RALIYA-22
.
Hajiya Tabawa ta dade da sanin Asabe tun a
wani zaman sayar da abinci da tayi a cikin birni
to amma kuma bambancin rayuwarta da kuma
rayuwar Asabe shine ita tabawa ta dade da yin
murabus da sha'anin zaman aure
Rayuwarta gabaki daya ta dogara ne a tashoshin garuruwa na motoci" inda take kafa rumfunan sayar da abinci ita da yaranta na bariki" idan ta fahimci wannan garin yayi mata zafi ciniki ya cushe sai kuma ta canza sheka ta koma wani gari"
Amma ita Asabe bata shiga ruwa tsundum ba"
asha ruwan tsuntsaye take yi da harkar bariki"
tana dan tsayawa tayi aure" amma da zarar anyi auren to in har akaci sa'a yayi tsawon rai takanyi wata takwas zuwa wata tara" kuma in har ta fito to bata da wasu abokan arziki sai ire-iren. wadannan karuwai 'yan tasha"
wata majiya tace Asabe tana jin tsoron
mahaifinta ne shiyasa bata shiga harkar bariki
tsundum ba" Amma in har ta wayi gari watarana taga bashi a raye to ita ma bangaren Zaman aure sai dai a bar wa 'yan baya tarihi"
A can cikin dakin Asabe ita ma tana a kwance
batayi barci ba" ko da yake dama in ma aka
kawo mata zancen barci ai kamar anyi wauta ne Domin kuwa a yadd take kankame da wannan uwar akwati dake cike da Dalolin Amurka to bata da karfin imanin da zata iya runtsa idanu tayi barci bata kallonshi"
GARABASA:-- Yanda zaka ringa samun 50mb kyauta A Layinka na MTN
Lokaci-lokaci bayan ta tabbatar ta kulle ko ina a
cikin dakin ta zage labule" sai ta bude akwatin"
domin ta kara tabbatar da abinda ke a ciki ba
budar ido bane" kuma da gaske ne ba mafarki
take yi ba
Hakika kudin suna nan kamar yadda suka tsince su a daji ita da tsohon Mijinta za'a ce
Yanzu wato balarabe sarkin tsoro" domin ita dai
Asabe tana mamakin yadda za'ace dan adam mai rai da lafiya a jiki ya tsinci akwati cike da kudi" kuma wai har ya tsaya yana wani bata lokaci da wasi-wasi.
Kudi duk inda suke kudi ne Kuma ba abin
wasa bane" samun su kawai ke da wahala"
amma in har ka samesu" to duk matsalolin da
Zasu biyo baya masu saukin warwarewa ne"
kamar yadda Asabe tayi imani
Da ganin kudin tun a lokacin tasan cewar ba
kudin nageriya bane" to amma kuma tasan inda
ake canjin kudin a kano" domin kuwa ita 'yar
birni ce gaba da bayanta shiyasa ta yanke shawarar ta samu wuri ta boye
kanta da kuma kudin a lokaci guda"
Idan ta huta kuma ta gama shirya yadda zatayi
da kudin" daga nan sai ta debi wasu a ciki ko ba yawa koda a cikin habar zaninta ne ta nufi birni acanza mata su taga shin miliyan nawa zasu koma
Ko miliyan uku ta fara canzawa a kudin najeriya sun isheta ta sayi gida a birni" ta koma can kudin kuma sun isheta ta bude akawun a banki ta sami wata 'yar sana'a ta karya tana yi" tana canza kudin sannu a hankali yau da gobe wata rana duk sai ta mayar dasu kudin nageriya"
tasan cewar zuwa lokacin ta zama biloniya"
wacce za'a rika jin labarinta ako ina" kuma indai har kudin sun taru to tasan cewar ba kowanne mutum bane zai sa mata ido ya zargi inda ta same su"
Babu wata sana'a kwakkwara dan lokaci kankani ba" tasan matsalar wannan zamani" kuma tasan abinda mutane ke so" in dai zaka rika yiwa mutane alheri a wannan zamani kana basu kudi to komai laifin ka sai ka zama babban mutum"
Haka kawai sai ayi ta girmamaka ana yi maka
fadanci" komai ka fadi babu wanda zai karyataka" kuma abinda kake so shi za'ayi maka" don haka menene abin wahala?"
Tun da dai ga kudin nan tsaba a cikin akwati"
kuma duk nata ne ita kadae"
Asabe ta sake mika hannu tana zaune ta taba
akwatin ta sake bude shi" domin ta sake
tabbatarwa kudin sunanan"
A daidai lokacin da tayi murmushi ne bayan kudin sun haska mata idanunta sai taji wani abu a waje kamar faduwar nakiya ya cika ko ina a gidan" to amma kuma ba nakiya bace karar fadowar kofar gidan ne" wacce bangis ya kwadawa wani murgujejen gatari" ta tsage gida biyu ta tarwatse sai kace kofar gilashi bata jan katako na madaci ba"
Asabe taji gabanta ya fadi" tayi sauri jikinta yana kyarma ta mayar da murfin akwatin ta rufe shi da kyau" A sannan ne kuma taji sautin shigowar kartin a fusace cikin gidan" Asabe ta dafe kirjinta a tsora ce"
"me yake faruwa?" ta tambayi kanta"
me ya kawo barayi cikin gidan" kuma ya akayi
suka san akwai kudi a boye a cikin akwatin ta?"
Asabe ta fara safa da marwa a cikin dakin" gashi kuma babu hanyar guduwa nan da nan ta fara sheshshekar kuka tace a zuciyarta"
"Na shiga uku a ina zan boye kudina?"
A daidai lokacin da take inda-indar inda zata
boye kudinta ne" bala dake dauke da dakon
itatuwan duka ya sauke da kyar sannan ya duke
yana kwance igiyar da suka daure itacen"
Dama haka suke yi idan suka fita aiki kowa da
irin matsayin da yake takawa"
Bangis mai sare kofar gida" komai karfin kofa sai ya watsar da ita" a duka daya"
shi kuma bala shine ke daukar itatuwan duka"
musamman tunda rana zaije daji ya saro icen
koyar aduwa" ya tara wuri guda ya dauko"
Sai dare yayi idan sun fita aiki saiya sauke kowa ya zabi nashi" Amma aikin duka tare sukeyi" idan itatuwan sun kare a jikin mutum daya" sai su sake fita tsakar gida kowa ya sake zabo sabon icen su rufarwa wani"
kuma basu damu da mace ba" tun da dai
sha'anin sana'a ya kawo haka" ko mace suka
rufarwa a ka'ida sai itatuwan sun kare a jikinta
bayan sun yi mata lilis" kamar suna fyadin
shinkafa" ko dawa.
.
A wannan karon ma haka sukayi" bayan kowa
yazabi icce daya" ya shake a hannunsa sun bar
ragowar itacen a kasa" sai bangis yaja baya a
fusace" ya ruga a guje yasa kafa ya banke kofar
dakin farko wanda ke kusa da zaure" kofar ta
fashe a lokaci guda" sannan ta karkace tabar jikin ginin ita bata fadi ba" kuma bata tsaya ba"
Bangis yasa hannu ya fizgo kofar kwanon ta fadi kasa" karuwan dake ciki su biyu da kuma dan daudun suka taso a tsorace suna ihu" bangis ya kara shiga ciki da yake babu haske a cikin dakin sun kashe wuta"
Sai yakai hannu jikin bango a kusa da kofar dakin ya lalubo inda makunnin yake" ya kunna wuta haske ya gauraye ko ina a cikin dakin"
jiniya da kuma Idon Gwal suna a makure a jikin
bango daga su sai wasu guntayen shimi na barci masu hade da karamin siket" shi kuma daya gayyar tsiyar yana tsugunne ya makure a gefe daya ya lullube jikinshi da zani yana sanye da gajeren wando"
Da shigar bangis cikin dakin bai tsaya jiran komai ba" sai ya nufi inda karuwan biyu suke" bala ya biyoshi a baya dauke da nashi iccen" shi kuma lado niga" shugaban tafiyarsu" ya tsaya a waje yana gadi" don kada wani a cikin sauran dakunan ya bude ya fita a guje ya tona masu asiri"
Bala da bangis suka fara jibgar idon gwal da
jiniya kowanne idan ya daga nashi iccen sai ya
kure karfinshi" tun na bara waccan da kuma na
badi" wanda baizo ba" sannan su kimawa
kowacce a baya wani lokaci kuma ko ina suka
samu duka kawai suke yi" karuwan suka birkice
suna ihu" kowacce jikinta yayi kala-kala da jini
saboda kayayuwan dake a jikin itatuwan"sai da
Bala yaga jiniya ta sandare zata suma" sannan
ya tsaya fara tambayarta"
"Ina kudi da sarkoki suke?"
Idon gwal ce take da dan sauran rai" ita ce tayi
kokarin nuna musu wata jakarsu karama dake
sagale a jikin bango" ita ma karfin halin tayi
shine domin ta kwaci kanta kada su kashe ta"
amma duk jini ne a goshinta da fuskarta"
Bala yayi saurin zuwa" inda jakar take ya ciro ta
ya zage zip din ya leka ciki" babu wanda yasan
komai a ciki sai shi kadai bangis daya tsaya da duke" shima yana jiran bala
ya ciro jakar" sai ya tambaye shi da ido" bala ya
girgiza kai alamar ya gamsu da abinda ke cikin
jakar!
Yanda Zaka Hana Wayarka Shan Chaji
Bangis ya harari mata biyu dake zube a kasa"
cikin jini suna murkususu" sannan sai suka hada ganinsu wuri guda akan dan daudun wanda duk abinda akeyi yana makure yana rusa kuka" Bil hakki da gaskiya tamkar wani karamin yaro" bala yana rike da jakar a hannun hagu" dauke da katon ice a hannun dama"
Bangis ya rike nashi iccen da hannuwa biyu"
kamar zaiyi faskare" suka tararwa katon
shu'umin dan daudun suna ta jibgarsa baji ba
gani" ya jefar da zanin daga shi sai gajeren
wando fari" kafin kiftawar ido da bismilla duk sun farfasa masa fata" jini yana zuba" kamar ruwan leda" a wannan karon bangis ya tambayeshi
"Ina kudinka suke?"
Dan daudun yace a tsorace yana magiya"
"kudina suna wajen yayata" kuje ku tambayeta
Ita ke da sarkoki masu tsada" kuyi mani rai babu kudi a wajena" bala yayi mamakin yadda muryarshi ta dawo ta namiji garas" kamar bai taba rangwada ba" ya
dubi fuskarshi yaga tasha shegen kalangu da
kuma jan baki da kwalli radau"
Idanunshi har sun rabu dashi" sai ya sake daga
iccen ya maka mashi akai tas!! Icen ya karye yayi tsalle ya hadu da rufin dakin" dan daudun ya fasa kururuwa ya dafe kanshi" sannan ya kife kasa yana haure-hauren mutuwa" jini yana tsiyaya agoshin shi" bangis ya fashe da dariya yana cewa bala
Kada ka bata masa kwalliya mana" ko kana so
ne ta rage tsada wajen samarinta?"
Bala ya jefar da ragowar guntun iccen daya karye yace da bangis a fusace"
"Ai wannan dama kashe shi mukayi" ko banza
mun rage mugun iri"
suka fice waje suna dariya" da zuwan su inda
lado yake tsaye suka mika mashi jakar ya amsa araine" kamar abin wasa" tun kafin yayi magana bangis yace dashi
"Kada ka damu oga sunce mu tambayi hajiyarsu za'a samu alheri sosai a wajenta kudin suna cikin dakinta"
Lado yace dashi"
"to me kake jira ba aikinka bane..?
Bangis ya dauko gatarinshi na fasa kofa ya daga shi" sannan ya gabzawa kofar ta yanke ya fadi kasa"
to amma kuma ga mamakinsu maimakon su sami Hajiya tabawa a tsaye tana jiran tsammanin bala'in dake zuwa gareta" sai suka sameta asume a kasa ko numfashi bata yi"
Abinda basu sani ba" shine tun lokacin da ta
farka barci a tsorace taji burarin yaranta 'yan
fashi suna casa su a daki"
Kafin suzo kan nata dakin" nan take hawan jininta ya taso" bata san lokacin da ta silale kasa ta fadi ba
uwa tafiyar kenan.....