Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Raliya 26

RALIYA-26
.
Raliya tana zaune tana zaman jira" xuwa can taji sallamar Rufa'i mijinta" ya shigo cikin gida yana fara'a rike da leda a hannunshi na hagu" ya riko idrisu da daya hannun"
Raliya ta amsa sallamar tace dashi
"shi kuma wannan a ina ka tsinto shi" ina ta
nemanshi zanyi mishi wanka tun dazu"
Rufa'i ya saki hannun idrisu ya rugo a guje ya
fada jikin uwarshi"
Can nagan shi tare da yara a dandali suna
guje-guje"
ya zauna a gabanta yana murmushi da gani
tasan cewar an dace" an samo abinci" to amma
kuma ga alama bayan abinda ya shigo dashi a
ledar akwai kuma wani albishir mai dadi da ya
kosa ya sanar da ita" Rufa'i ya kwance bakar ledar Raliya taga shinkafa ce" yar gwamnati kwano biyu" da fakitin makaroni" da magi" ta rike numfashinta cikin mamaki" domin kuwa rabon da taga makaroni agidan tun tana amarya" sanda abubuwa na farko-farko" kafin gari yayi gari" Raliya ta tambayeshi
"Rufa'i me yasa ka sawo shinkafa da makaroni"
mu da muke neman masara da kubewa
mushashshiya.....?
"Rufa'i yaci gaba da yi mata murmushi" suka
dubi juna yace
"kada ki damu Raliya" in Allah ya yarda wahalar
mu tazo karshe" wannan somin tabi ne"
Raliya ta dubeshi cikin rashin fahimta"
"Kamar yaya Rufa'i nifa ban gane ba"
Rufa'i yayi ajiyar zuciya yace da ita"
"Da na fita dazu na hadu da wani abokina dake birni" shine yazo ya shaida min wani abin farin
ciki" wai yaso ya dauke ni mu rika sana'ar kifi
tare" yana so in zama babban yaronshi" zai ajiye ni awani gari inda ake sayen kifi sosai" ya kafa min depot a can yana kawo mani kifin daga birni ni kuma ina sayarwa" to har mun gama komai
shine ya bani dubu goma yanzu wacce zan samu mota mu kwashe kayanmu zuwa garin tare
Raliya ta rike baki cikin mamaki"
"Ina zamu zauna idan mun koma wani garin?
Rufa'i yayi mata dariya"
"Haba Raliya ga gidajen haya nan ba iyaka" yanzu aduniyar nan wanne gari zaka je ka rasa indai kana da kudi" wannan ba matsala bace zamu samu gida kada ki damu"
Raliya sake cewa "to yaya su baba ka sanar da su sun amince kuwa?" Rufa'i yace
"Na biyo ta gida na shaida musu halin da ake ciki kuma sun amince domin wannan abin karuwa ne" Raliya duk wanda ya sami labari dole ne ya tayani murna"
Yanzu shiye-shirye zaka fara yi" yace jibi yake so mu koma can baki dayanmu"
Raliya ta girgiza kai cikin wani sabon mamaki
tace "Ai ni abin ne duk yazo mani a kurace wallahi" abu ba zato ba tsammani haka?"
Rufa'i yaci gaba da murmushi"
"Haka rayuwa take dama Raliya" Idan ubangiji
ya nufe ka da samun wani arziki kana kwance
abinka ba zato ba tsammani sai kaga yazo ya
sameka" In Allah ya yarda wannan sana'a da
Zamu fara ta kifi alheri ne" kuma wannan canjin
gari da zamu yi mu koma wani garin shima duk
alheri ne" bazamuyi dana sani ba"
Raliya tayi saurin cewa
"Allah ya sa haka" kuma Allah ya taimakemu"
Ta zaunar da idrisu danta a kasa wanda yake ta
kokarin taka gwiwarta ya kamo wani abu a jikin
bango" daga baya ta sake tambayar Rufa'i
"wanne gari yace zai ajiye ka inda zamu zauna
ya rika kawo maka kifin kana sayarwa?"
Rufa'i yace "Ba nesa bane nan ne kusa" yace mani kwanar tsamiya zamu koma" domin ana zuwa sarin kifi agarin kuma yace mani indai na kula to za'a sami riba mai yawa"
Da ya ga kamar Raliya tana tunani sai ya sake
cewa "ko baki taba zuwa kwanar tsamiyar bane Raliya shine fa wannan garin da aka taba yin wani shaharren manomi wanda duk jihar nan babu kamar shi" sunan shi marigayi Alhaji Hashimu MAI ABINCI HAR BAYAN RAI"
.
======>++++++++++<=======
.
Sai da ya kwace fiye da minti biyar a tsaye a
kofar gidan yana tunanin abinda zai fada mata
wanda zai kwantar mata da hankali"
Domin a yadda suka rabu da safe dazu da zai
fita" yasan cewar in har a wannan karon ya shiga baizo mata da labarin sabon gidan da ya nema ba" inda zasu koma" to ba zasu kwana lafiya ba"
Ya tsaya shiru yana sake-sake azuciyarshi"
wani mutumi ya wuce shi a tsaye sau biyu yana
mishi sallama" amma ko dago kai baiyi ba"
Zuciyarshi tayi nisan zango"
mutumin ya wuce saurayin yana mamakin abin da kesa mutane na dorawa kansu damuwa ba gaira ba dalili da ransu
To amma kuma da'ace yasan abinda ke damun
wannan saurayi mai suna ABASHE da bai ce hakaba" abashe matsakaici ne mai farar fata wanda ko ba fadawa mutum ba da ganinshi ansan cewar yaci kaji a duniya" to sai dai wannan tuni ya zama tarihi" domin kuwa a halin yanzun ba'a maganar kaza" shi bama ta abinci yake yi ba" ta muhalli yake yi" wannan wannan shine abinda ke hadashi fada kullum da matarshi. abashe haifaffen garin kwanar tsamiya ne" wanda ya dade da fita neman kudi ya dira birnin kano da sa'a
A cikin shekara biyu yayi karfi a kantin kwari a
dalilin wani ubangidanshi mai kirki da ya samu"
wanda ya buda mashi kofofin samun arziki ba
mugunta" da bakin ciki" karayar arzikin da ta samu ubangidanshi ne ya sa shima dole ya turgude suka fadi kasa tare da kwance uwa kwance"
Gashi kuma kafin ayi haka Abashe ya auri wata
yarinya 'yar birni kuma 'yar hutu wacce bata son hada hanya da wahala a rayuwarta"
tun faruwar al'amarin mara dadi matar wacce
bata fi shekara daya a hannunshi ba" mai suna
KUBURA" ta fara juya mashi baya" bala'i na safe
dabam" na rana dabam" ga kuma na dare" to
amma baya tsayawa a gida kafin ta farka barci
tayi bala'in safe" shi tuni yabar gidan yayi nisa
baya dawowa da rana kwata-kwata" sai dai idan
ya dawo da daddare ta zazzage mashi kwandon tsiyar da ta tara tun safe har daren"
Ganin cewar zaman kano bana rago bane" dole
ne a tashi a nema" kuma ganin yadda hanyoyi
suka toshewa Abashe sai ya yanke shawarar
daukar matashi su koma garin su kauyen kano
inda ya baro" domin kuwa acan rayuwa da dan
sauki ba kamar zama a birni ba ne" inda ko bola ka tara a cikin gida saika bada kudi an kwashe maka ita.
Abashe ya daufi fiye da sati daya suna kai ruwa
rana da kubura wacce ta tsaya kai da fara bazata bishi ba" sai dai in sauwake mata zaiyi"
to amma da ya tsara mata dabararshi cewar
Zuwa zaiyi yayi noma a gonar mahaifinsu na
shekara daya kacal ya sayar da amfanin gonar
su sake dawowa birni su sami jarin yin sana'a
saita hakura amma da ganin yanayin fuskarta a
sanda suka zo garin to an san cewar dole ce
kawai ta kawo ta" kamar yadda kare yake fadi in ance dashi dan kauye
Da yake babu sauran dakin da mace zata zauna agidansu Abashe" kuma koma akwai safayar daki" kubura tace bazata zauna a gidan su na gado ba" mai dauke da matan aure goma sha biyu" dakunan su a jere ciki daidai" bandaki daya dafa duka" da kuma dakin girki na kasa"
Sai Abashe ya nemi gidan haya" a wani gida a
bakin kasuwa na wani barawo da mota ta taba
kashewa da daddare" an biyoshi mai suna LADO.
.
Tun wasu shekaru da suka wuce" dakuna biyu
dake a gidan lado marigayin barawon" wani dan kasuwa ya kama su haya aka zuba farin wake aciki yana jira yayi tsada a kwashe asayar" saura daki daya kawai ya rage inda maigidan ya zauna"
to amma kuma abin takaici silin dakin ya tuntsiro
ya kusa ruguzowa" kamar an dora wasu kaya a
ciki"
Tun a ranar farko da wadannan ma'aurata suka
tare a gidan matar ta fara balbala masifa" domin kuwa a cewarta dakin baiyi mata ba" gara tun da wuri su canza gidan"
wannan silin idan ya fadowa mutum ai sai dai
azo a ceci bawa bazan iya ba"
kwanansu shida kenan a gidan" kullum maganar kenan guda daya" A rana ta hudu ne Abashe yace da ita
Kiyi hankuri kubura na fadawa masu gidan
wannan matsala kinsan mai gidan ya dade da
rasuwa" wata mahaifiyarshi ke iko da gidan"
kuma ta tsufa" bata da kudi" amma tace in gyara silin a cikin kudin da zamu biya na haya sai mu warware daga baya"
kubura ta turo baki tace a fusace
"Sam!! Bazan iya zama sai anyi wani gyara ba"
Idan zakaje ka nemo mana gidan mutunci da
Zamu zauna kaje ka nemo" idan kuma ba haka
ba" to wallahi kaji na rantse maka zan hada
inawa-inawa in koma kano" domin nifa dama
matsamin kayi ba'a son raina nazo wannan kauyen ba ehee!!
Ganin cewa allura zata tono garma" sai ya fara
fafutukar nemo wani gidan"
A halin yanzu anyi mashi alkawarin awashe gari yaje yaga gidan" sanna ya fadi mashi farashin yaji idan zai iya biya" to wannan shine abin da yake tunani a ranshi da ya tsaya a kofar gidan" yana tsara yadda zai fadawa rabin ran tashi" don ta fahimce shi" su samu dai su sasanta" domin masifar shi ma ta ishe shi.
.
Abashe ya shiga cikin gidan da zuwa bai zame ko ina ba" sai dakin wanda shine na karshe a jerin dakunan guda uku"
ya sami kubura a zaune a bakin gadonta tayi
shiru tana tunani" tana sanye da atamfa da
kallabinta" tun kwalliyarta ta rana" fitilar kwai ta
haske kakkausar fuskarta sai faman cika take yi tana batsewa"
Abashe yayi mata sallama ko gezau bata yi ba"
da yake yasan irin zaman da sukeyi" sai ya zauna a bakin gadon kusa da ita ya fara lallashinta
Kiyi hakuri kubura indai akan wannan gidan ne
komai yazo karshe" In Allah ya yarda gobe zamu tashi na sami wani gidan.
Kubura taja numfashi mai tsawo tace dashi a
fusace Dakata malam" kada ka raina mani hankali batun yau kake yi mani wadannan karairayin ba" Idan zaka bani takardata da arziki ka bani" Idan kuma so kake yi kabani da tsiya" to zamu zuba dani da kai mu gani" amma ni na gaji bazan iya ba"
Abashe ya rage murya yace da ita"
"Duk abin bai kaimu ga haka ba" kubura kin san
ba'a zaune nake ba" ina iya kokarina akan neman gidan nan" kuma tunda an samu menene kuma da wani tsokano abinda ya wuce" daga gobe ta kare" kuma ki bari ki gani"
Kubura ta dago kanta ta kalli rufin dakin" ya
babbako har wani tozo-tozo yake yi" tace a
fusace
In ban da wulakanci da harkar karanta ace kamar ni da arzikina da mutuncina ka dauko ni ka.....