Galadiman Katsina Justice Mamman Nasir Ya Tsallake Rijiya Da Baya.
Galadiman Katsina kuma tsohon Mai shari'a na babbar kotun daukaka kara wato Justice Mamman Nasir ya Tsallake rijiya da baya, biyo bayan wani hari da Wasu yan bindiga suka kai masa jiya litinin da daddare a jihar Katsina.
Datiijo Mamman Nasir wanda shine hakimin malunfashi. Allah ya tsareshi daga wannan harin da aka kaimasa,inda ya Tsira batare da ko rauni ba.Yanzu haka yana gida cikin koshin lapia.