya juyo fankacecen
bayanshi"
A daidai lokacin ne Rambo ya tashiya lalubi
bindigarshi dake kasa" to amma kuma baya iya
ganin komai sai wasu fararen taurari dake gada
a cikin idanuwanshi" da kuma dan dishi dishin
koren ganyayen dake cunkushe ako ina a cikin
fadamar a cikin dan abinda ya gani ne kadan-
kadan ya hango Naziru yana gudu dauke da
akwatin kudin ya juyo bayanshi saitin inda Rambo ke zaune a kasa Rambo ya auna fankacecen bayan Naziru sannan yaja kunamar bindigar" tun kafin sautin bindigar ya bayyana daga can nesa Naziru yayi tsalle sama kamar an buga kwallon kafa" akwatin kudin ne ya fara dawowa kasa" kafin gawar Naziru ta Fado kanshi jini yana tsiyaya ta bakin shi kamar an
bude famfon ruwa Rambo ya tashi da kyar da takarkara ya nufi inda akwatin kudin suke" da zuwanshi yana huci kamar maciji" har zai wuce sai yayiwa gawar Naziru kallon karshe" domin kuwa acikin shekaru fiye da goma wannan shine karo na farko" da ya samu matsala a wannan sana'ar tasu sannan kuma rabon da wani ya sami sa'a ya nausheshi tun a zamanin da yake dambe" to amma kuma wannan karon da ya dubi miliyoyin kudin dake hannunshi a cikin akwati saiya ji abin ya bashi sha'awa bai san lokacin da yayi murmushi ba. Domin kuwa ba wanda zai sami Dala miliyan hamsin a duniya kudi hannu" yayi tsammanin
bazai sha wahala ba" Rambo ya koma inda
abokinshi Dumfama yake kwance ya dafe cikin shi inda Naziru ya caka mishi zundumemiyar
wukarshi" fuskarshi ta canza ta koma launin
shudi-shudi" da kyar yake numfashi ya daga
kanshi ya kalli Rambo wanda ke tsaye da
Miliyoyin Kudin a hannun shi.
A gaisheka namijin duniya" yace dashi yana
numfashin karfin hali" da'ace yagudu ya sha
da ba abinda zai hana in kashe kaina in huta da
bakin ciki Dumfama ya dubi raunin dake dafe a
hannunshi ya kalli jinin dake biyowa ta yatsunshi kamar ya matse ledar manja" ya lumshe idanunshi ya sake budewa sannan yace "yi sauri ka daukeni mubar nan
abokina" yayi min rauni" ina bukatar agajin gaggawa Rambo yayi murmushi sannan yace
da dumfama baka bukatar zuwa ko ina Dumfama zamanka anan zai fiye maka sauki
Dumfama ya dubi abokinshi atsorace ban gane abinda kake nufi ba Rambo" yanzu fa ba lokacin wasa ba ne" na kosa muje asibiti jinina
ya kusa karewa Rambo ya sake kankame akwatin kudin ya ce "Baka da hankali abokina" me yasa kake tsammanin zan iya rabuwa da
wadannan Miliyoyin kudin ? Ka tayani Addu'ar
neman sa'a zan tafi sai mun hadu adarussalam
wannan itace ranar da zamu rabu abokina" na
sami abinda na fito nema shekara da shekaru.
Dumfama ya kalli Rambo cikin kunan
rai. ka bani kunya Rambo" ban taba tsammanin
akwai wasu kudin da zaka samu ka gujeni ba"
banyi tsammani ba Rambo ya fashe da dariyar mugunta"
"Ba'ayin amana da kudi abokina Miliyan
Hamsin ba kudin da zaka bani amanarsu bane awannan duniyar" tun ina yaro nake
Farautar Kudi shekaru ashirin kenan sai yau
na same su Gobe zan gudu in tafi Kasar amurka kada ka damu abokina ko bayan ka mutu zan rika tunawa dakai" idan na gina kamfani sunanka zan sawa kamfanin" ai nayi maka halacci Dumfama" ko banyi maka ba abokina?"
Rambo ya sake fashewa da dariyar mugunta
sannan ya kankame akwatin kudin ya
juya da sauri kamar walkiya ya bace a cikin
fadamar Dumfama ya cije lebenshi a fusace"
sannan ya dubi jinin dake zuba daga jikinshi"
yasan cewar nan bada wani lokaci ba" jinin
jikinshi zai kare ya mutu" a wulakance a cikin daji" sai yanzu Dumfama ya tuno irin barnar da yayi arayuwarshi"
Ya taba jagorantar 'yan fashi sunje sun kashe
kawunshi sun kwashe dukiyarshi" to menene don yanzu abokinshi yaci amanarshi ya gudu da kudin da suka farauto tare?" wannan kadan
ne daga cikin halin 'yan adam.
.
Dumfama ya rarrafa yana cije lebe ya dauko
bindigarshi data fadi cikin wani alayyahu" ya rike bindigar ya kura wa hancinta idanu
tsawon lokaci a fusace yana neman abinda zai
kashe a cikin wannan fadamar" domin ya huce haushin abinda abokinshi yayi mishi Yana rike da bindigar yana waige-waige domin yaga giftawar wani tsuntsu ya harbeshi su mutu tare"
Cikin sa'a ya hangi wasu mutane sun nufo inda
yake a guje" sanye da kayan 'yan sanda"
Dumfama yayi murmushin farin ciki domin kuwa duk duniya bashi da wani abokin gaba irin 'dan sanda" ya dade yana shan duka ahannun 'yan sanda har karyashi sun taba yi a kafa lokacin da yana yaro"
Dumfama ya saita bindigarshi ya
auna wani kakkaura a cikin tsofaffin 'yan sandan biyu" ya dirka masa bindigar"
Dan sandan yayi kuwwa sannan.......