Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Raliya 27

RALIYA-27
.
"In Banda wulakanci da harkar karanta ace
kamar ni da arzikina da mutuncina ka dauko ni ka sakani a wannan dakin" silin ya lalace ba'a gyara ba" sai kura ke zubowa yatu nayi shara takai sau talatin a dakin nan" Abashe ya sake cewa kiyi hankuri gobe iyanzu kina a wani daki in Allah ya yarda"
Kubura tayi tsaki tace Ai kamata yayi ace tantabaru ke kwana anan" kai ni wallahi ko tantabarata bazan ajiye ta anan ba.....
Ta sake hararar rufin dakin dama shi yafi komai
tunzurata abinda wannan mata bata sani ba
shine" wannan rufin daki yafi karfin matsayinta"
Da ace za'a ciro abinda ke ciki wanda ya lalata
silin ya kusa ruguzowa"
Da ace duniya ta san komai ke a ciki a boye tun
shekara shida da suka wuce" to ko shugaban
kasa zaiyi fatan ya zauna a ciki"
Abashe yace da ita a lokaci guda da ya bita suna kallon rufin dakin"
"Ni kaina kullum na shigo dakin ina bakin cikin in kalli silin din nan ji har wani doro-doro yake yi sai kace katako ya balle a ciki"
"kubura ta yatsine fuskarta sannan ta duba
agogon dake manne a jikin bango" taga karfe sha daya na dare saura minti ashirin"
ta matsa sosai kan gadonta ta jawo matashi
daya ta jefa shi can karshen gadon kusa da jikin bango" sannan ta fara warware bargon dake cukuikuye akan gadon"
Abashe dake zaune yana kallonta cikin damuwa yace
"Haba kubura yau ma haka zakiyi min" kwanan
mu wajen goma kenan fa a haka"
ta kalle shi cikin raini"
"me kake so inyi maka...?"
Ganin wata masifar zata sake tasowa" sai ya
rage murya yace da ita
"A'a ba wani abu bane dama gani nayi ana zafi
sosai" kuma naga zaki kwanta baki dan rage
kayan jikinki ba"
Ta sake taso mashi da fada tace
"to banga damar cire kayan ba" idan kana da
karfi kazo ka kamani da tsiya ka cire mani"
ta murguda baki tana harararshi" sannan ta juya mashi baya ta kudundune jikinta duka a cikin bargo" har safiya tayi Abashe yana a zaune abakin gadon cikin takaici yana kallonta"
.
======>++++++++++<=======
.
Anyi haka da kwana biyu Rufa'i ya tare da
iyalanshi suka bakunci garin kwanar tsamiya" da yamma a cikin wata karamara akori-kura" ta
debe su da kayansu"
Lokacin da suka sauka a gidan wannan abokin
Rufa'i wanda ya kawo shi garin don suyi sana'a
tare" sai mutumin ya amshe su hannu biyu da
yake dama ya dade da sanin maganar" yace dasu tun kafin su sauke kayansu daga motar"
"Ai ba tsayawa bata lokaci za'ayi ba" sai mu
wuce gidan da na samar maku" yana can kun
baro shi a bakin kasuwa"
mutumin ya shiga motar yana nunawa direban
hanyar da zai bi tare da su Rufa'i har suka isa
gidan hayar da ya samar masu"
Ba wani boyayyen gida bane" gidan marigayi lado ne" dan fashin da mota ta kashe a titi" wadanda suka bi wata mai abinci har gidanta suka kasheta" wai ita hajiya tabawa"
koda yake tuni an mance da wannan labari a
garin" domin ba yanzu abinda ya faru ba shima
Rufa'i bai sani ba" gida dai gida ne ko na
wanene" kuma shi bako ne haya ya kama" kuma biya zaiyi"
mutumin yacewa Rufa'i a lokacin da motar tayi
fakin a kofar gidan" shekaran jiya wanda ke zaune a gidan ya tashi"
wani yaron mu ne da ya sami karayar arziki ya
dawo daga birni" mai suna Abashe ba wata
matsala kuyi zamanku tun da dai sana'a ta kawo ku"
Alabashi idan an sami abinda aka zo nema daga baya sai ku canza wani wajen wanda yafi wannan sukuni"
Rufa'i yayiwa mutumin godiya" nan da nan ya
taimakesu suka fara shiga da kayan cikin gida"
ba wasu kaya bane dama na azo a gani ba katifa ce da sauran kayan tarkacen kwanonin abinci dana aiki"
Bayan direban ya tafi tare da mutumin da ya
nuna musu hanyar gidan" sai rufa'i da Raliya
matarshi suka fara shiga da kayansu cikin dakin"
Sai a lokacin suka lura da rufin dakin inda silin ya kusa ruguzowa mai tsautsayi kawai yake jira" Rufa'i ya tsaya ya kalli silin yace da Raliya dake a bakin kofa" "Kai!! Raliya wannan dakin zai zaunu kuwa" dubi silin din yadda ya kusa ruftowa anya bazamu canza gida ba"
Raliya dake rike da hannun dan su idrisu tace da mijin nata"
"Ba komai Rufa'i mu zauna hakan nan Allah zai
kare mu" kada ka manta akan abin nema muka
fito" ko ina muka tsuguna yayi tunda ba'a garin
mu" muke ba"
Rufa'i ya daga kai ya kalli silin din yace
"Bazamu zauna a dakin nan ba sai mun gyara
silin din nan" bari in dauko turmi a waje in hau in gani ko zan iya gyara wa" Raliya tace dashi
"Baka rabuwa da jawo aiki Rufa'i don Allah kada ka taba musu daki iya gani iya kyalewa"
Rufa'i ya wuce ta" ya fita waje cikin sauri yana
cewa" masu gidan ne zasu kwana ciki ko kuwa mu!" idan dakin ya kashemu wa gari ya waya bamu ba?
Ya kinkimo wani tsohon turmi da suka gani a
tsakar gidan" Raliya ta shige cikin dakin ta bashi hanya ya shigo ya ajiye turmin a tsakar dakin ya kifa bayan shi ya fara kokarin hawa"
Raliya ta kalli tozon silin din tace
"Gaskiya wannan wauta ne Rufa'i ina jin tsoron
ka taba silin din nan" ya haye saman turmin yace da ita
"idan bazaki iya tsayawa ba ki fita waje ki jirani in gama raliya tayi dariya tace dashi............
t