Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Raliya 25

RALIYA-25
.
Mahaifiyar Lado mai suna Haire ita ta hanashi
sayar da gidan" tace sai tayi mishi baki idan ya
sayar kuma lado yafi jin tsoron bakinta" domin
kuwa wani abokinshi watarana sunje satar
mangwaro a bayan gari yake shaida mashi
cewar
"Uba sai ya tsinewa danshi sau miliyan bata
kamashi ba"
Amma uwa data tsine sau daya to mutum ya
shiga uku ya lalace
Wannan shine ilmin da lado ke takama da ya
sani" domin kuwa a karyar abokinshi da ya
ruwaito wannan zancen shima yace a wajen wani malami yaji dake wa'axi a kasuwa don haka ya rike wannan gida nashi da mutunci wanda ke da dakuna uku da zaure hade da dakin girki da katanga"
Duk da gidan kasa ne" anyi mashi rufi na
Zamani" an buga kwano kuma anyi sili da wani
kwali mai karfi"
Anan lado yake zaune shi kadai tun rasuwar
babansu" kuma anan suke wuni shi da manyan
abokanshi biyu suna shaye-shaye" wato bala da bangis
Sa talauci ya ishe su ne suna zaune aikin yi" sai
suka fara yawon sata Da farko kananan sace-sace suke yi" to amma da suka ga wuyansu yayi kwari sai suka fara babbar
sata wato kwace" da kuma fashi da makami"
Duk da ana zarginsu da wannan hali" rana bata
taba baci aka kamasu ba" Amma ana taka-
tsantsan dasu a cikin garin" kuma 'yan sanda
suna nan suna lura da duk wani motsi da sukeyi A wannan karon lado ya isa gida a guje dauke da miliyoyin kudin shi" bayan ya sami sa'ar tserewa 'yan sandan saiya fara tunanin inda zai boye kudin"
Lado ya kulle kofa ya ajiye akwatin a kasa" ya
durkusa hannunshi yana rawa ya sake budewa"
Ba rufa ido bane kudi" Dalolin Amurka 
Sababbi!!
Lado yasan cewar yana a cikin hadari" domin
kuwa babu yadda za' ayi mutum ya tsinci irin
wadannan makudan kudi ya boye su ya zauna
lafiya" dole ne a tsananta bincike" kuma dole ne afahimci wanda ya same su indai zai fito dasu ya rika facaka a cikin al'umma Yanzu menene abin yi? Lado ya tambayi kansh"
sai a lokacin ya tuno da abokan tafiyarshi su bala da bangis"
A wanne hali suke ciki an kama su?" ko kuma
suma sun gudu sun kai labari"
Lado yasan cewar inhar 'yan sanda sun kama su" to shima asirinshi ya tonu" domin kuwa idan aka tuhume su dole ne su fadi sunanshi" kuma duk inda ya shiga za'a bishi akwakuloshii"
Lado yaji tsoro ya kamashi" lallai zama bai
ganshi ba" to amma kuma yaya zaiyi da wannan makudan Kudin ?" zai yiwu ace ya tafi dasu duk inda zaije"
Akwai matsala babba" dole ne ya boye su kamar yadda yayi niyya tun farko" idan ya gudu ko awanne zamani" kuma komai dadewa idan yadawo zai iya dauko abinshi" ba tare da kowa ya sani ba"
Lado ya mayar da akwatin ya rufe cikin sauri
Zuciyarshi na bugawa aguje kamar tabaren injin nikan ruwa"
A ina zai boye su?"
Lado ya fara waige waige cikin dakin" babu wani lungu da zai boye su hankalinshi kwance" katifa daya ce shirgegiya wacce ta tsare rabin dakin" sai wata doguwar kujera wacce rigarta ta fara zazzarewa soson ciki ya fara lekowa waje" babu inda zai boye wadannan kudi ba tare da wani ya shigo bai gansu ba"
Lado ya daga kanshi sama ya kalli rufin dakin"
nan da nan yaji ya samu wajen boye su mai
kyau" domin kuwa rufin sili ne kuma ba wani mai karfi bane sosai da zaiyi wahalar budewa" nan da nan ya hau kan kujera cikin sauri ya fara sa hannu ya banbanro siraran katakon da suka taba silin din" bayan ya banbaro layi uku sai ya jawo silin da tsiya ta bude guda biyu a cikin jerin gidajen rufin da aka yi da katako"
Lado yayi sauri ya sauko ya kinkimo katon
akwatin ya fara kokarin zirashi cikin ramin da yabude a cikin rufin dakin. 
Bayan ya tura akwatin da tsiya yana rufe idanu
saboda kurar dake kakkabowa daga cikin silin
din" tana zubo mishi a fuska" sai ya gyara
katakon ya mayar da rufin yana tura kusoshin da hannu a cikin ramin su"
Lado ya kammala gyara silin kamar bai boye
komai aciki ba" yana yi yana digirgire akan
kujerar da ya taka ya hau" bayan ya tabbatar
komai ya gyara babu wanda zai shigo dakin ya
fahimci akwai wani abu da aka boye" sai kuma
ya fara tunanin abin da zai yi na gaba zama bai
kamashi ba
Domin kuwa yasan cewar inhar aka kama bangis da bala" ko kuma idan tsautsayi ya ratsa aka kashe su" to shima asirin shi ya tonu domin kuwa an saba ganinsu tare" kuma kowa yasan abokanshi ne" kuma abokin barawo barawo ne"
Lado yaga cewar kamata yayi" yayi sauri yabar
garin a cikin wannan dare" domin kuwa a
kowanne lokaci bayan yanzu 'yan sanda zasu
iya xuwa su kamashi in har sunci sa'ar kama
Bala da bangis"
Lado yayi sauri ya fito ya kulle dakin shi da kyau" sannan ya fice waje ya bude kofar gidan ya sake kulleta da kanshi"
To amma kuma wurin zuwa mai sauki ne" komin dare ana samun mota" duk inda zaije indai har zai bar garin ya tserewa 'yan sanda" to komai yayi kyau" ko yasan lokacin da zai dawo a cikin wani daren"
A wani lokaci idan kura ta lafa ya dawo ya bude
silin ya dauki kudinshi"
Lado yayi murmushin jin dadi" ya ya tuna cewar
shifa yanzu miloniya ne
Ya sake kallon gidanshi sau daya kafin ya tafi"
Ya tuno mahaifiyarshi wacce tace saita tsine
mashi idan ya sayar da gidan" hakika tayi
gaskiya" domin kuwa da'ace ya ketare
maganarta" ya sayar da gidan tuni da yanzu bai
san wanda zai dankawa amanar wadannan kudin ba a duniya"
Lado ya juya ya nufi tashar moto cikin sauri"
yana bin lunguna da jikin gidaje don kada ya
gamu da 'yan sanda ko kuma 'yan banga dake
faturol din unguwar" yaje bakin titi kenan sai yaji an hura usur abayan shi" wasu 'yan sanda uku suka fara tsaya ya tsaya"
Lado ya rude ya sheka da gudu kamar ranshi zai fita" ya fada kan titin bai tsaya dubawa ba"
A daidai lokacin ne wasu motoci biyu da suka
jero a guje suna tsere a cikin daren suka cim
masa" motar dake gaba kirar (IBECO) wacce aka ciko ta fal da lodin albasa ita ta fara yin awan gaba da shi" ta jefar dashi can gaba kan titi" kafin direban ya taka birki ya kaucewa gawar shi" tuni har manyan tayoyin gaba sun haye han lado"
Kafin tatoyi ashirin da biyu su gama sukuwa
akanshi sanda motar ta wuce har sun nikeshi
yayi falle-falle akan titin"
motar dake biye a baya kirar (MAN) wacce ta
dauko lodin awaki ta karashe dan abinda motar
gaba ta rage"
.
Da safiya tayi sai da 'yan sanda bakwai suka yi
minti goma" suna aikin banbare nama da
kasusuwan lado wadanda suka kame akan titi"
.
=====>++++++++++++<======
.
BAYAN SHEKARA SHIDA
Raliya tana zaune a bakin kofar dakin ta" tana
kallon wani dan tunkiya na makwabtansu da
kullum yake shigowa sashin su yana cin kanzon abinci dake a bakin kwata"
A halin yanzu da dan tunkiyar yake ta zagaye-
Zagaye a cikin gidan bai sami kanzon komai ba" sai yayi tsalle sau biyu yayi kuka" sannan ya fita waje a guje"
Raliya tayi ajiyar zuciya sannan tace a sanyaye"
"muma bamu samu munci ba" ballantana har mu zubar kaima ka samu"
Wannan yanayi na babu ya dade" kuma ya zama dan gari a wajen Raliya da mijinta Rufa'i
Bana shekara shida kenan da yin aurensu" gashi har Allah yayi wa auren abarka Raliya ta haifi kyakkyawan yaro tun shekaru biyar da suka wuce mai suna Idrisu
Gashi a halin yanzu ma wani cikin gareta har
yakai wata biyar" to amma kuma ta bangaren
rufin asiri" sai dai ayiwa Allah godiya" tun da dai akwai rai da lafiya"
A halin yanzu da Raliya take a zaune tayi tagumi tana jiran mijinta rufa'i ya dawo da abin da zasuci" kusan karfe uku kenan na rana" amma
kuma abin takaici har yanzu Raliya bata karya
ba"
Rabonta da Abinci tun daren jiya" gata da ciki to
amma ya zatayi tunda babu?"
Da a can da farko-farko idan basu sami abin
jefawa a baki ba" saita aika gidansu a samo
mata abinci" shi kuma Rufa'i sai ya zagaya
wajen abokai ya zauna wanda ya dan sami
sukuni ya fito da shi" su taru a ci"
to amma yanzu abubuwan sun ishi kowa"
Yanzu ana cikin tsakiyar rani ne" tsabar hatsi ta
dami kowa" to wa zai jure kullum ya rika turo
mashi yaro da kwano in ana gajiya ai dole ne
yaji da wannan zaman babu na Raliya da Rufa'i 
Shiyasa take hakuri idan Rufa'i ya samo su ci"
idan bai samo ba su hakura yunwa dai ba kisa
take yi ba" sai dai asha wahala kafin a samu a ci"
Dan su Idrisu ne abin tausayi" shi kuma yaje
yawo" yana dai fita gidajen makwabta yana
wasa da yara" yawanci acan yake samun nashi
yadan ci a hannu a hannu ba yawa sai kaga har
ya koshi"
Rufa'i yana iya kokarinshi" yana noma kuma
yana zuwa kwadago safiya da yammaci"
to amma kuma da yake zama ne irin na karkara
bai iya sana'a ba" dole dan abinda aka noma ko
buhu arba'in ne ba inda yake zuwa"
Baya kaiwa wata daminar yake karewa" idan
babu lafiya ana bukatar magani dole hatsin nan
da za'a sayar" idan sallah tazo a ciki za'a dauka
ayi hidima ayi dikci aci nama"
Idan dakuna suna bukatar gyara" ko kuma idan
katanga ta fadi a ciki za'a dauka a sayar ayi
gyara"
Ga hidimar bukukuwa da haife-haife basa karewa"
idan ana fadin gaskiya kuwa sai dole ne Rufa'i 
ya shiga tsomomuwa Zama ba sana'a ba dabara bace"
Raliya ta dade tana bashi shawara ya kama
sana'a Rufa'i ya kan daukar mata alkawarin zai
duba ya gani"
to amma abinka da mutumin da bai saba abu ba"
koya fadi baya cikawa" don haka saita rabu
dashi" yayi abinda ya gada kuma ya iya"
Mutane suna mamakin wannan baiwar Allah gata 'yar boko kyakkyawa" amma ta hakura sai
faman wahala take sha tare da wannan dan
kauyen miji nata" gashi wasa-wasa har zata yi
haihuwa ta biyu"
Raliya bata damuwa domin kuwa tayi tawakkalin
tun tana karama tayi amanna da cewar samu da rashi duk daga Allah ne"
To me zai sa ta damu kanta" tun da dai mutum
bai yiwa kanshi arziki idan suna da rabon jin
dadi a duniya" to komai dadewa ai zasuji" don
haka babu matsala" Allah yasan halin da suke
ciki" kuma shine mai badawa" Don haka komai
tsanani indai anyi hakuri to sauki zaizo
Raliya tana zaune tana zaman jira" zuwa can sai taji sallamar Rufa'i mijinta" ya shigo cikin gidan, yana fara'a rike da.......amma