Kungiyar ma'aikatan lafiya ta kasa Nigerian Medical Association ta ce daga yanzu babu wani likita da zai da zai Kara duba jami'in hukumar KAROTA yayin da ya je asibiti don neman agajin likita, inda shugaban kungiyar reshen Kano Dr Sanusi Muhammad Bala ya ce tun a ranar 4 ga wannan wata na janairu ne wasu jami'an KAROTA suka ci zarafin wani Likita da ke aiki a asibitin Kashi na Dala ta hanyar dukan sa da takalmi Kuma kungiyar ta kaiwa hukumar kara amma har yanzu bata dauki mataki ba.
Showing posts with label labarai. Show all posts
Showing posts with label labarai. Show all posts
MATAIMAKIN SHUGABAN KASA YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA
A LOKACIN DA JIRGINSA YAI HADARI
Jirgin mataimakin Shugaban kasa Pastor Yemi Osibanjo yayi hatsari a Kabba, Jahar Kogi.
A kokarin hukumar zabe ta kasa INEC na ganin anyi sahihin zabe, hukumar ta samar da wata sabuwar manhaja (Application) mai suna INEC eReporter zaka iya samun wannan application din a Play Sore.
Idan ka dauko wannan app din zai baka damar fadawa hukumar zabe halin da ake ciki a yankinku na rashin zuwan jami’an zabe, ko magudun zabe, matsalar card reader ko kuma yunkurin kawo hargitsi da duk wani abu da kuka ga kuna da bukatar isarwa ga hukumar.
Da wannan app zaku iya aikawa da sakon rubutu, hoto, ko video dama sauti kai tsaye ga hukumar.
‘Yan uwana MATASA mu hada hannu da hukumomin kasarmu domin tabbatar da sahihin zabe mai Inganci.
Abubuwan dasuke hana fingerprint aiki
Yana Da Kyau Ka Karanta: Menene Ma’anar Thumbprint?
1. Cutar Dermatitis: wannan cutar tana kawo bushewar yanyatsu. Kuma tana jawo yatsun mutun suqi fitowa fingerprint scanner.
2. Qonewa: Idan mutun yaqone a yatsa, kafun yawarke hakan na iya hana fingerprint yayi aiki.
3. Yawan anfani da yatsu
4. Yawan anfani da chemical kamar bleach, chlorine, acetone dasaurandu.
5. Tsarin halitta.

Galadiman Katsina Justice Mamman Nasir Ya Tsallake Rijiya Da Baya.
Galadiman Katsina kuma tsohon Mai shari'a na babbar kotun daukaka kara wato Justice Mamman Nasir ya Tsallake rijiya da baya, biyo bayan wani hari da Wasu yan bindiga suka kai masa jiya litinin da daddare a jihar Katsina.
Datiijo Mamman Nasir wanda shine hakimin malunfashi. Allah ya tsareshi daga wannan harin da aka kaimasa,inda ya Tsira batare da ko rauni ba.Yanzu haka yana gida cikin koshin lapia.