Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Yadda Yan Social Media Zasu Sanar Da INEC Halin Da Ake Ciki A Yankunansu

A kokarin hukumar zabe ta kasa INEC na ganin anyi sahihin zabe, hukumar ta samar da wata sabuwar manhaja (Application) mai suna INEC eReporter zaka iya samun wannan application din a Play Sore.
Idan ka dauko wannan app din zai baka damar fadawa hukumar zabe halin da ake ciki a yankinku na rashin zuwan jami’an zabe, ko magudun zabe, matsalar card reader ko kuma yunkurin kawo hargitsi da duk wani abu da kuka ga kuna da bukatar isarwa ga hukumar.
Da wannan app zaku iya aikawa da sakon rubutu, hoto, ko video dama sauti kai tsaye ga hukumar.
‘Yan uwana MATASA mu hada hannu da hukumomin kasarmu domin tabbatar da sahihin zabe mai Inganci.

Cc Sharfadi.com