Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Raliya 18

RALIYA-18
.
Rambo yahau saman bishiyar ya boye kudin a
makale a jikinshi" ya dora akwatin akan wani
reshe ya kwantar dashi" sannan ya fara shawarar fita neman abinci" domin kuwa a halin yanzu ya fahimci idan har bai nemi abinci ba" to in ba sa'a ba nan da wani lokaci bazai iya tafiya ba Rambo ya sauko daga bishiyar yabar akwatin kudin shi a sama" sannan ya fara waige-waige domin ya samu wani abu a cikin kayan itatuwa da zai tsinka yaci" to amma kuma duk bishiyoyin dake wajen babu wanda ke da wani abinci da za'a tsinka" yawanci daga tsofaffin kukoki" sai gamji da kuma gawo" sai kuma dorawa da kadanya birjik ko ina
Rambo ya yanke shawarar shiga cikin dajin domin samun abinci" ya fara tafiya kenan saiya tsaya ya waigo ya daga kanshi sama" ya tabbatar akwatin kudinshi suna nan ba abinda ya samesu Rambo yaci gaba da tafiya yana yi yana
waigawa" domin kuwa ba'a son ranshi zai rabu
da wannan akwati mai miliyoyin kudi ba" to
amma kuma ai yunwa ta kare komai da zarar ya
nemi abinci yaci" zai dawo cikin hanzari yahau
sama ya kwanta tare da akwatinshi kafin gari ya waye
Rambo yana cikin tafiya sai yaci karo da wata
doguwar giginya" wacce 'ya'yanta suka nuna
jawur dasu a sama" har guda biyu sun fado kasa Rambo yayi hanzarin daukar giginya daya yaji ta nuna" nan da nan ya share wuri ya zauna agindin itaciyar giginyar" ya fasa kwallo daya dake hannunshi" ya fara sha bai dade ba azaune yaji tunaninshi ya koma can wata duniya" yakamata ace a yanzu haka yana kasar turai" tare da fararen 'yan matan turawa kyawawa Amma yanzu cikin rashin sa'a gashi a daji cikin dare" yana neman abinci zaici to amma kuma da zarar Rambo ya tuno irin miliyoyin kudin da suka jefashi cikin wannan wahalar sai yaji sun cancanta su sashi kwana a daji
Rambo ya kammala shanye giginyar ya
kishingida domin ya dan huta" kafin ya koma inda ya boye akwatin akan bishiya" yana nan har barci ya dan fara surashi" ba'a dade ba" ba zato ba tsammani sai yaji wasu abubuwa dake kama da wukake su kimanin ashirin sun hadu wuri guda sun kwashe naman cinyarshi a lokaci daya kamar yadda yaro ke yago tsokar biredi" idan yana jin yunwa
Rambo ya tashi a gigice yakai hannu a fusace"
yaji ya mari fuskar wani abu cukus! Mai laima
laima" dago kanshi keda wuya yana kara sai ya
hada idanu da katuwar kurar dake tsaye a kanshi tana tauna naman dake bakinta" farin wata ya haske ko ina a jikinta" tana tauna naman suna kallon-kallo ita da Rambo
Gama taunar keda wuya sai ta sake matsowa da sauri wajen Rambo tana gurnani"
Rambo ya fasa kururuwa iyakar karfinshi sannan ya sake matsawa baya a tsorace ya duba cinyarshi yaga farin kashi a fili yana kyalli a cikin hasken farin watan babu tsoka
Rambo ya dafe kafarshi yaja jikinshi ya matsa
jikin itaciyar giginyar" domin yabar inda kurar
Take A lokacin ne ta rugo a guje ta haureshi da kafarta na hagu" sannan ta tattakeshi da ragowar kafafuwanta" ta sake tirmisa katon bakinta a kwankwasonshi" ta sake samun nasarar debo katuwar tsokar nama"
Rambo ya fashe da kuka yana kururuwa" kurar ta sake tsayawa tana taunar naman dake bakinta"
tana kallon Rambo dake burari da jajayen
idanuwansa" bayan ta kammala sai ta sake
matsawa inda yake a kwance baya iya tashi" tayi tsalle ta sake dirmisa bakinta a jikinshi" ta jawo fatar kirjinshi yana kallo" fatar ta biyota nan da nan kurar ya tattake fatar ta tsinkata" taci gaba da taunawa" ko ina a jikin Rambo yayi face-face da jini"
Abu na karshe da yaji kafin ranshi ya fita" shine
bakin kurar dake kokarin karya dokin wuyanshi"
har zuwa lokacin da Rambo ya mutu hankalinshi yana kan akwatin kudinshi da ya boye a saman bishiya
Da ace yasan kurar zata sake biyoshi da bai
sauko daga saman bishiyar ya bar akwatin
kudinshi ba.
Kafin safiya tayi" kurar ta gayyato jariran
'ya'yanta suka karashe dan abinda taci ta rage
na ragowar jikin Rambo
.
=====>**********************<=====
.
Lokacin daurin auren Rufa'i da masoyiyarsa
Raliya yazo
A ranar daurin auren matasan karkara sunyi
wasanni iri iri da kuma raye-raye" da bikin ya
tashi ne abokan Rufa'i suka rakashi dakin
amaryarshi Raliya"
Duk wanda ya kalli wadannan ma'aurata biyu
yasan cewar suna cikin farin ciki" domin kuwa
Allah ya cika masu burinsu
Haka Rufa'i da matarshi Raliya" suka ci gaba da
rayuwarsu a kauyen Danmarke" wani lokaci idan suna cikin nishado haka kawai sai su tuno rigimar da akayi a kauyensu na misayar akwati a mota duk da yake cewar abin tsoro ne" yakan ba Raliya dariya"
Tasancewar wannan al'amari ya zama tarihi
bazai sake faruwa ba"
Abinda Rufa'i da matarshi Raliya basu sani ba
shine akwatin da ake ta rigima a kanshi har
Yanzu yana nan a raye a saman wata bishiya tun watanni uku da suka wuce
.
A safiyar wata lahadi ne an tashi da lullumi da
kuma sanyi muku-muku" wata tsohuwar mota
mai ruwan toka kirar (HONDA ACCORD) ta keto
ta cikin kauyen tungar malam tana burari
kamar an tayar da injin nika
motar tazo daidai wurin da wasu mutane ke zaune sun zagaye wutar dake ci suna shan dumi" tare da wata budurwa dake sayar da koko da siga" kwatsam! Sai motar ta fada cikin wani karamin rami" inda wata kwata kebi tana wucewa motar ta yunkura kamar zata haye ramin" sai kuma ta sare nan take tayi dif" ta mutu ko kawo wuta batayi
Wani dogon mutum ke cikin motar tare da wata 'yar figilgilar matarshi tana sanye da atamfa dinkin zamani ta tsira dankwalinta a kusa da goshinta tana zazzare idanuwa" da ganinta ansan cewar da wahala tayi hankuri da kuma ladabi Mutumin yaci gaba da shurar motar kamar keken dinki" amma kuma ko sau daya bata kawo wuta ba" yana cikin kokarin ganin motar ta tashi ne" sai mutanen kauyen suka ji matar dake cikin motar ta fara balbalawa mijin nata masifa
"Wai menene haka BALARABE ?
Baka iya fita ka bude murfin injin motar domin kaga abinda ke damunta" idan ka sake har lokaci ya kure ban sami wacce zanje nema ba wallahi sai ranka ya baci"
tun jiya kasan motar bata da lafiya" amma baka kaita an gyara ba sai yanzu da muka fito zaka kama wani haure hauren munafurci"
Dogon mutumin ya share zufar dake fuskarshi da kuma dogon gemunshi yace da matar a fusace"
Amma baki da imani ASABE saboda Allah da gangan zan lalata motar tawa" ni banfiki son muje lafiya domin inyi sauri in dawo ba" ina fa da aikin da zanyi kika matsa mani saina kaiki unguwar nan" kuma yanzu zaki kama yi mani masifa" to da wanne zanji da lalacewar motar zanji ko kuwa da masifarki Asabe?
Mutanen kauyen suka mayar da hankalinsu kan mutumin da kuma matarshi wadanda suke ta misayar maganganu a cikin motar" wadanda ke shan dumi a bakin wutar" tuntuni sun bar wajen sun matso kusa da motar" sunyi mamaki da sukaji matar ta dakawa mutumin tsawa tace dashi a fusace
"Ni ce kake cewa masifaffiya balarabe ?"
Don kaga mun shigo cikin jama'a shine kake wannan cika bakin ko?" zamu bar nan din" zamu koma gida" saika fadamin wacce kake cewa masifaffiya" yan kwanakin nan nayi maka sakwa-sakwa naga ka fara raina ni" to wallahi zaka sha mamaki indai nice
Dogon mutumin yace da ita
"Idan mum bar nan don Allah kisa wuka ki yankani Asabe bana so ki barni da rai"
Wani dattijo dake a zaune a cikin mutanen kauyen yana shan koko a roba" ya taso yaje inda motar ta kafe ya duba ya cewa dogon mutumin
"Salamu-Alaikum malam ya akayi ne mukeji kuna ta sa-in-sa kaida iyalin naka meya faru ne?"
Dogon mutumin ya waigo ya kalli tsohon yace dashi" baba wannan matar bata da mutunci" wallahi in banda rashin imani tare muka fada da ita a cikin motar ta lalace" amma zata hauni da masifa" to ni zan lalata motar da kaina?" ko ta fini son motar tawa ne?
Tsohon ya dubi 'yar gajeriyar matar yaga ta zare mashi idanu" gata dai a tsayi bazata wuce rabin mijinta ba to amma kuma ko miskala zaratan bata shayin fada masa maganar da taga dama" wannan abu ya daurewa tsohon kai" yace da dogon mutumin
Bari in kira yara gasu can mu turaku mu gani" idan ka fita a cikin motar watakila a samu ta tashi"
Tsoho ya kwadawa wasu samari kira a cikin wadanda ke shan dumin nan da nan suka garzayo" suka matso wajen domin kuwa dama suna son zuwa kallon fadan da sukaji miji da matar sunayi a cikin motar" suna gudun kada suzo ba wani dalili ace sunje yin tsegumi ne"
Tsohon da kuma samarin suka hadu a bayan motar suka fara tura motar" balarabe yana tare da matarshi Asabe a cikin motar" har mutanen kauyen suka fitar da motar daga cikin kwatar"
Asabe bata sake fadan komai ba" saida balarabe ne ya fito yayi musu godiya ya basu hannu suka gaisa yana sanye da fararen kayanshi farare dinkin kaftani" dake tattare da wani tarihi da balarabe baya so ya rika tunoshi" tsohon ya cewa balarabe
malam indai sha'anin matane sai kayi hankuri ko ina haka suke kaji Allah ya kiyaye hanya sai kun dawo
Balarabe ya shiga cikin motar ya tayar da ita" saida ya amshi wuta ya tuka ya tafi tare da azababbiyar matarshe Asabe wadannan ma'aurata biyu dake a cikin motar suna tattare da dimbin tarihi mai yawa a zamanin aurensu" Allah ya hadasu suka zama miji da mata amma kuma kowa ya gansu yasan cewar ba abokan zama da juna bane
Domin kuwa a kullum Asabe bata da wani aiki sai musgunawa wannan miji nata malam balarabe wanda yake kamilin mutum mai mutunci da kwarjini a wurin mutane"
A dalilin ta ya shiga cikin masifu a duniya iri-iri ba iyaka" to amma kuma har yanzun Allah bai kawo karshen zamansu ba" suna nan a zaune da dadi da ba dadi.....
.
KUN TUNA SUWAYE WAYANNAN MATA DA MIJIN ??