RALIYA-19
.
Da Dadi Ba Dadi dayawan mutanen suna rade-radin cewar wasu lokuta har dukan balarabe matar keyi ko kuma ta kulle gidan idan ya fita koda ya dawo ba zata bude mishi ya shigo ba" sai dai ya kwana a masallaci dake a kusa da gidan shi to idan ma duk wannan sharrine na masu karawa miya gishiri" abinda kowa ya sani ne Asabe bata ragawa malam balarabe kuma duk abinda tace tana so a duniya saiya nemo mata koda kuwa ace sata zaiyi
Da farko farko kafin ya aureta da kamshin arziki" to amma kuma tun sanda tazo gidanshi bana shekaru kusan biyu kenan duk al'amuranshi sun tabarbare sun lalace bashi da komai a duniya yanzu in banda wannan tsohuwar mota da kuma gidanshi
Ba karamin sa'a balarabe yaci Asabe ta barshi
ya kara aure ba a shekarar da ta gabata" koda
yake auren ba wani mai wahala bane" aure ne na rufawa juna asiri" wata yarinya ce data rabu da sana'ar bariki ko kuma da akayi korar matan
banza ta rasa inda zata sa kanta sai kakarta ta
daukota tazo da ita wajen malam balarabe domin yayi mata nasiha ta sami miji tayi aure"
Bayan yayi mata fada ne ya jawo hankalinta data tuba" sai ta sanarwa kakarta cewa malam
Balarabe take so" Da yake makwabtan juna ne da gidan balarabe dana kakar yarinyar mai suna MOMI ba'a wuce sati biyu ba aka daura auren momi ta tare gidan malam balarabe"
tun daga ranar da akayi auren saida Asabe tayi
kwana talatin da shida tana zazzaaga masifa a
cikin gidan" sannan kuma tun lokacin da akayi
auren har zuwa yanzu sai Asabe taga dama
takeyin abinci a gidan"
Idan ta bushi iska duk ranar da abincinta ya
Zagayo sai ta rike kayan abincin ba zata yiba
kuma bazata bar momi kishiyarta ta amsa tayi
girkin ba Sai dai idan malam balarabe ya dawo ya iske ba'ayi komai ba a gidan sai ya nemowa
amaryarshi abinda zataci a boye domin kuwa
idan ya kuskura Asabe ta gani to a ranar bazai
kwana a cikin gidan ba" sai dai ya kwana a masallaci
Sauda yawa Asabe tasha hayewa kishiyarta
momi ta nemeta da masifa na gaira ba dalili duk lokacin da irin wannan ta taso momi bata kula ta watarana haka kawai sunci abinci sun koshi" sai Asabe taje har dakin kishiyarta taci mata kwala tace da ita ta fahimci tana yi mata wani gani-gani don taga itace amarya a lokacin ne momi ta nunawa Asabe ko ita wacece" bayan ta lakadawa Asabe shegen duka a cikin dakin sai tace da ita "koda kike ganin ina yi maki shiru shiru" ni ba tsoronki nake yi ba" ina kyaleki ne Asabe saboda yanzu ba zaman banxa nakeyi ba" zaman aure nake yi"
Amma da ace a lokacin da nake zaune a gidan
MAI LOMA" kafin in tuba ke kanki baki isa kizo ki tare da irin wannan rashin mutunci ba""
na zauna da masifaffun mata wadanda suka
damaki suka shanyeki a wurin fitina" irinsu
marigayiya SIMA kawata" irin su surayya" da
kinsan zamanin da mukayi a baya da kin gane
cewa ni din nan hatsabibiya ce" to amma yanzu
bada bane ina so ki hada kai dani mu zauna
lafiya" Allah ya bamu miji mai kwazo da hakuri
me zai sa ki rika tayar mana da Hankali Asabe?
Tun daga wannan ranar Asabe ta fara tsorata da momi" domin kuwa ta gano cewar hakika itama momin ba kanwar lasa bace" haka suke ta zama cikin hakuri duk kurar da Asabe ta kwaso sai ta watsa ta akan mijinsu malam balarabe momi tana kallo bata ce komai domin kuwa ita a ganinta laifin balarabe ne daya bari har matarshi tafi karfin shi.
Balarabe yana da wata bakar mage wacce yake matukar so a duniya domin kuwa ita kanta magen tana da nata tarihin
rayuwar" farkon haduwar balarabe da wannan
magen tsoron ta yake ji" to amma daya ga cewar duk inda yaje tana nan biye dashi" sai ya dauke ta a matsayin amana tunda zuwan momi gidan take gatanta malam balarabe
Amma kuma ita Asabe haka kawai sai ta hau
magen da duka don balarabe yaji haushi idan
abin ya dami momi sai ta cewa Asabe
"Bai kamata kina zaluntar dabba ba Asabe
wannan magen da kike gani a wani lokaci da ya
wuce" tafi ki gatanci" wata kawata data rasu take da magen" bayan mutuwarta sai ta barwa wani gaye mai suna Sule Oska shi kuma da ya mutu gashi yanzun ta dawo hannun malam balarabe itama yanzu magen ta shiryu ne" ta baro gidan mai loma ta dawo gidan malamai bai kamata kina takura mana ba ni da ita" domin kuwa duk tarihin mu daya da ita"
Wannan shine dan takaitaccen tarihin rayuwar
auren malam balarabe tare da wannan mata data zame mashi karfen kafa wato Asabe ko a
lokacin da yake kan tuka motar a hanyar kauyen da zai kaita" sai da ya tuno irin wadannan halaye data sha yi mashi na alatsine tun shekara da shekaru Wani lokacin sai balarabe yayi kamar zai saki matarshi Asabe" to amma da zarar ya shigo
gidanshi sun hada ido" sai yaji yana masifar
sonta bazai iya rabuwa da ita ba"
Sannan kuma wasu lokutan koda ace ya dauki
alkawarin idan ta sake sashi wani abu bazai yi
ba" da zarar tazo ta tsaya gabanshi ta kalleshi ko me ta sashi sai ya tashi yaji jikinshi yana rawa ta riga ta zame mishi bala'i bazai iya rabuwa da ita ba"
Balarabe da Asabe suna cikin tafiya a motar"
suna wuce bukkokin masara a gonaki" da kuma giccikan dawa da aka girbe" sunzo daidai wajen wani shuri kenan" daidai wani dan karamin fako da ya zama saura ba.a noma shi ba" sai dai shanu da awaki ke shiga suna kiwo"
Sai motar balarabe ta sake birkicewa" tana zillo
Zuwa can saita mace" balarabe yayi ajiyar zuciya sannan yayi sauri yayi fakin a gefen hanyar cikin ciyawa"
Asabe tayi tsaki iyakar karfinta" suka hada ido da mijinta balarabe" yayi saurin kawar da kanshi gefe guda" domin kuwa yasan cewar ta gama kulewa" ci gaba da kallonta ba alheri bane agareshi" ga shi kuma nan daji ne ko fada suka yi babu mai sasantasu" sai dai ta bugi na bugu ta kyaleshi" ba yadda zaiyi da ita" Asabe ta dakawa balarabe tsawa a fusace
To ka tsaya zaman jiran motar ta gyara kanta ne bazaka fita ka duba aga abinda ya sameta ba? Balarabe yayi sauri ya bude kofar motar ya fita kafin ya bude murfin injin ne yaji Asabe taci gaba da balbala mishi azabar da ta saba"
Ina amfanin mace ta auri matsiyacin miji a
duniya" kawai da kuruciyar mutum duk ya lalace a banza ace kana da miji motar arziki ma bashi da ita" ni in banda ma kaddare me zan dauka awajen gayyar tsiya"
Ba wani muhalli na fita kunya" ba motar arziki
ba gara ma zama na a gidan Alhaji mai nasara
ba" ina cikin mutumci naja wa kaina na fito" dole ne in gaggauta komawa wurin tsohon mijina mai Nasara
Balarabe yana jin matarshi Asabe tana ta aikin
bala'i a cikin motar yasan cewar jira takeyi ya
tanka mata ta fito taci mishi mutunci" yaci gaba
da gyara wayoyin injin motar baice da ita uffan
ba Domin kuwa shi dama yawanci yafi mayar mata da martani idan yaga akwai mutane a kusa dasu to amma idan su biyu ne baya kulata ya riga ya saba
Akwai lokutan da in aikinta ya zagayo da zarar ya dawo daga sallar isha'i ya kwanta domin ya
huta" zata haushi da masifa" idan ta gama
wannan sai ta fada wannan" a haka har barci
yake kwasheshi tana masifa ita kadai bata sani
ba Idan irin haka ta faru" sai Asabe tasa hannu ta makawa balarabe duka ya tashi barci afirgice domin kuwa bata son tana zazzagawa mutum bala'i yayi shiru ya mayar da ita mahaukaciya tafi son ko sau daya ne mutum ya dan ce da ita wani abu" to amma kuma a wannan karon ma
haka akayi" Balarabe yaci gaba da gyaran motar kamar baya jinta!
Da Asabe tayi iya tsiyarta" har makogwaronta ya fara zafi" saita hakura taci gaba da zama a
cikin motar" zuwa can da taji zaman ya isheta"
saita bude motar ta fito waje" bata cewa
Balarabe komai ba" saita nufi gindin wata
karamar bishiya mai yawan reshuka" wacce ke
gefen labin da shanu ke wucewa" ta zauna a
gindin bishiyar" tana wasi-wasi a zuciyarta"
wajen wata bokarta zataje" batason tana bata
lokaci idan sunyi alkawari shiyasa ta matsawa
mijinta balarabe ya kawota a mota" gashi kuma
motar ta lalace" tuntuni bokar keyi mata aiki
akan wani hamshakin mai kudi da Asabe take
satar jiki taje wurinshi idan balarabe yaje wurin
aiki
Wasu makudan kudi take so ta fizga a wurin
attajirin" to amma kuma ta fahimci saita hada da 'yan dabarun da ta saba" na wani turare da take amsa a wurin bokarta"
Kudi!!" Hakika Asabe tana neman kudi a duniya
ido rufe" to amma kuma sunki taruwa"
Asabe tayi ajiyar zuciya" sannan ta jingina a jikin bishiyar ta daga kanta sama" tana kallon
reshikan dake kadawa suna kara sannu a hankali idan iska ta busa"
A lokacin ne Asabe ta hango wani abu mai duhu-duhu a boye a can kololuwar bishiyar ganyaye sun rufeshi"
Asabe ta kura idanunta a tsammaninta kukun
Zuma ne da ake sawa a kira zuma ta taru" to
amma kuma sai Asabe taga abin yana kyalli
kamar akwati" tabbas akwati ne!
Ta tabbatarwa zuciyarta" me ya kawo akwati
saman bishiya" anya kuwa ba barayi bane suka yi sata suka zo suka boye a saman bishiyar?"
Asabe ta kwadaya mijinta balarabe kira cikin
kosawa" nan da nan ya saki gyaran motar ya
hanzarta zuwa wurinta tayi saurin nuna mishi
abinda ta gani a saman bishiyar Wani abu na gani kamar akwati a saman bishiyar nan gashi can duba ka gani Balarabe ya daga kai yabi yatsan Asabe matarshi kuwa inda take nuna mashi" ya hango abin baki wuluk a cikin reshuka" akwai wani dan karfe mai
kyalli a jikinshi yace "tabbas wancan akwati ne" to amma meya kawo akwati nan?
Asabe tace da balarabe Hau ka ciro min shi mu gani" watakila rabona ne ya gifta
Balarabe ya kama bishiyar ya hau" sannu a
hankali har yakai reshen da akwatin yake"
Asabe tana kasa.
Tags
# Raliya
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
Raliya
Category:
Raliya