_
Assalamu alaikum, a yau zamuyi magana akan Google Alert da kuma yadda ake amfani dashi, sai a biyomu.Kamar yadda kuka sani Google wanda a hausance ake kira da matambayi baya bata shafi ne da zai baka damar tambayar dukkan wani abu da ya shige maka duhu shi kuma ya baka amsa.Menene Google Alert?Google Alert tsari ne da zaibaka damar zabar wasu bangarori ko kalmomi, ko kuma darasi, sai ka baiwa google umarnin duk sanda aka sanya wani sabon abu mai alaka da wannan a internet to ya sanar da kai,
wannan tsarin zai baka damar sanin halin da bangaren da ka zaba yake ciki a duniyar yau.Misali kai dalibi ne kana karantar Ilimin Computer zaka iya shiga Google Alertsai ka sanya alert na ilimin computer to da zarar an saka wani sabon abu a internet da ya shafi wannan ko daga Ina a duniya to google zasu tura maka ta email dinka.Rm
Yadda Ake Amfani Da Google Alert:Yadda ake amfani da google alert shine ka kasance kana da Google account wato Gmail sai ka ziyarci https://www.google.com/alertsBayan kayi register zaka iya zabar lokacin da kake so su dinga tura maka sakon email din.Sannan kana da damar kirkirar alert a bangarori daban-daban ko guda nawa ne.Zamu dakata anan sai a rubutu na gaba